Hausa Bible
Galatiyawa 3
1 Ya ku Galatiyawa, kuna hauka ne? Ko wani ya yi muku magani ne? Ga shi, a fili na bayyana muku Yesu Almasihu wanda ya mutu a kan gicciye.
2 Yanzu ina so in yi muku tambaya ɗaya tak. Ruhun Allah ya zo muku saboda kun bi ayyukan Koyarwar Musa ne, ko kuwa saboda kun gaskata da maganar da kuka ji ne?
3 Yanzu wane irin wawanci kuke da shi haka? Ga shi, kun fara da Ruhun Allah, amma yanzu kuna so ku ƙarasa da ƙoƙarin kanku na halin mutuntaka!
4 Ashe, wahaloli dabam-dabam da kuka sha sun zama banza ke nan? Haka zai yiwu kuwa?
5 Wato, Allah wanda ya ba ku Ruhunsa, yana kuma yin abubuwa masu ban mamaki a cikinku, kuna tsammani yana yin haka ne saboda kuna bin ayyukan Koyarwar Musa, ko kuwa saboda kun ji maganar Almasihu kun kuma gaskata?
6 Ku dubi rayuwar Ibrahim mana. An rubuta cikin Maganar Allah cewa, “Saboda Ibrahim ya gaskata Allah, sai Allah ya lissafta wannan adalci ne a gare shi.”
7 To, sai a gane cewa, masu bangaskiya su ne zuriyar Ibrahim.
8 Rubutacciyar Maganar Allah ta faɗa tun dā cewa waɗanda ba Yahudawa ba za su iya samun matsayin adalci a gaban Allah ta wurin bangaskiya. Saboda tun dā ma an sanar wa Ibrahim labari mai daɗi cewa, “Ta wurinka ne dukan alˈummai za su sami albarka.”
9 Saboda haka, masu bangaskiya za a albarkace su tare da Ibrahim mai bangaskiya.
10 Gama duk waɗanda suke tsammani Allah zai karɓe su don suna bin Koyarwar Musa, laˈanannu ke nan. Gama Rubutacciyar Maganar Allah ta ce, “Duk wanda bai aikata dukan abin da yake a rubuce a Littafin Koyarwar Musa ba, laˈananne ne shi.”
11 To, a fili yake, babu wanda zai iya zama mai adalci a gaban Allah ta wurin bin Koyarwar Musa, domin an rubuta cewa, “Mai adalci, ta wurin bangaskiya ne, zai rayu.”
12 Koyarwar Musa ba daga cikin bangaskiya take ba. Kamar yadda aka rubuta, “Wanda ya aikata dukan abin da aka faɗa cikin Koyarwar Musa, a gare ta ne zai rayu.”
13 Laˈanar nan ta Koyarwar Musa mun kuɓuta daga gare ta, saboda Almasihu ya fanshe mu daga laˈanar nan, da yake an mai da shi abin laˈana saboda mu ne. Gama an rubuta, “Duk wanda aka rataye shi a kan gungumen itace, laˈananne ne ga Allah.”
14 Almasihu ya fanshe mu ne domin albarkar nan da aka yi wa Ibrahim ta zo wa waɗanda ba Yahudawa ba kuma ta wurin Almasihu Yesu. Ta haka, mu ma, ta wurin bangaskiya, mun iya samun Ruhun nan da Allah ya yi alkawari.
15 ˈYanˈuwa, bari in ba ku misalin abin da kuka saba da shi. Idan mutum biyu sun yi yarjejeniya sun kuma sa hannu domin a tabbatar da shi, to, ba mai soke shi, ba kuma mai ƙara wani abu a kai.
16 To, Allah ya yi yarjejeniya da Ibrahim da kuma zuriyarsa. Ba a rubuta cewa “da zuriyoyi” ba, wanda zai nuna kamar suna da yawa. Aˈa, an ce “zuriyarka,” mutum ɗaya ke nan, wato Almasihu.
17 Abin da nake nufi shi ne Allah ya yi yarjejeniya da Ibrahim ya kuma tabbatar da ita. Koyarwar nan ta Musa wadda aka kawo bayan shekara ɗari huɗu da talatin ba za ta iya mai da yarjejeniyar nan da Allah ya yi tun dā wofi ba.
18 Gama da a ce gādon albarkar nan ta Allah ana samuwa ta wurin bin Koyarwar ne, ashe, da ba za a samu ta wurin alkawari ba. Ibrahim kuwa, ta wurin alkawari ne Allah ya ba shi albarkar.
19 To, in haka ne, don me aka kawo Koyarwar Musa? An yi ƙari da Koyarwar ne domin a nuna mana zunubanmu a fili. An kawo ta da nufi cewa za a yi aiki da ita har ranar da zuriyar nan ta Ibrahim za ta zo, wadda dominsa ne aka yi alkawarin. Ga shi kuwa wannan Koyarwa, malaˈiku ne suka ba da ita, ta hannun mutum mai tsayawa tsakanin Allah da mutane.
20 Kuma ba a bukatar mai tsayawa tsakani idan alˈamari ya shafi mutum ɗaya ne, Allah kuwa ɗaya ne.
21 Ashe, wannan yana nufin Koyarwar tana gāba da alkawarin Allah ke nan? Aˈa, ko kusa! Gama da a ce an kawo wata koyarwa wadda za ta sa mu rayu, wannan zai nuna za a sami adalcin Allah ta hanyar bin koyarwar ke nan.
22 Maimakon haka an rubuta cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, dukan duniya tana ƙarƙashin ikon zunubi. Don me? Domin alkawarin nan da aka yi bisa ga bangaskiya ga Yesu Almasihu, za a ba da shi ga waɗanda suka ba da gaskiya.
23 Kafin lokacin bangaskiya yă zo, Koyarwar nan ta kulle mu kamar ˈyan kurkuku, sai lokacin da bangaskiya ta bayyana.
24 Wato, aka danƙa mu a hannun Koyarwar Musa domin ta kai mu ga Almasihu, domin ta wurin bangaskiya ne mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah.
25 Yanzu kuwa da yake bangaskiya ta zo, ba mu kasance a ƙarƙashin renon Koyarwar Musa kuma ba.
26 Gama ta wurin bangaskiya ga Almasihu Yesu, dukanku kun zama ˈyaˈyan Allah.
27 An kuma yi muku wankan baftisma wadda ta nuna cewa ku na Almasihu ne, saboda haka kun kuma ɗauki halin Almasihu, ya zama halinku.
28 Saboda haka, ba bambanci tsakanin Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba. Ba kuma bambanci tsakanin ɗa da bawa, ko tsakanin mace da namiji. Ai, dukanku ɗaya ne cikin Almasihu Yesu.
29 In kuwa ku na Almasihu ne, kun zama zuriyar Ibrahim ke nan, kuma masu cin gādon nan bisa ga alkawarinsa.