Hausa Bible
Yahaya 8
1 Amma Yesu ya tafi Tudun Itatuwan Zaitun.
2 Da sassafe kuma Yesu ya sāke shiga Haikali. Dukan mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu.
3 Sai malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa suka kawo wata macen da aka kama ta tana yin zina. Suka sa ta tsaya a tsakiyarsu.
4 Sai suka ce wa Yesu, “Malam, macen nan an kama ta ne, tana cikin zina.
5 To, Koyarwar Musa ta umarce mu mu jejjefe irin waɗannan da duwatsu har su mutu. Kai kuwa me ka ce?”
6 Sun yi wannan tambaya ne domin su gwada shi, domin dai su sami wani laifin da za su yi ƙararsa a kai. Amma Yesu ya sunkuya, ya yi rubutu a ƙasa da yatsarsa.
7 Da suka dinga yi wa Yesu tambayoyi, sai ya tashi tsaye ya ce musu, “To, duk wanda bai taɓa yin zunubi a cikinku ba yă fara jifarta da dutse.”
8 Sai Yesu ya sāke sunkuyawa, ya yi rubutu a ƙasa.
9 Da suka ji haka kuwa, suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya, tun daga babbansu zuwa ƙaraminsu, aka bar Yesu shi kaɗai, da macen a tsaye a gabansa.
10 Sai Yesu ya miƙe tsaye, ya tambaye ta ya ce, “Uwargida ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”
11 Sai ta amsa ta ce, “Maigirma, babu kowa.” Sai Yesu ya ce, “Ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, amma kada ki ƙara yin zunubi.”]
12 Sai Yesu ya ƙara yi wa mutane magana ya ce, “Ni ne hasken duniya. Duk wanda yake bina ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami haske na rai.”
13 Sai Farisiyawa suka ce wa Yesu, “Kana yi wa kanka shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.”
14 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ko da ma na yi shaida a kaina, ai, shaidata gaskiya ce, gama na san inda na fito, da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ba, ko kuma inda za ni.
15 Ku kuna yin shariˈa ne bisa ga ganin mutum. Ni kuwa ba na yi wa kowa shariˈa.
16 Amma ko da ma zan yi shariˈa, shariˈata ta gaskiya ce, gama ba ni ne kaɗai ba, amma Ubana wanda ya aiko ni yana yi tare da ni.
17 A cikin Koyarwarku an rubuta cewa, idan shaidu biyu sun faɗa abu iri ɗaya, to, dole ne a karɓi shaidarsu.
18 To, ni ina ba da shaida wa kaina, Uba kuma wanda ya aiko ni shi ne na biyun.”
19 Sai suka tambaye shi suka ce, “Ina Uban nan naka yake?” Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba ku san ni ba, ba ku kuma san Ubana ba. Da kun san ni, da kun san Ubana ma.”
20 Yesu ya faɗa wannan magana ne a lokacin da yake koyarwa kusa da inda ake ajiye kuɗin baiko a Haikali. Amma duk da haka ba wanda ya kama shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.
21 Sai Yesu ya ƙara gaya wa mutanen cewa, “Zan tafi, za ku kuwa neme ni, za ku kuma mutu cikin zunubinku. Inda za ni kuwa, ba za ku iya zuwa ba.”
22 Wannan ya sa shugabannin Yahudawa suka ce, “Wato, zai kashe kansa ne da ya ce, ‘Inda za ni kuwa, ba za ku iya zuwa ba’?”
23 Amma Yesu ya ci gaba da cewa, “Ku daga nan ƙasa kuke, ni kuwa na fito daga sama ne. Ku na duniyar nan ne, ni kuwa ba na duniyar nan ba ne.
24 Shi ya sa na ce muku za ku mutu cikin zunubanku. Domin in ba ku ba da gaskiya cewa ni ne shi wanda na gaya muku nake ba, za ku mutu cikin zunubanku.”
25 Sai suka tambayi Yesu suka ce, “Kai wane ne?” Yesu ya amsa musu ya ce, “Ni ne wannan da na faɗa muku tun daga farko.
26 Akwai abubuwa da yawa da zan iya faɗa game da ku, in kuma hukunta. Amma ina gaya wa mutane abubuwan da na ji daga wurin wanda ya aiko ni ne kaɗai, kuma yana faɗin gaskiya ne.”
27 Mutanen ba su gane cewa yana magana da su ne game da Uban ba.
28 Shi ya sa Yesu ya ce musu, “A lokacin da za ku ɗaga Ɗan Mutum, a lokacin nan ne za ku gane ni ne shi. Za ku gane cewa ba na yin kome da ikon kaina, amma ina faɗin abin da Uba ya koya mini ne kawai.
29 Wanda ya aiko ni kuwa yana tare da ni, bai bar ni ni kaɗai ba, gama kullum ina yin abin da yake so.”
30 A lokacin da Yesu yake faɗin waɗannan abubuwa mutane da yawa suka gaskata da shi.
31 Sai Yesu ya ce wa Yahudawan nan da suka gaskata da shi, “In dai kun ci gaba da riƙe koyarwata, ku almajiraina ne na gaske.
32 Saˈan nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ba ku ˈyanci.”
33 Suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne, ba mu taɓa zama bawan kowa ba. To, me ya sa ka ce za mu sami ˈyanci?”
34 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Gaskiya, ina gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne.
35 Ai, bawa ba ya zama a gida har abada, amma ɗa na gida ne har abada.
36 Saboda haka idan Ɗan ya ˈyantar da ku za ku sami ˈyanci na gaske.
37 Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuna so ku kashe ni, domin ba ku karɓi koyarwata ba.
38 Ina faɗa muku abin da na gani a wurin Ubana, amma ku kuna yin abin da kuka ji daga ubanku.”
39 Suka amsa masa suka ce, “To, ai, Ibrahim ne ubanmu.” Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “In da ku ˈyaˈyan Ibrahim ne, da kun yi abubuwan da shi Ibrahim ya yi.
40 Ni mutum ne mai faɗin gaskiya wadda na ji daga wurin Allah, amma kuna ƙoƙari ku kashe ni. To, ai, Ibrahim bai yi irin wannan abu ba.
41 Saboda haka kuna yin abin da ubanku yake yi ne.” Amma Yahudawan suka ce, “Mu ba shegu ba ne. Allah ne Ubanmu, kuma shi ne kaɗai Uban da muke da shi.”
42 Yesu ya ce musu, “Da a ce Allah ne Ubanku da kun ƙaunace ni, domin daga wurin Allah na fito, yanzu ga ni a nan. Ban zo da ikon kaina ba, Allah ne ya aiko ni.
43 Me ya sa ba ku gane maganata ba? Saboda ba ku iya saurari koyarwata ba.
44 Ku na ubanku Shaiɗan ne, kuma kuna so ku yi abin da yake so. Shi mai kisa ne tun farko kuma ba ruwansa da gaskiya, domin babu gaskiya a cikinsa. Duk lokacin da yake ƙarya yana nuna halinsa ne, gama shi mai ƙarya ne, uban ƙarya kuma.
45 Amma saboda ina faɗin gaskiya, ba ku gaskata da ni ba.
46 Wane ne a cikinku yana da shaida wadda ta nuna na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya nake faɗa, to, me ya sa ba ku gaskata ba?
47 Wanda yake na Allah yakan saurari abin da Allah yake faɗa. Amma ku ba ku saurari abin da Allah ya faɗa ba don ku ba na Allah ba ne.”
48 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ashe, ba gaskiyarmu ba kuwa, da muka ce kai mutumin Samariya ne wanda yake da aljani?”
49 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ba mai aljani ba ne. Ina girmama Ubana ne, amma ku kuwa kuna ƙasƙantar da girmana.
50 Ba ni nake nema wa kaina ɗaukaka ba. Akwai wani wanda yake nema mini, shi ne kuma mai yin hukunci.
51 Hakika, ina gaya muku, duk wanda yake biyayya da koyarwata ba zai taɓa mutuwa ba sam.”
52 Sai Yahudawan suka ce masa, “To, yanzu kam, mun tabbata kana da aljani. Ai, Ibrahim da annabawa sun mutu, amma kai ka ce, ‘Duk wanda yake biyayya da koyarwata ba zai taɓa mutuwa ba sam.’
53 Kana tsammani ka fi babanmu Ibrahim ne? Shi kuwa ya mutu, haka nan ma annabawa sun mutu. Kana tsammani kai wane ne?”
54 Yesu ya amsa musu ya ce, “Idan na ɗaukaka kaina, wannan ɗaukaka ba a bakin kome take ba. Wanda yake ɗaukaka ni shi ne Ubana, wanda kuke cewa wai shi ne Allahnku.
55 Ku ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Da a ce na ce muku ban san shi ba, da na zama mai ƙarya kamarku. Amma na san shi, ina kuma biyayya da abin da yake faɗa.
56 Ga shi ubanku Ibrahim ya yi farin ciki sosai don dai yă sami ganin zamanina, ya kuwa gan shi, ya kuma yi murna.”
57 Sai Yahudawa suka ce wa Yesu, “Ga shi, har yanzu ba ka ma kai shekara hamsin ba tukuna, kuma kana cewa ka ga Ibrahim?”
58 Yesu ya ce musu, “Gaskiya, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ina nan.”
59 Da Yesu ya faɗa wannan magana sai suka ɗebo duwatsu domin su jejjefe shi. Amma Yesu ya ɓoye kansa, ya fita ya bar Haikalin.