Hausa Bible
Markus 14
1 Sauran kwana biyu a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan Firistoci da malaman Koyarwar Musa suka nemi hanya su kama Yesu a ɓoye, su kashe shi.
2 Amma suna cewa, “Ba dai a lokacin biki ba, domin kada mutane su tā da rikici.”
3 Yesu yana Betani a gidan wani mutum wanda ake ce da shi Siman mai cutar fatar jiki. Yana cin abinci ke nan, sai ga wata mace ta zo da wata ˈyar kwalabar da aka yi da dutsen onis cike da man ƙanshi mai tsada sosai wanda aka yi da nardi zalla. Sai ta fashe kwalabar ta zuba man a kan Yesu.
4 Waɗansu kuwa da suke wurin suka ji haushi, suka ce wa juna, “Yaya aka ɓata wannan mai haka?
5 Da an sayar da shi kuwa, da an sami yawan kuɗin da ake biyan lebura yini ɗari uku a ba talakawa, ai, da ya fi!” Sai suka tsawata wa matar sosai.
6 Amma Yesu ya ce, “Ku bar ta mana. Don me kuke damunta? Ai, abu mai kyau ne ta yi mini.
7 Masu bukata suna tare da ku kullum. Ko yaushe kuke so, kuna iya yi musu alheri, amma ba kullum ne nake tare da ku ba.
8 Ta yi iyakacin ƙoƙarinta. Ta shafa jikina da mai domin shirin binnewata.
9 Hakika ina gaya muku, duk inda za a yi shelar labarin nan mai daɗi a duniya duka, za a dinga faɗin abin da macen nan ta yi domin tunawa da ita.”
10 Ana nan, sai Yahuda Iskariyoti ɗaya daga cikin almajirai sha biyun nan, ya je wurin manyan firistoci domin yă bashe Yesu a gare su.
11 Da suka ji haka suka yi murna sosai, har suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Yahuda kuwa ya fara neman hanya domin yă bashe shi.
12 A ranar farko ta Bikin Burodi Marar Yisti, wato ran da akan yanka ɗan rago na Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka cin Bikin Ƙetarewa?”
13 Sai ya aika almajiransa guda biyu, ya ce musu, “Ku shiga gari. Can za ku gamu da wani mutum yana ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi.
14 Duk gidan da ya shiga, ku ce wa maigidan, ‘Malam yana tambaya cewa ina ɗakin da zai ci Bikin Ƙetarewa da almajiransa?’
15 Shi kuwa zai nuna muku wani babban ɗakin sama wanda aka gama gyaransa don bikin. A wurin za ku shirya mana abinci.”
16 Sai almajiran suka tashi, suka shiga cikin gari, suka kuwa sami abubuwa kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya abincin Bikin Ƙetarewa.
17 Da yamma ta yi, Yesu da almajiransa sha biyun nan suka zo gidan.
18 Suna cin abinci ke nan, sai Yesu ya ce, “Hakika ina gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wanda yanzu yake cin abinci tare da ni.”
19 Sai almajiran suka fara baƙin ciki, suna ce masa da ɗaya-ɗaya, “Ko ni ne?”
20 Yesu ya amsa, ya ce, “Ɗaya daga cikinku sha biyun nan ne dai, wanda muke ci daga ƙwarya ɗaya.
21 Ɗan Mutum zai mutu, kamar yadda yake a rubuce game da shi. Amma kaiton wanda zai ba da Ɗan mutum! Zai fiye wa mutumin nan da ma ba a haife shi ba.”
22 Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ga Allah, ya kakkarya, ya ba almajiransa, ya ce, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”
23 Bayan wannan kuma, ya ɗauki kwaf na ruwan inabi ya yi godiya ga Allah, ya ba su. Dukansu kuwa suka sha daga ciki.
24 Saˈan nan ya ce musu, “Wannan jinina ne. Jini na cikar yarjejeniyar. Za a zubar da shi saboda mutane da yawa.
25 Ina gaya muku gaskiya, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba, sai dai a ranar da zan sha wani sabon a mulkin Allah.”
26 Bayan da suka rera waƙa, sai suka fita suka tafi Tudun Itatuwan Zaitun.
27 Yesu ya ce wa almajiransa, “Dukanku za ku gudu ku bar ni, kamar yadda aka rubuta cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin, tumakin kuma za su gudu.’ ”
28 “Amma bayan da na tashi daga matattu, zan riga ku zuwa Galili.”
29 Sai Bitrus ya ce masa, “Ko dukansu sun gudu sun bar ka, ni kam, ba zan bar ka ba.”
30 Yesu ya ce masa, “Gaskiya ina gaya maka, yau, a cikin daren nan, kafin zakara yă yi cara sau biyu, za ka yi musūn sanina sau uku.”
31 Amma Bitrus ya yi ta maimaitawa da ƙarfi yana cewa, “Ko da za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musūn saninka ba sam.” Dukan sauran almajiransa ma suka faɗa haka.
32 Suka tafi wani wurin da ake ce da shi Getsemani wato, wurin matsewar ˈyaˈyan zaitun, sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan. Zan je in yi adduˈa.”
33 Sai ya ɗauki Bitrus, da Yakub, da Yohanna tare da shi. Ana nan, sai ya fara damuwa ƙwarai, har jikinsa ya yi sanyi.
34 Sai ya ce musu, “Baƙin ciki da yake a raina zai iya kashe ni. Ku zauna a nan, ku yi tsaro.”
35 Da ya je gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi adduˈa ya ce, idan ya yiwu, a ɗauke masa wannan lokacin wahala.
36 Ya ce, “Abba, Uba, kowane abu mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf na wahala. Duk da haka dai, ka yi abin da kake so, ba abin da ni nake so ba.”
37 Bayan wannan, sai ya dawo ya sami almajiran nan uku suna barci. Sai ya ce wa Bitrus, “Bitrus, kana barci ne? Ashe, ba za ka iya tsaro ko da awa ɗaya ba?
38 Ku yi tsaro kuna kuma adduˈa domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Lallai ruhu ya ɗauka, amma jikin ba ƙarfi.”
39 Sai ya sāke komawa, ya yi adduˈa, yana maimaita maganar dā.
40 Saˈan nan ya sāke dawowa, ya same su suna barci don idanunsu sun cika da barci sosai. Suka kuma rasa abin da za su faɗa masa.
41 Sai ya je ya dawo, na uku ke nan, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Shi ke nan! Lokaci ya yi da za a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi.
42 Ku tashi mu tafi! Ga mai bashe ni nan ya iso!”
43 Yesu yana cikin magana ke nan, sai ga Yahuda, ɗaya daga cikin almajiransa sha biyun nan, ya zo tare da mutane da yawa suna riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci, da malaman Koyarwar Musa, da shugabanni ne suka turo su.
44 Yahuda, wanda zai bashe shi kuwa, ya riga ya shirya musu alama cewa, “Wanda zan sumbace shi, shi ne mutumin. Ku kama shi ku tafi. Ku riƙe shi da kyau.”
45 Da zuwan Yahuda, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu, ya ce masa, “Malam!” Sai ya sumbace shi.
46 Sai mutanen kuwa suka kama Yesu suka riƙe shi da ƙarfi.
47 Amma ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake tsaye kusa, ya zare takobinsa, ya sari bawan babban firist, ya yanke masa kunne.
48 Yesu ya ce musu, “Kun fito da takuba da sanduna ku kama ni sai ka ce ɗan fashi?
49 Kowace rana ina tare da ku a Haikali ina koyarwa, ba ku kama ni ba. Ba kome. An yi haka ne fa domin annabcin Rubutacciyar Maganar Allah yă cika.”
50 Daga nan dukan almajiran suka bar shi, suka gudu.
51 Akwai wani saurayi ya bi Yesu, ba shi da riga, sai mayafi kawai. Da mutanen suka yi ƙoƙarin kama shi,
52 sai ya bar mayafinsa a hannunsu ya gudu tsirara.
53 Suka kai Yesu wurin babban firist, sai manyan firistoci, da shugabanni, da kuma malaman Koyarwar Musa suka taru duk a wurin.
54 Bitrus kuma ya bi Yesu, amma daga nesa. Ya bi shi har cikin filin gidan babban firist ɗin. A wurin ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta.
55 Manyan firistoci da sauran ˈyan majalisa suna ta neman wani abu da za a yi shaida a kan Yesu cewa ya yi laifi domin su kashe shi, amma ba su samu ba.
56 Mutane da yawa kam sun yi shaidar ƙarya, amma bakinsu bai zo ɗaya ba.
57 Daga baya waɗansu suka tashi tsaye, suka yi wa Yesu shaidar ƙarya suka ce,
58 “Mun ji ya ce, wai zai rushe Haikalin nan da mutane suka gina, yă gina wani cikin kwana uku, wanda ba ginin mutum ba.”
59 Duk da haka dai shaidarsu ba ta zo ɗaya ba.
60 Sai babban firist ya tashi ya tsaya a tsakiyarsu, ya tambayi Yesu, ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da suke bayar a kanka fa?”
61 Amma Yesu ya yi shiru, bai ba shi ko amsa ba. Sai babban firist ɗin ya sāke tambayarsa, “Ko kai ne Almasihu Ɗan Mai Albarka?”
62 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne. “Kuma za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa cikin girgije na sararin sama.”
63 Sai babban firist ya yage rigunansa, ya ce, “Wace shaida kuma muke bukata?
64 Kun dai ji saɓon da ya yi wa Allah! Mene ne raˈayinku?” Sai dukan mutane suka yanke masa shariˈa cewa a kashe shi.
65 Waɗansu ma suka fara tottofa masa miyau, suka ɗaure masa idanu, suka kuma mammare shi, suna ce masa, “Faɗa wanda ya mare ka!” Masu gadi kuma suka yi ta yin masa dūka.
66 Bitrus kuwa yana ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya a cikin maˈaikatan babban firist ta zo wurin.
67 Da ta ga Bitrus yana jin ɗumin wuta, sai ta dube shi da kyau, ta ce masa, “Ai, kai ma kana tare da Yesu Banazaret nan!”
68 Amma Bitrus ya yi musū, ya ce, “Ban san ma abin da kike magana ba. Ban gane ba sam!” Da faɗin haka, sai ya tashi ya je zauren gidan. Nan da nan sai zakara ya yi cara.
69 Da yarinyar ta sāke gan shi a wurin, sai ta faɗa wa waɗanda suke tsaye a wurin, “Wannan ma ɗaya daga cikinsu ne.”
70 Sai Bitrus ya sāke yin musū kuma. Bayan ɗan lokaci kaɗan, waɗanda suke tsaye kusa da Bitrus suka ce masa, “Ba shakka, kai ma ɗaya daga cikinsu ne. Kai ba mutumin Galili ba ne?”
71 Amma Bitrus ya fara zagi yana laˈanta kansa, yana rantsuwa kuma a gabansu, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan da kuke maganarsa ba.”
72 Nan da nan sai zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya faɗa masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu, za ka yi musūn sanina sau uku.” Da ya tuna wannan magana, sai ya fashe da kuka.