Hausa Bible
Romawa 11:24
Ku waɗanda ba Yahudawa ba dai, kuna kamar itacen zaitun nan irin na daji wanda bayan da aka saro shi, sai aka haɗa masa aure da itacen zaitun irin wanda aka nome. Wannan kuwa da aka yi ba bisa ga ƙaˈidar auren itatuwa ba ne. To, tun da yake su Israˈilawa su ne kamar irin itacen zaitun wanda aka nome, zai zama abu mai sauƙi sosai ga Allah yă sāke mai da rassan nan da aka sare a itacen nan wanda shi ne asalinsu.
Open Bible reader