Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 21
1 Saˈad da muka bar su, muka shiga jirgin ruwa muka miƙe sai Kos, washegari kuma sai Rodes, daga nan kuma sai Fatara.
2 Da muka sami jirgin da zai je ƙasar Finikiya, sai muka shiga muka tafi.
3 Da muka fara hangen Sayifurus, muka mai da shi hagunmu, muka ci gaba da tafiya har ƙasar Suriya. Sai muka sauka a Taya, don a nan ne jirgin zai sauke kayansa.
4 Da muka sami inda masu bi suke, muka zauna a nan kwana bakwai. Sai Ruhu ya zuga su suka gaya wa Bulus kada yă je Urushalima.
5 Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu. Dukan masu bi kuma har da matansu da ˈyaˈyansu suka raka mu har bayan gari. Saˈan nan muka durƙusa a gefen ruwa muka yi adduˈa,
6 muka yi wa juna ban kwana. Saˈan nan muka shiga jirgi, su kuma suka koma gida.
7 Da muka gama tafiyarmu daga Taya, muka kai Tolemayis, muka gaisa da ˈyanˈuwa, muka kuma yi kwana ɗaya a wurinsu.
8 Washegari muka tashi muka je Kaisariya, muka shiga gidan Filibus mai waˈazi, wanda yake ɗaya daga cikin bakwai ɗin nan waɗanda aka zaɓa domin hidimar jamaˈar masu bi a Urushalima, muka sauka a wurinsa.
9 Yana da ˈyaˈya huɗu ˈyan mata waɗanda ba su yi aure ba. Su masu yin annabci ne.
10 To, bayan da muka yi ˈyan kwanaki a wurin, sai wani annabi mai suna Agabus ya zo daga yankin Yahudiya.
11 Da Agabus ya zo wurinmu, sai ya ɗauki ɗamara ta Bulus. Sai shi Agabus ya ɗaure hannuwansa da ƙafafunsa ya ce, “Ga abin da Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai ɗamarar nan, su kuma ba da shi ga waɗanda ba Yahudawa ba.’ ”
12 Da muka ji haka, mu da mutanen da suke wurin muka roƙi Bulus kada yă je Urushalima.
13 Sai Bulus ya amsa ya ce, “Don me kuke yin haka? Me ya sa kuna kuka kuna ɓata mini zuciya? Ai, a shirye nake ba ma a ɗaure ni kawai ba, har ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”
14 Tun da ba mu iya sa ya canja raˈayinsa ba, sai muka yi shiru, muka ce, “Bari nufin Ubangiji yă cika.”
15 Bayan kwanakin nan muka shirya muka tafi Urushalima.
16 Waɗansu almajirai daga Kaisariya suka raka mu, suka kai mu wurin Manason wanda za mu sauka a wurinsa, shi mutumin Sayifurus ne, ɗaya daga cikin almajirai na farko.
17 Da muka zo Urushalima, ˈyanˈuwa suka karɓe mu da murna.
18 Washegari Bulus ya tafi tare da mu zuwa wurin Yakub, dattawan jamaˈar masu bi kuwa duka suna nan.
19 Bayan ya gaisa da su, sai ya bayyana musu dalla-dalla abubuwan da Allah ya yi a cikin waɗanda ba Yahudawa ba ta wurin aikin da shi Bulus ya yi.
20 Da suka ji haka, suka yi wa Allah yabo. Suka ce wa Bulus, “To, ka gani ɗanˈuwa, dubban mutane a cikin Yahudawa sun ba da gaskiya, dukansu kuwa masu kishin bin Koyarwar Musa ne.
21 An gaya musu labarinka, wai kana koya wa dukan Yahudawan da suke cikin waɗanda ba Yahudawa ba su yar da Koyarwar Musa. Wato, kana ce musu kada su yi wa ˈyaˈyansu kaciya, ko kuwa su bi sauran alˈadunmu.
22 To, yaya za mu yi? Lallai za su ji labarin zuwanka.
23 Saboda haka sai ka yi abin da za mu faɗa maka. Muna da mutum huɗu a nan da suka yi rantsuwa.
24 Sai ka tafi da su ku bi ƙaˈidar Koyarwa ta tsabtacewa gaba ɗaya, ka kuma biya kuɗin tsabtacewar don a yi musu aski. Ta haka kowa zai sani cewa duk abin da aka gaya musu game da kai ba gaskiya ba ne, za a ga cewa kai kana kiyaye Koyarwar Musa.
25 Amma game da waɗanda ba Yahudawa ba da suka ba da gaskiya, mun riga mun aika wasiƙa a kan mun yanke hukunci cewa, kada su ci abin da aka miƙa wa gunki hadaya, kada su yi lalata, kada su ci naman dabbar da aka murɗe ko nama tare da jini.”
26 Washegari Bulus ya ɗauki mutanen nan suka tsabtace tare. Saˈan nan ya shiga Haikali domin yă sanar da ranar cikar tsabtacewarsu, wato ranar da za a ba da baiko domin kowane ɗayansu.
27 Da kwana bakwai ɗin suka kusan cika, waɗansu Yahudawa daga Asiya suka ga Bulus a Haikali. Sai suka zuga taron mutane, suka kama shi,
28 suna ihu suna cewa, “Ku ˈyanˈuwa Israˈilawa, ku taimaka! Ga mutumin nan da yake bi koˈina yana zagin mutanenmu, da Koyarwarmu, da kuma wannan Haikalinmu. Har ma ya kawo waɗansu Helenawa a cikin Haikali ya ƙazantar da wurin nan mai tsarki.”
29 Sun ce haka ne saboda dā ma sun ga Bulus tare da Turofimus, mutumin Afisa, a cikin gari. Wannan ne ya sa suka yi tsammani Bulus ya shigo tare da shi a cikin Haikalin.
30 Sai duk garin ya ruɗe, jamaˈa suka taso gaba ɗaya a guje suka kama Bulus, suka fitar da shi daga Haikali, aka kuma rufe ƙofofin nan da nan.
31 Suna ƙoƙari su kashe shi ke nan, sai labari ya kai wurin shugaban ƙungiyar sojoji cewa Urushalima tana cikin rikici ainun.
32 Nan take ya ɗibi sojoji da manyan sojojin Roma, suka tafi wurin da gudu. Da jamaˈar suka ga shugaban da sojojinsa, sai suka daina dūkan Bulus.
33 Sai shugaban ya zo ya kama Bulus, ya sa a ɗaure shi da sarƙa biyu. Saˈan nan ya yi tambaya ko shi wane ne, da kuma abin da ya yi.
34 Taron kuwa suna ta hayaniya, waɗansu su ce wannan, waɗansu su ce wancan. Saboda yawan hayaniyar shugaban bai iya samun ainihin tushen maganar ba, sai ya ba da umarni a kai Bulus barikin soja.
35 Da Bulus ya zo bakin matakala, sai da sojoji suka ɗauke shi saboda rikicin taron ya yi yawa.
36 Gama taron mutanen da suka biyo sun yi ta ihu suna cewa, “A yi gaba da shi!”
37 An kusa shigar da Bulus barikin soja ke nan, sai ya ce wa shugaban, “Ko ka yarda in yi magana da kai?” Sai shugaban ya ce, “Ashe ka iya Helenanci?
38 Ba kai ne mutumin Masar nan da shekarun baya ya jawo tawaye ba, har ya ja mutanen nan dubu huɗu masu kisan kai a daji?”
39 Sai Bulus ya amsa ya ce, “Ai, ni Bayahude ne na Tarsus a ƙasar Kilikiya. Ni ɗan birni mai muhimminci ne. Ina roƙonka, ka bar ni in yi wa mutanen nan magana.”
40 Sai ya ba shi izni, Bulus kuwa ya tsaya a kan matakala, ya ɗaga wa jamaˈa hannu su yi shiru. Da suka yi tsit, sai ya yi musu magana da yaren Aramaya.