Skip to content

Hausa Bible

Luka 8

1 An jima kaɗan sai Yesu ya zazzaga garuruwa da ƙauyuka, yana waˈazi yana shelar labari mai daɗi na mulkin Allah. Almajiransa sha biyun nan kuwa suna tare da shi,

2 da waɗansu mata waɗanda aka raba su da mugayen ruhohi aka kuma warkar da su daga rashin lafiyarsu. A cikinsu kuwa akwai Maryamu daga Magadala, wadda aka fitar da aljanu bakwai daga cikinta.

3 Akwai kuma Yowana matar Kuza, shugaban gidan Hirudus, tare da Suzanna, da waɗansu mata da yawa waɗanda suke yi musu hidima da kayansu.

4 Da mutane da yawa suna ta taruwa daga garuruwa dabam-dabam suna ta zuwa wurin Yesu, sai ya ba su wannan misali.

5 “An taɓa yin wani mutumin da ya je yă shuka iri a gonarsa. Yana cikin yafa iri ke nan, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattaka su, sai tsuntsaye kuma suka cinye su.

6 “Waɗansu suka fāɗi a kan dutse. Da suka tsira sai suka bushe saboda babu ruwa a wurin.

7 Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙayoyi, suka yi girma tare, har ƙayoyi suka sha ƙarfinsu.

8 Waɗansu irin kuma suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka yi tsaba ɗari-ɗari.” Da Yesu ya gama faɗin haka sai ya ɗaga murya ya ce, “Bari mai kunnen ji, yă ji!”

9 Saˈad da almajiran Yesu suka tambaye shi maˈanar misalin nan,

10 sai ya ce, “An yarda muku ku san asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane ina magana da misalai ne domin, “ ‘Ko sun duba ba za su gani ba, ko sun ji ba za su gane ba.’ ”

11 “Ga maˈanar misalin nan. Irin shi ne kalmar Allah.

12 Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne kwatancin mutanen da suka ji, amma Shaiɗan ya zo ya ƙwace kalmar daga zuciyarsu, domin kada su ba da gaskiya su kuma sami ceto.

13 Irin da suka fāɗi a kan dutsen kuwa, su ne kwatancin mutanen nan da suka ji kalmar, suka kuma karɓe ta da farin ciki. Amma ba ta yi tushe a cikinsu ba. Sun ba da gaskiya na ɗan lokaci, amma saˈad da gwaji ya taso musu, sai suka watsar da bangaskiyarsu.

14 Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne kwatancin mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, sai damuwar duniya da neman arziki, da son jin daɗi, ya sa sun kāsa ba da amfani.

15 Irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne kwatancin mutanen da suka ji kalmar, suka kuma karɓa da zuciya ɗaya suka riƙe, suka jimre suka ba da amfani.

16 “Ba wanda zai kunna fitila yă ɗauki kwano yă rufe ko kuwa yă sa ta a ƙarƙashin gado. A maimakon haka, zai sa ta a kan sanda mai riƙe fitilu domin mutanen da za su shiga su ga haske.

17 “Gama ba abin da yake a ɓoye, wanda ba za a bayyana ba, kuma ba abin da yake asiri, wanda ba za a tone shi a fili ba.

18 “Ku yi hankali fa da yadda kuke ji, domin wanda yake da abu, za a ƙara masa, amma wanda ba shi da abu, abin da yake tsammani yana da shi ma, za a karɓa daga gare shi.”

19 Saˈan nan mamar Yesu da ˈyanˈuwansa suka je wurinsa, amma ba su iya kai wurinsa ba saboda yawan mutane.

20 Sai wani mutum ya gaya wa Yesu cewa, “Ga mamarka da ˈyanˈuwanka suna tsaye a waje suna so su gan ka.”

21 Yesu ya ce wa dukan mutanen da suke wurin, “Waɗanda suka ji kalmar Allah, suka kuma aikata, su ne mamata da ˈyanˈuwana.”

22 Wata rana Yesu da almajiransa suka shiga jirgin ruwa, sai ya ce musu, “Mu haye zuwa wancan gefen tekun.” Sai suka fara tafiya.

23 Da suke cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Ba labari sai babban hadari mai iska ya taso a tekun. Suka shiga wani hatsari, saboda ruwa ya fara shiga cikin jirgin.

24 Almajiran suka je, suka tā da Yesu, suka ce, “Maigirma! Maigirma! Za mu halaka!” Yesu ya tashi, ya tsawata wa iskar da kuma ruwan da yake hauka, sai suka yi tsit.

25 Sai ya ce wa almajiran, “Ina bangaskiyarku?” Amma suka ji tsoro sosai, suka kuma yi mamaki, suna ce wa juna, “Wane ne wannan wanda yake wa iska da raƙuman ruwa umarni har suna yi masa biyayya?”

26 Yesu da almajiransa suka yi ta tafiya a cikin jirgin ruwa har suka kai sashen yankin Garasinawa wanda yake a hayin Tekun Galili.

27 Yesu yana sauka daga jirgin ke nan sai ga wani mutumin garin wanda yake da aljanu. Mutumin ya daɗe yana yawo ba riga, kuma ba ya iya zama a gida, kullum yana wurin da ake binne mutane.

28 Da ganin Yesu, sai mutumin ya fāɗi a gaban Yesu, ya tā da murya da ƙarfi yana ihu yana cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba!”

29 Ya faɗa haka ne gama Yesu ya riga ya tsawata wa ƙazamin ruhu yă bar shi. Domin sau da yawa ƙazamin ruhun yakan buge shi. Ko da yake akan tsare shi ƙafa da hannu duk a ɗaure da sarƙa, duk da haka yakan tsintsinke sarƙoƙin. Aljanin kuma yakan kore shi zuwa hamada.

30 Yesu ya tambaye shi, “Mene ne sunanka?” Sai mutumin ya amsa, “Sunana Tuli ne,” gama aljanun suna da yawa a cikinsa.

31 Suka yi ta roƙonsa kada yă tura su a ramin da ake tsare aljanu a ciki.

32 Kusa da wurin nan kuwa, akwai wani babban garken aladun da yake kiwo a gangaren tudun. Sai aljanun suka roƙi Yesu yă bar su su shiga cikin aladun. Shi kuwa ya yarda musu.

33 Suka fita daga cikin mutumin suka shiga cikin aladun. Sai dukan aladun suka tashi a guje suka gangara cikin tekun, suka mutu a ciki.

34 Da masu lura da aladun suka ga abin da ya faru, sai suka gudu zuwa gari da ƙauyuka domin su kai labari.

35 Mutane suka fito domin su ga abin da ya faru. Da suka kai wurin Yesu, suka ga mutumin da aljanun suka fito daga cikinsa yana zama kusa da Yesu, ya sa riga yana kuma hankalinsa ɗaya. Sai tsoro ya kama su duka.

36 Waɗanda suke nan lokacin da abin ya faru, suka yi ta gaggaya wa mutane yadda aka warkar da mutumin.

37 Sai dukan mutanen kewayen yankin Garasinawa suka roƙi Yesu yă bar garinsu, don sun ji tsoro sosai. Da Yesu zai shiga jirgi yă tafi ke nan,

38 sai mutumin da aka fitar da aljanu daga cikinsa ya zo, ya roƙi Yesu yana cewa, “Bari in tafi tare da kai.” Amma Yesu ya sallame shi ya ce,

39 “Koma gida, ka yi shelar manyan abubuwan da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi ya bi ta cikin garin, yana faɗin abin da Yesu ya yi masa.

40 Da komawar Yesu daga wancan gefen tekun, mutane suka yi masa maraba don dā ma suna jiransa ne.

41 Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, wanda yake shugaban majamiˈa ya zo ya durƙusa a gaban Yesu, ya roƙe shi yă je gidansa,

42 domin wadda take ˈyarsa kaɗai, wadda ta kai shekara goma sha biyu, tana bakin mutuwa. Da Yesu ya kama hanya, mutane suka yi ta binsa suna matsa shi a ta kowane gefe.

43 A cikinsu kuwa akwai wata mace wadda ta sha wahala da ciwon zub da jini na tsawon shekara goma sha biyu. Ta kashe duk abin da take da shi wurin neman magani, amma ba wanda ya iya warkar da ita.

44 Sai ta bi ta cikin yawan mutanen nan ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Sai zub da jinin nan nata ya tsaya cik.

45 Yesu ya ce, “Wa ya taɓa ni?” Kowa ya ce ba shi ba ne, sai Bitrus ya ce, “Maigirma, ai, mutane sun kewaye ka ta kowane gefe, suna matsarka.”

46 Amma Yesu ya ce, “Ni dai, wani ya taɓa ni, gama na ji iko ya fita daga gare ni.”

47 Da matar ta ga dai an gane ta, sai ta fita, jikinta yana rawa, ta fāɗi a gaban Yesu. Ta kuma bayyana masa a gaban kowa dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take.

48 Yesu ya ce mata, “ˈYata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”

49 Bai ma ƙāre maganar ba, sai ga ɗan aika daga gidan Yayirus, ya zo, yana gaya wa Yayirus cewa, “Kada ma ka sa malam ya yi wata wahala, ai, ˈyarka ta mutu ko.”

50 Da Yesu ya ji haka, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka dai ba da gaskiya, za ta sāke rayuwa.”

51 Da suka kai gidan, bai yarda kowa yă shiga tare da shi ba sai Bitrus da Yohanna da Yakub, da kuma baban yarinyar da mamarta.

52 Dukan mutanen da suke gidan, sai kuka suke yi suna ihu domin yarinyar. Yesu ya ce musu, “Kada ku yi kuka, yarinyar ba ta mutu ba, tana barci ne kawai!”

53 Sai suka yi masa dariyar reni, domin sun sani ta mutu.

54 Yesu kuwa da ya kama hannunta sai ya tā da murya ya ce, “Yarinya, ki tashi!”

55 Ranta kuma ya dawo, ta tashi tsab, sai Yesu ya umarta a ba ta abinci ta ci.

56 Iyayenta suka kama baki suna mamaki, amma Yesu ya ja musu kunne cewa kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.

Open Bible reader