Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 27:40
Sai suka yanke igiyoyi na dukan ƙarafa masu nauyin, suka bar su a ruwa. A daidai lokacin kuma suka ɓalle maɗaurin abin juya jirgin. Saˈan nan kuma suka tā da zannuwan da suke gaban jirgin daidai yadda iska za ta tura shi gaba. Sai suka sa kai zuwa gefen teku.
Open Bible reader