Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 13
1 To, a jamaˈar masu bin da take a Antakiya, akwai waɗansu annabawa da malamai, wato Barnaba, da Simeyon wanda ake ce da shi Baƙi, da Lushiyus daga Sayirin, da Manayen, wanda ya yi girma tare da Sarki Hirudus, da kuma Shawulu.
2 Saˈad da suke yi wa Ubangiji sujada, suna kuma yin azumi, sai Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnaba da Shawulu domin aikin da na kira su su yi.”
3 Bayan da suka yi azumi da adduˈa, sai suka sa wa Barnaba da Shawulu hannun albarka, suka sallame su.
4 Barnaba da Shawulu kuwa, waɗanda Ruhu Mai Tsarki ya aike su, suka tafi Salukiya, daga can kuma suka shiga jirgin ruwa zuwa Sayifurus.
5 Da suka kai Salamis, suka yi waˈazin Kalmar Allah a majamiˈun Yahudawa. Yohanna kuma yana tare da su yana taimakonsu.
6 Bayan sun zazzaga tsibirin duka har Bafos, suka sadu da wani Bayahude mai sihiri, shi annabin ƙarya ne, mai suna Bar Yoshuwa,
7 wanda yake tare da gwamna Sarjiyus Bulus. Gwamna Sarjiyus Bulus kuwa mutum mai hikima ne. Sai gwamnan ya kira Barnaba da Shawulu don yana so yă ji kalmar Allah.
8 Amma Alimas, mai sihirin nan, gama haka maˈanar sunansa da Helenanci take, bai ba su goyon baya ba, yana nema yă juye hankalin gwamnan nan domin kada yă ba da gaskiya.
9 Amma Shawulu kuwa, wanda ake ce da shi Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya zuba wa Alimas ido,
10 ya ce, “Kai ɗan Shaiɗan! Mai gāba da duk abin da yake na adalci! Kana cike da ruɗu da mugunta kawai. Ba za ka daina ɓata miƙaƙƙun hanyoyin Ubangiji ba?
11 Yanzu fa, hannun Ubangiji yana gāba da kai, za ka zama makaho. Za a ɗauki ɗan lokaci ba ka ga hasken rana ba.” Nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe idanunsa, ya yi ta lalubawa yana neman wanda zai yi masa jagora.
12 Da gwamna ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, yana mamakin koyarwar Ubangiji.
13 Sai Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafos a cikin jirgin ruwa, suka je Ferga ta ƙasar Famfiliya. Yohanna wanda ake ce da shi Markus kuwa ya bar su ya koma Urushalima.
14 Su kuwa suka ci gaba daga Ferga, suka tafi Antakiya ta ƙasar Bisidiya. Ranar Hutu ta Mako kuwa suka shiga majamiˈa suka zauna.
15 Bayan da aka yi karatu daga Koyarwar Musa da littattafan annabawa, sai shugabannin majamiˈa suka aika musu cewa, “ˈYanˈuwa, idan kuna da wata maganar gargaɗin da za ku yi wa jamaˈa, sai ku yi.”
16 Sai Bulus ya miƙe tsaye, ya ɗaga hannu a yi shiru, ya ce, “Ku ˈyanˈuwana Israˈilawa, da sauran masu tsoron Allah, ku saurara!
17 Allahn jamaˈar Israˈila ya zaɓi kakanninmu, ya mai da jamaˈar nan alˈumma mai girma a lokacin da suke a ƙasar Masar, ya kuma fito da su daga ƙasar da ikonsa mai girma.
18 Ya yi haƙuri da su wajen shekara arbaˈin a cikin daji.
19 Bayan da ya halaka alˈumma bakwai a ƙasar Kanˈana, ya ba jamaˈar Israˈila gādon ƙasar.
20 Wannan ya ɗauki wajen shekara ɗari huɗu da hamsin. “Bayan haka kuma Allah ya naɗa musu alƙalai har zuwa zamanin annabi Samaˈila.
21 Saˈan nan suka roƙa a naɗa musu sarki, sai Allah ya ba su Shawulu ɗan Kish, mutumin zuriyar Benyamin, wanda ya yi mulki har shekara arbaˈin.
22 Bayan da Allah ya cire Shawulu, ya sa Dawuda yă zama sarkinsu. Cikin shaidar da Allah ya bayar game da Dawuda, ya ce, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne mai zuciya irin tawa, wanda kuma zai aikata dukan nufina.’
23 Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Israˈila Mai Ceto, Yesu, kamar yadda ya yi alkawari.
24 Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi wa mutanen Israˈila duka waˈazi su tuba a kuma yi musu baftisma.
25 Yayin da Yohanna ya kusa gama aikinsa, sai ya ce, ‘Wa kuke tsammani nake? Ba fa ni ne shi ɗin nan ba. Amma akwai mai zuwa a bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.’
26 “Ku ˈyanˈuwana, zuriyar Ibrahim da kuma ku masu tsoron Allah waɗanda ba Yahudawa ba, mu ne fa aka aiko mana labarin ceton nan.
27 Gama masu zama a Urushalima da shugabanninsu ba su gane shi ne Mai Ceton ba, ba su kuma gane maganar annabawan da ake karantawa a kowace Ranar Hutu ta Mako ba. Amma sun cika wannan maganar annabawa yayin da suka hukunta Yesu.
28 Ko da yake ba su same shi da laifin da zai kai ga hukuncin kisa ba, duk da haka suka roƙi Bilatus a kashe shi.
29 Da suka cika duk abin da aka rubuta game da shi cikin Rubutacciyar Maganar Allah, sai suka sauko da shi daga kan gungumen itace, suka sa shi a kabari.
30 Amma Allah ya tashe shi daga matattu.
31 Kwanaki da yawa kuwa yana ta bayyana ga waɗanda suka bi shi zuwa Urushalima daga Galili, waɗanda yanzu su ne shaidunsa ga jamaˈa.
32 Mu ma mun kawo muku labari mai daɗi cewa alkawarin nan da Allah ya yi wa kakanninmu,
33 ya cika mana shi, mu da muke ˈyaˈyansu, saˈad da ya tā da Yesu daga matattu. Kamar yadda yake a rubuce cikin Zabura ta biyu cewa, “ ‘Kai Ɗana ne, yau na zama ubanka.’ ”
34 “Allah ya tā da Yesu daga matattu a kan cewa Yesu ba zai sāke mutuwa ba balle yă ruɓa. Hakika, Allah ya cika wannan kalma game da tashinsa cewa, “ ‘Zan ba ka albarkun nan masu tsarki kuma tabbatattu waɗanda na yi wa Dawuda alkawari.’ ”
35 “Domin a wata Zabura ma ya ce, “ ‘Ba za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.’ ”
36 “Bayan da Dawuda ya cika aikin da Allah ya ba shi a zamaninsa, sai ya yi barci, aka kuwa binne shi tare da kakanninsa, jikinsa kuma ya ruɓe.
37 Amma Yesu wanda Allah ya tā da shi daga matattu bai ruɓa a kabari ba.
38 “Saboda haka ˈyanˈuwana, ku san wannan cewa ta wurin Yesun nan ne ake sanar muku da gafarar zunubanku.
39 Ta wurinsa kuma duk wanda ya ba da gaskiya ya sami ˈyanci ke nan daga dukan zunuban da Koyarwar Musa ta kāsa ba da ˈyanci a kai.
40 Saboda haka sai ku mai da hankali, kada abin nan da Allah ya faɗa cikin littattafan annabawa yă faru da ku, wato,
41 “ ‘Ku saurara, ku masu yin baˈa! Yi mamaki, ku halaka! Gama zan yi wani aiki a kwanakinku, aikin da ba za ku gaskata ba, ko da wani ya gaya muku.’ ”
42 Bulus da Barnaba suna fitowa daga majamiˈar ke nan, sai mutane suka roƙe su su ƙara yi musu magana a kan abubuwan nan kuma a Ranar Hutu ta Mako mai zuwa.
43 Da jamaˈa suka watse, sai Yahudawa da yawa, da kuma waɗansu masu shiga addinin Yahudawa da ƙwazo, suka bi Bulus da Barnaba, waɗanda suka yi musu magana, suka ƙarfafa su su ci gaba da rayuwa cikin alherin Allah.
44 Da Ranar Hutu ta kewayo, kusan duk birnin suka taru domin su ji kalmar Allah.
45 Amma da Yahudawa suka ga taron mutane masu yawa, suka yi kishi sosai, suna musūn abubuwan da Bulus ya faɗa suna maganganun reni.
46 Amma Bulus da Barnaba suka yi magana ba tsoro, suka ce, “Ku Yahudawa ku ne ya kamata a fara yi muku kalmar Allah. Amma tun da kuka ƙi ta, kun nuna ba ku cancanci ku sami rai na har abada ba. To, za mu je wurin waɗanda ba Yahudawa ba.
47 Domin Ubangiji ya riga ya umarce mu da ya ce, “ ‘Na sa ka ka zama haske ga waɗanda ba Yahudawa ba, don ka kawo ceto har zuwa iyakar duniya.’ ”
48 Da waɗanda ba Yahudawa ba suka ji haka, suka ji daɗi sosai, suka yabi kalmar Ubangiji. Waɗanda aka ƙaddara musu samun rai na har abada kuma suka ba da gaskiya.
49 Kalmar Ubangiji kuwa sai ta ƙara bazu a ƙasar duka.
50 Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah, waɗanda ake ba su girma, da kuma waɗansu manyan mutanen garin. Suka tā da tsanani ga Bulus da Barnaba, suka kore su daga garinsu.
51 Manzannin kuwa suka kakkaɓe ƙurar ƙafafunsu domin shaida a kan mutanen garin, suka tafi Ikoniya.
52 Masu bi na Antakiya kuma suna cike da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.