Hausa Bible
Ibraniyawa 7
1 Wannan Melkizedek shi sarkin Salem ne, da kuma firist na Allah Mafi Ɗaukaka. Ya sadu da Ibrahim a lokacin da Ibrahim yake dawowa bayan da ya ci nasara a yaƙin da ya yi da waɗansu sarakuna. Da suka sadu, Melkizedek ya sa wa Ibrahim albarka,
2 Ibrahim kuwa ya ba shi zakka ta kome. Da farko dai, maˈanar sunan Melkizedek ita ce “Sarkin Adalci.” Saˈan nan kuma shi sarkin Salem ne, wato “Sarkin Salama.”
3 Melkizedek kuwa ba shi da baba ko mama ko asali. Ba shi da farkon kwanaki ko ƙarshen rai. Amma kamar Ɗan Allah, shi firist ne har abada.
4 Ku dubi irin girman mutumin nan. Har Ibrahim kakan kakanninmu ya ba shi zakka ta kayan da shi Ibrahim ya ƙwace a yaƙi.
5 Bisa ga Koyarwar Musa, dukan zuriyar Lawi waɗanda su firist ne sukan karɓi zakka daga hannun jamaˈa, wato daga hannun ˈyanˈuwansu, ko da yake su ma zuriyar Ibrahim ne.
6 Amma Melkizedek, wanda asalinsa ba ɗaya ba ne da zuriyar Lawi, ya karɓi zakka a hannun Ibrahim, ya kuma albarkaci Ibrahim wanda shi ne aka yi masa alkawaran.
7 Ba shakka wanda yake sa albarka ya fi wanda yake karɓar albarka girma.
8 Ga shi ma firistoci na zuriyar Lawi, ko da yake su masu mutuwa ne, sukan karɓi zakka daga hannun mutane. Amma game da Melkizedek, wanda ya karɓi zakka daga hannun Ibrahim, an ba da shaida cewa shi rayayye ne.
9 Har ma ana iya cewa Lawi da kansa, wanda zuriyarsa ce mai karɓar zakka, ya ba da tasa zakka ta hannun Ibrahim.
10 Ana iya faɗa haka domin a lokacin da Ibrahim ya sadu da Melkizedek ba an riga an haifi Lawi ba tukuna, amma yana cikin jikin kakansa.
11 Ga shi, tsarin firistoci irin na zuriyar Lawi ya zo tare da Koyarwar Musa wadda aka ba Israˈilawa. Da a ce aikin firistoci na zuriyar Lawi yana iya kawo zaman cikakke, ai, da ba dalilin da wani firist dabam yă sāke zuwa, wanda yake bisa ga tsarin Melkizedek, ba bisa ga tsarin Haruna ba.
12 Gama idan an canja tsarin firistoci, dole ne a canja Koyarwar ma.
13 Shi wanda ake faɗa waɗannan abubuwan a kansa, wato Ubangijinmu, ya fito daga wata zuriya ne dabam. Ba ko ɗaya daga zuriyarsa da ya taɓa yin hidima a matsayin firist.
14 Lallai Ubangijinmu ya fito daga zuriyar Yahuda ne, wadda Musa bai yi wani zance a kanta ba lokacin da yake magana game da firistoci.
15 Wannan magana ta ƙara fitowa a fili sosai, saˈad da wani firist dabam ya bayyana, wanda yake kamar Melkizedek.
16 Wannan kuwa ya zama firist ba bisa ga wata doka ko ƙaˈida game da zuriyar ˈyan Adam ba, amma bisa ga ikon rai marar ƙārewa.
17 Gama an yi shaida game da shi cewa, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”
18 An kawar da Koyarwar ta dā a gefe ke nan saboda rashin ikonta da rashin amfaninta.
19 Koyarwar Musa ba ta isa ta sa wani abu yă zama cikakke ba. Amma yanzu aka shirya wata sa zuciya mafi kyau wanda ta wurinsa muke matsowa kusa da Allah.
20 Allah ya tabbatar da wannan shiri tare da rantsuwa. Sauran firistocin sukan shiga aikinsu ba tare da rantsuwa ba.
21 Amma wannan ya zama firist ne tare da rantsuwar da Allah ya yi cewa, “Ubangiji ya riga ya rantse, ba zai kuma canja nufinsa ba, ‘Kai firist ne na har abada.’ ”
22 Bisa ga wannan rantsuwa ne kuma Yesu ya zama mai tabbatar da yarjejeniya mafi kyau.
23 Firistoci irin na dā sun yi yawa domin mutuwa takan hana su ci gaba da aikinsu.
24 Amma Yesu yana riƙe da matsayin firist na har abada, domin shi da kansa yana nan har abada.
25 Saboda haka yana da iko, yau da kullum, yă ceci duk waɗanda suke matsowa kusa da Allah ta wurinsa, tun da yake kullum a raye yake, domin yă yi roƙo ga Allah a madadinsu.
26 Irin wannan babban firist ne muke bukata. Shi kuwa mai tsarki ne, marar laifi, marar tabo, an ware shi daga masu zunubi, an kuma ɗaukaka shi gaba da sammai.
27 Shi ba kamar waɗancan manyan firistoci ba ne. Ba ya bukata yă dinga miƙa hadaya kullum, wato yă fara miƙa saboda nasa zunubai kafin yă miƙa saboda zunuban jamaˈa. Shi kam ya miƙa tasa hadaya sau ɗaya tak, a lokacin da ya miƙa kansa.
28 Gama bisa ga Koyarwar Musa akan zaɓi babban firist cikin kāsawarsa daga cikin mutane. Amma alkawarin nan da Allah ya yi tare da rantsuwa, ya iso ne bayan da an ba da Koyarwar Musa. Bisa ga alkawarin nan ne aka naɗa Ɗan wanda an mai da shi cikakke har abada.