Hausa Bible
Ibraniyawa 11
1 Bangaskiya ita ce kasancewa da tabbaci a kan abin da muka sa zuciya a kai, zaman tabbaci kuma game da abin da ba a iya gani.
2 Ta wurin bangaskiya ne mutanen dā suka sami yabo daga wurin Allah.
3 Ta wurin bangaskiya mun gane cewa bisa ga kalmar Allah ne aka halicci dukan duniya, har abin da ake gani ya fito ne daga abin da ba a iya gani.
4 Ta wurin bangaskiya ne Habila ya miƙa wa Allah hadayar da ta fi ta Kayinu kyau. Ta yin haka ya sami yabo daga wurin Allah cewa shi mai adalci ne, saˈad da Allah ya karɓi bayarwarsa. Habila kuwa ya mutu, amma saboda bangaskiyarsa yana magana har yanzu.
5 Ta wurin bangaskiya ne aka ɗauki Enok, domin kada yă ga mutuwa. Ba a kuwa same shi ba, saboda Allah ya riga ya ɗauke shi. Kafin a ɗauke shi an ba da shaida cewa ya faranta wa Allah rai.
6 In ba tare da bangaskiya ba, ba ya yiwuwa a faranta wa Allah rai, gama duk mai matsowa kusa da Allah dole ne yă ba da gaskiya cewa akwai Allah kuma yana ba da lada ga duk waɗanda suke nemansa.
7 Ta wurin bangaskiya ne Nuhu, bayan da Allah ya yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, ya yi biyayya, ya shirya jirgin ruwa domin a ceci iyalinsa. Ta haka, ya sa an hukunta duniya, shi kuwa ya zama mai gādon adalci wanda ake samuwa ta bangaskiya.
8 Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim ya yi biyayya ya kama hanya zuwa wata ƙasa wadda aka yi masa alkawari cewa zai karɓi gādonta. Shi kuwa ya kama hanya ko da yake bai san inda za shi ba.
9 Ta wurin bangaskiya ya zauna kamar baƙo a ƙasar nan da Allah ya yi masa alkawari. Yana zama a cikin tentuna, shi da Ishaku da Yakub, waɗanda suka gāji alkawarin nan tare da shi.
10 Ya yi irin wannan zaman ne domin ya sa zuciya a kan birnin nan wanda yake da tushe, wanda Allah ne mai shirya, shi ne kuma mai gina shi.
11 Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim ya haifi ɗa, ko da yake ya tsufa sosai a lokacin, Saratu kuwa ba ta haifuwa. Ya ba da gaskiya cewa Allah mai aminci ne cikin alkawarinsa.
12 Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda ya tsufa har ya kai ga bakin mutuwa, aka haifi zuriya masu yawa kamar taurarin sama, kamar yashi a bakin teku waɗanda ba a iya ƙirgawa.
13 Duk waɗannan sun mutu a cikin bangaskiyarsu. Ba su karɓi abubuwan da Allah ya yi alkawari ba, amma suka hangi abubuwan nan daga nesa, suka yi murna da ganinsu, suka kuma ba da shaida a fili cewa su baƙi ne, ba ˈyan ƙasa ba, a duniya.
14 Waɗanda suke ba da irin wannan shaida suna nuna a fili ke nan cewa suna neman ƙasa ta kansu.
15 Da a ce suna ta tunani ne a kan ƙasar da suka bari a baya, ai, da sun sami zarafin komawa.
16 Amma sun sa zuciya a kan ƙasa mafi kyau, wato ta sama. Shi ya sa Allah bai ji kunya a ce da shi Allahnsu ba. Hakika, ya shirya birni saboda su.
17 Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim, a lokacin da aka gwada shi, ya miƙa Ishaku hadaya. Wato, shi da ya karɓi alkawarin nan yana a shirye yă miƙa makaɗaicin ɗansa,
18 ko da yake Allah ya faɗa masa cewa, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta sunanka.”
19 Ibrahim kuwa ya yi tunani cewa lallai ne Allah yana iya tā da matattu. Har ma bisa ga misali, ana iya cewa ya karɓi Ishaku daga matattu ne.
20 Ta wurin bangaskiya ne Ishaku ya albarkaci Yakub da Isuwa game da abubuwa masu zuwa.
21 Ta wurin bangaskiya ne Yakub, a lokacin da zai mutu, ya sa wa kowane yaron Yusuf albarka, ya kuma yi sujada ga Allah yayin da yake jingine a kan sandansa.
22 Ta wurin bangaskiya ne Yusuf, a lokacin da ya kusa mutuwa, ya yi magana game da fitowar Israˈilawa daga ƙasar Masar, ya kuma ba da umarni game da ƙasusuwansa.
23 Ta wurin bangaskiya ne iyayen Musa suka ɓoye shi har wata uku bayan haifuwarsa. Sun yi haka domin sun ga cewa yaron kyakkyawa ne, ba su kuma ji tsoro game da umarnin sarki ba.
24 Ta wurin bangaskiya ne Musa, saˈad da ya yi girma, ya ƙi a ce da shi ɗan ˈyar Firˈauna.
25 Ya zaɓi yă sha wahala tare da mutanen Allah a maimakon yă ji daɗin romon zunubi na ɗan lokaci.
26 Saboda ya kafa ido ga ladan da yake a gaba, ya ɗauka cewa wulaƙancin da aka yi masa saboda Almasihu abu mai kyau ne fiye da dukiyar Masar.
27 Ta wurin bangaskiya ne ya bar ƙasar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba. Ya jimre saboda yana ganin wanda ido ba ya iya gani.
28 Ta wurin bangaskiya ne Musa ya kiyaye Bikin Ƙetarewa, ya kuma yayyafa jini domin kada mai halakar da ˈyaˈyan farin nan yă taɓa ˈyaˈyan fari na Israˈila.
29 Ta wurin bangaskiya ne Israˈilawa suka bi ta cikin Tekun Ciyawar Iwa, a kan busasshiyar ƙasa. Amma da Masarawa suka yi ƙoƙari su bi su, sai ruwa ya kwashe su.
30 Ta wurin bangaskiya ne katangar birnin Yeriko ta fāɗi bayan da aka yi ta kewaye ta har kwana bakwai.
31 Ta wurin bangaskiya ne Rahab karuwar nan, ba ta halaka tare da marasa biyayya ba, domin ta karɓi ˈyan leƙen asirin ƙasar nan cikin salama.
32 Me kuma zan ƙara cewa? Ba ni da zarafi in yi zance a kan Gideyon, da Barak, da Samson, da Yefta, da Dawuda, da Samaˈila, da kuma annabawa.
33 Ta wurin bangaskiya ne waɗannan suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka karɓi abubuwan da aka yi alkawari, suka rurrufe bakunan zakoki,
34 suka tsai da ikon wuta, suka tsere kaifin takuba. Suka mai da rashin ƙarfi yă zama da ƙarfi a gare su. Suka kori sojojin ƙasashe dabam-dabam.
35 Mata suka karɓi matattunsu waɗanda aka tā da su da rai. Aka gwada wa waɗansu azaba, su kuwa suka ƙi a sake su, domin suna nema su tashi daga matattu cikin rayuwa mafi kyau.
36 Waɗansu suka sha baˈa da bulala, waɗansu kuwa suka sha ɗauri da sarƙa, waɗansu aka jefa su a kurkuku.
37 Aka jejjefe su da duwatsu, aka yanka su kashi biyu da zarto, aka kuma kakkashe su da takobi. Suka yi ta yawo sanye da fatunan raguna da na awaki. Suka yi zama cikin rashi, da tsanani, da wulaƙanci.
38 Har ma duniya ba ta isa su zauna a cikinta ba. Sun yi ta yawo a hamada da kuma kan tuddai. Suna kwana a cikin kogwannin duwatsu, da kuma cikin ramukan a ƙasa.
39 Duk waɗannan Allah ya ba da shaidar yabo game da bangaskiyarsu, amma duk da haka ba su karɓi abin da aka yi alkawari ba.
40 Allah dai ya shirya abu mafi kyau dominmu. Nufinsa kuwa shi ne kada a kai su ga zaman cikakke idan ba tare da mu ba.