Skip to content

Hausa Bible

Ibraniyawa 9

1 To, yarjejeniya ta farko tana da ƙaˈidodinta na yin sujada, da kuma wurin da aka keɓe da tsarki a duniyar nan.

2 An kafa Tenti wanda yake da sashe na farko, inda aka sa sanda mai riƙe fitilu, da tebur, da Burodin da Aka Keɓe. Wannan sashe kuwa shi ne ake ce da shi Wuri Mai Tsarki.

3 Bayan babban labule na biyun kuma akwai sashen da ake ce da shi Wuri Mafi Tsarki.

4 A cikin wannan sashe kuwa akwai bagaden da akan ƙona turare mai ƙanshi a kai, da kuma Akwatin Yarjejeniya. Waɗannan abu biyu kuwa an shafe su da zinariya. A cikin Akwatin nan na Yarjejeniya kuwa akwai kwanon zinariya da manna a ciki, da sandan Haruna wanda ya fitar da ganye, da allunan dutse biyu na yarjejeniya.

5 A bisan Akwatin nan kuwa akwai halittu masu fikafikai na nuna kasancewar ɗaukakar Allah, waɗanda kuma suke inuwantar da inda ake ce da shi wurin ɗaukar alhakin zunubi. Amma a yanzu haka ba za mu iya yin magana dalla-dalla game da wannan batu ba.

6 Bayan da aka shirya kome haka, sai firistoci kullum su dinga shiga sashe na farko na Tentin, suna yin hidimarsu.

7 Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga sashe na biyun, yana kuma shiga wannan wurin sau ɗaya tak a shekara. Ba ya shigowa sai tare da jinin da zai miƙa saboda nasa zunubai, da kuma saboda zunuban da jamaˈa suka aikata ba tare da saninsu ba.

8 Ta haka Ruhu Mai Tsarki yana nuna cewa hanyar shiga ainihin Wuri Mafi Tsarki bai buɗu ba tukuna muddin wancan Tenti na farko yana nan tsaye.

9 Wannan kwatanci ne ga wannan zamani. Yana nuna cewa baye-baye da hadayun da akan miƙa ba su iya sa tunanin zuciyar mai sujada yă zama cikakke ba.

10 Waɗannan sun shafi maganar ci da sha da wanke-wanke iri-iri. Waɗannan ƙaˈidodi game da jiki ne kawai, waɗanda aka shimfiɗa kafin lokacin da aka kafa sabuwar ƙaˈida.

11 Ga shi, Almasihu ya riga ya zo a matsayin Babban Firist na alˈamura masu kyau waɗanda suke akwai yanzu. Ya kuma shiga cikin tenti mafi girma kuma mafi kyau, wadda ba mutum ne ya gina ba, wato ba irin ta wannan halitta ba.

12 Ya shiga wannan Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak. Bai shiga ta wurin jinin awaki ko na ˈyaˈyan shanu ba, amma ta wurin nasa jini ne, wanda ya samo mana fansa ta har abada.

13 Bisa ga Koyarwar Musa, akan yayyafa wa masu ƙazanta jinin awaki, da na bijimai, da tokar ˈyar saniya. Wannan yakan iya mai da masu ƙazanta marasa ƙazanta a jiki.

14 In wannan gaskiya ne, to, me za a ce da jinin Almasihu? Shi wanda ba shi da wani tabo, ya miƙa kansa ga Allah ta wurin Ruhun nan na har abada, ai, lallai ne jininsa zai iya tsabtace tunanin zuciyarmu, mu bar alˈadu marasa amfani domin mu bauta wa Allah Mai Rai.

15 Saboda haka Almasihu shi ne mai tsayawa tsakanin Allah da mutane a cikin sabuwar yarjejeniyar nan, domin waɗanda aka kira su su karɓi gādo na har abada wanda Allah ya yi alkawari. Wannan ya yiwu ne gama an riga an yi mutuwa wadda take ˈyantar da mutane daga zunuban da suka yi a zamanin yarjejeniya ta farko.

16 Idan wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole ne a tabbatar da mutuwar wanda ya yi alkawarin tukuna.

17 Gama alkawarin gādo ba shi da iko sai an yi mutuwa, wato ba ya ba da izni yayin da mai yinsa yana da rai.

18 Shi ya sa yarjejeniyar nan ta farko ba a tabbatar da ita ba sai ta wurin jini.

19 Bayan da Musa ya sanar wa dukan jamaˈa kowane umarnin da yake cikin Koyarwar, sai ya ɗauki jinin ˈyaˈyan shanu da na awaki, ya haɗa da ruwa. Saˈan nan ya ɗauki soson izob tare da jan gashin tumaki ya yayyafa jinin a kan Littafin Koyarwa da kuma a kan dukan jamaˈa.

20 Sai ya ce, “Wannan shi ne jini na tabbatar da yarjejeniya wadda Allah ya umarce ku ku kiyaye.”

21 Haka kuma ya yayyafa jinin a kan Tentin nan, da kuma a kan dukan kayayyakin da akan yi amfani da su domin hidimar sujada.

22 Lallai, bisa ga Koyarwar Musa, kusan kowane abu ne akan tsabtace da jini. Idan ba tare da jinin da aka zubar ba, ba yadda za a gafarta zunubai.

23 Ya zama dole waɗannan alˈadu su kasance haka domin a tsabtacewa waɗannan abubuwa na duniya. Gama su kwatancin abubuwan da suke a sama ne. Ainihin abubuwa na sama kuwa suna bukatar hadayar da ta fi ta farkon kyau.

24 Gama Almasihu bai shiga Wuri Mafi Tsarki wanda mutum ne ya gina ba, wanda yake kamanni ne kawai na ainihin wurin. Aˈa, sama ne da kansa ya shiga, domin yă bayyana a gaban Allah a yanzu saboda mu.

25 Ba wai ya shiga cikin sama domin yă dinga miƙa kansa kullum ba, kamar yadda babban firist yakan shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba.

26 In da haka ne, ai, da dole ne Yesu yă sha wahala a kai a kai ke nan, tun daga lokacin da aka halicci duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubai ta wurin miƙa kansa.

27 Kamar yadda aka shirya wa ɗan Adam yă mutu sau ɗaya tak, bayan haka sai shariˈar Allah,

28 haka kuma an miƙa Almasihu sau ɗaya domin yă ɗauki zunuban mutane da yawa. Shi kuwa zai sāke bayyana sau na biyu, ba domin yă ɗauki zunubai ba, amma domin yă kawo ceto ga duk waɗanda suke marmarin dawowarsa.

Open Bible reader