Skip to content

Hausa Bible

Romawa 11

1 To, ina tambaya, Allah ya ƙi mutanensa ke nan? Ina! Ko kaɗan! Ni da kaina mutumin Israˈila ne, daga zuriyar Ibrahim, kuma mutumin zuriyar Benyamin.

2 Allah bai ƙi mutanensa waɗanda ya zaɓa tun daga farko ba. Kun dai san abin da Rubutacciyar Maganar Allah ta faɗa game da Iliya, wato yadda shi Iliya ya kai kuka ga Allah a kan Israˈila cewa,

3 “Ubangiji, sun kakkashe annabawanka, sun kuma rurrushe bagadanka. Ni ne kaɗai na rage, kuma suna nema su kashe ni.”

4 Wace amsa ce Allah ya ba shi? Ya amsa da cewa, “Na yi wa kaina ajiyar mutane dubu bakwai waɗanda ba su durƙusa su yi wa allahn nan Baˈal bauta ba.”

5 Haka wannan ya kasance a yanzu ma. Akwai ragowar mutane waɗanda Allah ya zaɓa bisa ga alherinsa.

6 Zaɓen nan da Allah ya yi kuwa ya dogara ga alherinsa ne, ba ga ayyukan da mutanen suka yi ba. Gama in ba haka ba, alheri bai zama alheri na gaske ba.

7 To, yaya ke nan? Ai, Israˈilawa sun kāsa samun abin da suke nema. Sai dai waɗansu kaɗan da aka zaɓa a cikinsu ne sun samu, amma sauran sun zama masu taurin kai.

8 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Allah ya ba su ruhun rashin ganewa, da idanun da ba sa gani, da kunnuwan da ba sa ji. Wannan kuwa ya ci gaba har wa yau.”

9 Kuma Dawuda ya ce, “Bari bikinsu yă zama musu tarko, abin jawo musu hatsari. Bari yă sa su yi tuntuɓe yă jawo musu hukunci.

10 Bari idanunsu su yi duhu har su kāsa gani, nauyin wahala kuma yă zuba musu nauyi har abada.”

11 Har yanzu ina tambaya. Da Israˈilawa suka yi tuntuɓe, sun fāɗi har ba za su tashi ba ke nan? Ina! Ko kaɗan! Saboda zunubinsu ceto ya kai ga waɗanda ba Yahudawa ba, don a sa Israˈilawa su ji kishinsu.

12 In kuwa zunubin da suka yi ya kawo wa duniya albarka, in kuma kāsawarsu ta kawo albarku ga waɗanda ba Yahudawa ba, to, yaya fa albarkar nan za ta zama a lokacin da yawan Israˈilawa ya cika ɗungum?

13 Yanzu, da ku waɗanda ba Yahudawa ba nake magana. Tun da yake ni manzon Yesu ne ga waɗanda ba Yahudawa ba, zan yi ɗan taƙama da aikin nan nawa.

14 Ta yin haka ina fata cewa zan iya sa jamaˈata Israˈila su ji kishi, har ma wannan yă sa a ceci waɗansunsu.

15 Gama idan ƙinsu da aka yi, ya zama abin buɗe hanyar shirya tsakanin Allah da duniya, a saˈad da za a karɓe su fa, ba samun rai daga matattu ne wannan zai kawo ba?

16 Idan an keɓe sashe ɗaya na burodin hatsin nunan fari ta hanyar miƙa shi ga Allah, an keɓe dukan burodin da tsarki ke nan. Idan kuma aka keɓe wa Allah saiwar itace, dukan rassan itacen ma an keɓe su da tsarki ke nan.

17 To, an sassare waɗansu rassan itacen zaitun irin wanda aka nome, sai aka ɗauki wani reshen itacen zaitun irin na daji, aka kuma yi musu aure. Ku waɗanda ba Yahudawa ba kuwa, kamar reshen itacen zaitun na daji kuke, ku ne aka haɗa ku da tushen nan, wato Yahudawa, waɗanda daga gare su ne kuke samun albarkun Allah.

18 Saboda haka kada ku yi taƙama a kan cewa kun fi waɗancan rassan da aka sassare. Idan kuwa kuna taƙama, sai ku tuna cewa ba tushen ne yake dogara a gare ku ba, sai dai ku ne kuke dogara ga tushen.

19 Amma kana iya cewa, “Ai, an sassare rassan ne domin a sami dama a haɗa ni da tushen.”

20 Ƙwarai kuwa! Amma saboda rashin bangaskiya ne aka sassare su daga tushen, kai kuma bisa ga bangaskiya ne kake da zarafin zama haɗe da tushen. Saboda haka kada ka yi taƙama, a maimakon haka, ka ji tsoro.

21 Gama idan Allah bai bar rassan nan waɗanda su ne ainihin na tushen ba, kai ma ba zai bar ka ba.

22 A nan muna iya ganin yadda Allah yake da alheri da kuma tsanani. Ya nuna tsananinsa ga waɗanda suka fāɗi, amma ya nuna alherinsa a gare ka, wato, idan ka ci gaba da zama cikin alherinsa. Idan kuwa ba ka ci gaba da haka ba, kai ma za a sare ka daga tushen ke nan.

23 Idan kuwa su Israˈilawa ba su ci gaba da rashin bangaskiya ba, za a haɗa su da tushen, don Allah yana iya yă sāke mai da su a tushen.

24 Ku waɗanda ba Yahudawa ba dai, kuna kamar itacen zaitun nan irin na daji wanda bayan da aka saro shi, sai aka haɗa masa aure da itacen zaitun irin wanda aka nome. Wannan kuwa da aka yi ba bisa ga ƙaˈidar auren itatuwa ba ne. To, tun da yake su Israˈilawa su ne kamar irin itacen zaitun wanda aka nome, zai zama abu mai sauƙi sosai ga Allah yă sāke mai da rassan nan da aka sare a itacen nan wanda shi ne asalinsu.

25 Bāna so ku kasance da rashin sanin wannan asiri ˈyanˈuwa, domin kada ku ɗauki kanku ku masu hikima ne. Taurin zuciya ya faru ga sashe na Israˈila har dukan yawan waɗanda ba Yahudawa ba da za su shiga wurin Allah yă cika.

26 Ta haka za a ceci dukan Israˈila. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai Ceto zai zo daga Sihiyona. Zai kawar da duk ƙin bin Allah daga zuriyar Yakub.

27 Wannan ita ce yarjejeniyata da su, a saˈad da zan ɗauke musu zunubansu.”

28 Game da ƙin labari mai daɗin da suka yi, Yahudawa suka zama masu gāba da Allah. Wannan kuma domin amfaninku ne. Amma game da zaɓensu da aka yi, su mutane ne da Allah yake ƙauna. Wannan kuwa albarkacin kakannin kakanninsu ne.

29 Gama kyautai na Allah da kiransa ba abubuwa ne da Allah zai janye ba.

30 A dā ku waɗanda ba Yahudawa ba, ku masu rashin biyayya ga Allah ne, amma yanzu kam kun sami jinƙai ta wurin rashin biyayyar Yahudawa.

31 Haka kuma su Yahudawa sun zama masu rashin biyayya ga Allah a yanzu. Wannan kuwa domin su sami jinƙai ne ta wurin jinƙan nan da Allah ya nuna muku.

32 Gama Allah ya mai da dukan mutane kamar ˈyan kurkuku na rashin biyayyarsu. Ya yi haka domin yă nuna jinƙai ga dukansu.

33 Ina misalin zurfin yawan hikimar Allah! zurfin saninsa kuma marar iyaka ne! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincike, hanyoyin alˈamuransa sun wuce gaban ganewa!

34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Wa ya taɓa zama abokin shawararsa?”

35 “Wa ya taɓa ba Allah wani abu har da zai zama dole Allah yă mayar masa?”

36 Gama shi ne ya halicci dukan abubuwa, kuma abubuwan nan duka suna kasancewa ta wurinsa ne kuma dominsa. Bari ɗaukaka ta tabbata ga Allah har abada! Amin.

Open Bible reader