Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 27

1 Da aka shirya mu tashi a cikin jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya, sai suka danƙa Bulus da waɗansu ˈyan sarƙa a hannun wani babban sojan Roma, mai suna Yuliyus, ɗaya daga cikin sojojin ƙungiyar Kaisar Augustus.

2 Da muka shiga wani jirgi na Adiramitiyum, mai shirin tashi zuwa waɗansu garuruwan da suke gefen Asiya, muka fara tafiya. Aristarkus, wani mutumin Tasalonika ta ƙasar Makidoniya, yana tare da mu.

3 Washegari sai ga mu a Sidon. Yuliyus kuwa ya yi wa Bulus alheri, ya bar shi yă je yă ga abokansa su biya masa bukatarsa.

4 Da muka tashi daga nan a jirgin ruwa, iska tana gāba da mu. Saboda haka muka zaga ta bayan tsibirin Sayifurus inda iska ba ta da ƙarfi.

5 Bayan da muka ƙetare tekun da take kusa da ƙasar Kilikiya da Famfiliya, muka isa Mira ta ƙasar Likiya.

6 A nan babban sojan Roma ya sami wani jirgin Alekzandiriya mai zuwa ƙasar Italiya, ya sa mu a ciki.

7 Muka yi kwana da kwanaki muna tafiya a hankali, har da kyar muka kai kusa da garin Kinidus. Da iska ta hana mu ci gaba, sai muka zagaya gefen da ba iska, wato ta bayan tsibirin Kirit kusa da Salmoni.

8 Muka wuce shi da kyar, har muka isa wani wurin da ake ce da shi Amintacciyar Mafaka, kusa da birnin Lasiya.

9 Da yake an ɓata lokaci da yawa, tafiyar ma ta zama da hatsari, gama a lokacin ne shekara ta yi nesa har azumi na Ranar Ɗaukar Alhakin Zunubi ta wuce. Sai Bulus ya ba su shawara

10 ya ce musu, “Ranku yă daɗe, na ga fa tafiyar nan za ta zama da hatsari da kuma hasara mai yawa, ba hasarar kaya da jirgin kawai ba, har ma da rayukanmu.”

11 Amma babban sojan nan bai yarda da abin da Bulus ya faɗa ba, a maimakon haka ya saurari maganar mai tuƙin jirgin da kuma ta mai jirgin.

12 Da yake mafakar Lasiya bai yi kyau jirage su ci damina a nan ba, sai yawancinsu suka yarda a ci gaba da tafiya, a kuma yi ƙoƙari a kai Finiks, in ya yiwu, domin su ci damina a can. Finiks kuwa wata tashar jirgi ce a tsibirin Kirit wadda take fuskantar arewa ta wajen yamma, da kuma kudu ta wajen yamma.

13 Da iska ta fara hurawa daga kudu kaɗan-kaɗan, sai mutanen suka yi tsammani bukatarsu ta biya, sai suka jawo ƙarfen da yake riƙe jirgin, suka bi gefen tsibirin Kirit, kusa da bakin teku.

14 Ba da jimawa ba sai ga wata babbar iska daga arewa ta gabas ta bugo daga tsibirin.

15 Da iskar ta bugo jirgin, har ya kāsa fuskantar iskar, sai muka bari kawai iskar ta yi ta tura mu.

16 Da muka bi ta bayan wani ɗan tsibiri mai suna Kauda, inda iska ta ragu, da kyar muka jawo ƙaramin jirgin a sa shi a kan babban.

17 Bayan da suka jawo ƙaramin jirgin zuwa cikin babban jirgin, suka yi dabara suka ɗaɗɗaura igiyoyi kewaye da babban jirgin, domin kada ya farfashe. Suka kuma saukar da zanen jirgin domin su bar iska ta tura jirgin gama ba su iya tuƙinsa ba. Sun yi haka domin suna tsoro kada a jefa su a yashin Sirtis mai haɗiye kome.

18 Saboda ruwan yana hauka, yana jijjiga mu sosai, sai washegari suka fara kwashi kayan da yake a cikin jirgin, suka jefa a cikin ruwa.

19 A rana ta uku kuma, su da hannuwansu suka jefar da waɗansu kayan aikin jirgin.

20 Da dai muka yi kwana da kwanaki ba mu ga rana ko taurari ba, kuma babban hadari mai iska yana ta dūkanmu, sai muka fid da zuciya za mu tsira.

21 Da yake sun daɗe ba su ci abinci ba, sai Bulus ya tashi tsaye a tsakiyarsu, ya ce, “Jamaˈa, da kun ji maganata cewa kada ku tashi daga tsibirin Kirit, da ba ku fāɗi a cikin wannan hatsari da masifa ba.

22 Amma yanzu ina yi muku gargaɗi ku yi ƙarfin hali, don ba wanda zai yi hasarar ransa a cikinku, sai dai a yi hasarar jirgin.

23 Gama a daren jiya wani malaˈikan Allah wanda nake nasa, wanda nake kuma bauta masa, ya tsaya kusa da ni,

24 ya ce, ‘Kada ka ji tsoro, Bulus. Lallai za ka tsaya a gaban Kaisar. Ga shi kuma ta dalilinka Allah cikin alherinsa zai ceci abokan tafiyarka.’

25 Saboda haka sai ku yi ƙarfin hali, ku jamaˈa, gama na gaskata Allah a kan cewa yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka zai zama.

26 Amma fa dole ne iska ta jefar da mu a yashin wani tsibiri.”

27 A dare na goma sha huɗu, ana ta tura mu dai a Tekun Meditereniya. Wajen tsakiyar dare sai masu tuƙin jirgin suka yi tsammani mun yi kusa da ƙasa.

28 Sai suka gwada zurfin ruwan suka ga ya kai ƙafa ɗari da ashirin. Da muka ci gaba kaɗan, sai suka sāke gwadawa, suka sami ƙafa casaˈin.

29 Don tsoro kada jirginmu yă yi karo da duwatsu, sai suka saki ƙarafa masu nauyi guda huɗu ta bayan jirgin domin a hana jirgin tafiya. Sai suka zuba ido suka roƙi Allah gari yă waye da sauri.

30 Amma masu tuƙin jirgin sun yi ƙoƙari su gudu. Sai suka saukar da ƙaramin jirgin suna wayo kamar za su saukar da ƙarfe mai nauyi daga gaban babban jirgin.

31 Sai Bulus ya ce wa babban sojan Roma da kuma sojojin, “Idan mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba yadda za ku tsira.”

32 Da jin haka sai sojojin suka yayyanke igiyoyin ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.

33 Da gari ya kusan wayewa, sai Bulus ya roƙe su su ɗan ci abinci, ya ce, “Yau fa, kwana goma sha huɗu ke nan kuke zaman tsammani, ba ku ci wani abu ba.

34 Saboda haka ina roƙonku ku ci abinci don lafiyarku, tun da yake ba wani a cikinku wanda zai rasa ko gashin kansa guda ɗaya.”

35 Da ya faɗa haka, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya ga Allah a gabansu duka, ya rarraba ya fara ci.

36 Sai duka suka sami ƙarfafawa, su ma suka ci abinci.

37 Mu duka a cikin jirgin kuwa mutum ɗari biyu da sabaˈin da shida ne.

38 Da suka ci suka ƙoshi, sai suka rage wa jirgin nauyi ta zubar da alkama cikin ruwa.

39 Da gari ya waye masu tuƙin jirgin ba su iya gane da ƙasar da suke ba, amma dai sun lura da wani lungu mai yashi. Sai suka yi shiri su kai jirgin kan yashi idan zai yiwu.

40 Sai suka yanke igiyoyi na dukan ƙarafa masu nauyin, suka bar su a ruwa. A daidai lokacin kuma suka ɓalle maɗaurin abin juya jirgin. Saˈan nan kuma suka tā da zannuwan da suke gaban jirgin daidai yadda iska za ta tura shi gaba. Sai suka sa kai zuwa gefen teku.

41 Amma da muka isa wani wurin da ruwan yake haɗuwa, sai jirgin ya buga yashi, har kan jirgin ya shiga cikin yashin ya kāsa motsi. Sai jirgin kuma ya fara farfashewa ta baya saboda haukan raƙuman ruwa.

42 Sai sojojin suka yi shiri su kakkashe ˈyan kurkukun, domin kada waninsu yă yi iyo yă gudu.

43 Amma da yake babban sojan Roma ya so ya ceci Bulus, sai ya hana su. Ya kuma ba da umarni cewa dukan waɗanda suka iya ruwa su fara tsalle su shiga cikin ruwa su yi iyo zuwa gefen teku.

44 Sauran kuwa su hau katakai, ko su hau tarkacen jirgin. Da haka duka suka kai gefen teku lafiya lau.

Open Bible reader