Skip to content

Hausa Bible

Yahaya 19

1 Saˈan nan Bilatus ya sa a yi wa Yesu bulala.

2 Sai sojoji suka yi wata hular mulki ta reshen itacen ƙaya suka sa shi a kan Yesu, saˈan nan suka sa masa wata riga mai kalar jar garura irin ta sarakuna.

3 Suka yi ta zuwa wurinsa, suna ta marinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!”

4 Sai Bilatus ya sāke fitowa, ya ce wa Yahudawa, “Ga shi fa zan fito muku da Yesu, don ina so ku sani cewa ban same shi da wani laifi ba.”

5 Saˈan nan Yesu ya fito da hular mulki ta ƙaya a kansa da kuma riga mai kalar jar garura. Sai Bilatus ya ce musu, “To, ga mutumin.”

6 Da manyan firistoci da masu gadin Haikali suka ga Yesu, sai suka yi ihu suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Amma Bilatus ya ce musu, “Ku je ku gicciye shi da kanku, domin ni ban same shi da wani laifi ba.”

7 Yahudawan suka amsa masa suka ce, “Ai, muna da Koyarwa, kuma bisa ga Koyarwar ya kamata a kashe shi, gama ya mai da kansa Ɗan Allah.”

8 Da Bilatus ya ji wannan magana sai ya ƙara jin tsoro.

9 Sai ya sāke shiga cikin fādar, ya tambayi Yesu cewa, “Daga ina ne ka fito?” Amma Yesu bai ba shi wata amsa ba.

10 Saboda haka Bilatus ya ce masa, “Ka ƙi ka yi magana da ni ko? Ba ka sani cewa ina da iko in sake ka, ko in gicciye ka ba?”

11 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, ikon da kake da shi a kaina iko wanda Allah ya ba ka ne kawai. Mutumin da ya sa ni a hannunka ya fi ka zunubi.”

12 A kan wannan magana Bilatus ya nema yă saki Yesu, amma Yahudawa suka ɗaga muryarsu suka yi ihu suna cewa, “In dai ka saki wannan, to, kai ba abokin Kaisar ba ne. Ai, duk wanda ya mai da kansa sarki, yana yi wa Kaisar tawaye ke nan.”

13 Da Bilatus ya ji wannan abin da suka faɗa, ya fito da Yesu. Sai shi Bilatus ya zauna a kujerar shariˈa a wani wurin da aka kira Daɓen Duwatsu. Da yaren Aramaya kuwa ana ce da shi Gabbata.

14 Ranar nan kuwa Ranar Shirin Bikin Ƙetarewa ce, wajen tsakar rana. Sai shi Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku!”

15 Amma Yahudawa suka yi ihu suna cewa, “A kashe shi! A kashe shi! A gicciye shi!” Sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “Kuna so in gicciye sarkinku ne?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Ai, mu ba mu da wani sarki sai Kaisar.”

16 Saˈan nan Bilatus ya ɗauki Yesu ya ba Yahudawa domin su gicciye shi.

17 Sai sojoji suka tafi da Yesu. Yesu ya kuwa fita daga cikin garin yana ɗauke da gicciyensa da kansa zuwa wani wurin da ake ce da shi Wurin Ƙoƙon Kai. Da yaren Aramaya kuwa ana ce da wannan wuri Golgota.

18 A wurin ne fa aka gicciye Yesu, tare da waɗansu mutane biyu, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa.

19 Bilatus kuma ya rubuta wata sanarwa, wadda aka manne a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne, “YESU BANAZARET, SARKIN YAHUDAWA.”

20 Yahudawa da yawa sun karanta wannan sanarwa domin wurin da aka gicciye Yesu kusa da birni ne. Wannan rubutu kuwa an yi shi da yaren Aramaya, da Romanci, da kuma Helenanci.

21 Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce wa Bilatus, “Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa’, amma ka rubuta, ‘Wannan mutum ya ce wai shi ne Sarkin Yahudawa’.”

22 Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na riga na rubuta, na rubuta ke nan.”

23 Bayan da sojojin suka gicciye Yesu, suka ɗibi tufafinsa, suka raba kashi huɗu, kowanne soja ya ɗauki kashi ɗaya. Sun kuma ɗauki doguwar rigarsa wadda ba a ɗinka ta ba, amma an saƙa ta ne tun daga sama har zuwa ƙasa.

24 Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage wannan riga, amma mu yi ƙuriˈa a kanta, mu ga wanda zai ci.” Wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, “Suka rarraba rigunana a tsakaninsu, suka jefa ƙuriˈa a kan rigata.” Abin da sojojin suka yi ke nan.

25 To, waɗanda suka tsaya kusa da gicciyen Yesu kuwa su ne mamarsa tare da ˈyarˈuwarta, da Maryamu matar Kilobas, da kuma Maryamu daga Magadala.

26 Da Yesu ya ga mamarsa da almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mamarsa, “Mace, ga ɗanki!”

27 Saˈan nan ya ce wa almajirin, “Wannan ta zama mamarka.” Tun daga lokacin nan fa almajirin ya kai mamar Yesu gidansa ta zauna tare da shi.

28 Yesu ya san cewa a wannan lokaci ya gama dukan kome, kuma domin a cika abin da yake a cikin Rubutacciyar Maganar Allah sai ya ce, “Ina jin ƙishin ruwa.”

29 To, akwai wani gora cike da ruwan inabi mai tsami a ajiye a wurin. Sai suka jiƙa soso da ruwan inabi mai tsamin, suka soka soson a sandan izob suka ɗaga suka kai bakin Yesu.

30 Da Yesu ya karɓi ruwan tsamin nan sai ya ce, “An gama!” Saˈan nan ya sunkuyar da kansa ya saki ransa.

31 Saˈan nan shugabannin Yahudawa suka roƙi Bilatus yă ba da izni a kakkarya ƙafafun mutanen da aka gicciye, a kuma sauko da jikunansu daga gicciye. Sun yi wannan roƙo ne domin Ranar Shiri ce, kuma ba sa so jikunan su kasance a kan gicciye a Ranar Hutu ta Mako. Ranar Hutun nan mai zuwa kuwa Hutu ne na musamman.

32 Sai sojojin suka zo wurin mutanen da aka gicciye tare da Yesu suka kakkarya ƙafafun mutum na farko, saˈan nan suka je suka kakkarya ƙafafun mutum na biyun.

33 Amma da suka zo wurin Yesu, ba su kakkarya ƙafafunsa ba domin sun ga ya riga ya mutu.

34 Sai dai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu da māshi a gefe, wajen haƙarƙarinsa, sai nan da nan jini da ruwa suka fito.

35 Shi wanda ya ga abin da ya faru ne ya faɗa wannan, kuma duk abin da ya faɗa gaskiya ne. Kuma shi ma da kansa ya san gaskiya yake faɗi, kuma yana faɗinsa ne domin ku ma ku ba da gaskiya.

36 Wannan ya faru ne domin abin da yake a cikin Rubutacciyar Maganar Allah yă cika, wato, “Ba ko ƙashinsa ɗaya da za a karya.”

37 Wata Rubutacciyar Maganar Allah kuma ta ce, “Za su dubi wanda suka soka.”

38 Bayan haka Yusuf mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin tsoron Yahudawa, ya roƙi Bilatus izni domin yă ɗauki jikin Yesu. Bilatus kuwa ya yarda masa, ya kuwa je ya ɗauki jikin Yesu.

39 Nikodimus mutumin da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare, ya tafi tare da Yusuf, yana kuma riƙe da kayan ƙanshi, wato mur da alos a gauraye, wajen kilo talatin.

40 Sai mutanen nan biyu suka ɗauki jikin Yesu suka nannaɗe da yadin lilin tare da kayan ƙanshin nan bisa ga alˈadar Yahudawa ta binnewa.

41 A wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wata gona, a cikin gonar kuma akwai wani sabon kabari wanda ba a taɓa sa kowa a ciki ba.

42 Da yake ranar shiri ce ta Yahudawa, kuma kabarin yana nan kusa sai mutanen nan suka sa jikin Yesu a nan wurin.

Open Bible reader