Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 17
1 To, da Bulus da Sila suka bi ta Amfibolis da Afolloniya, suka kai Tasalonika, inda akwai majamiˈar Yahudawa.
2 Sai Bulus ya shiga wurinsu kamar yadda ya saba, Ranar Hutu ta Mako guda uku a jere yana muhawara da su daga cikin Rubutacciyar Maganar Allah.
3 Yana yi musu bayani, yana kuma tabbatar musu cewa dole ne Almasihu yă sha wahala, yă kuma tashi daga matattu. Bulus ya kuma ce, “Yesun nan da nake sanar muku, shi ne Almasihu.”
4 Sai waɗansu mutanen Yahudawa da kuma Helenawa masu bautar Allah haɗe da manyan mata masu yawa sosai, duk suka yarda da maganar Bulus da Sila, suka kuma haɗa kai da su.
5 Amma Yahudawa suka yi kishi, sai suka tara waɗansu ˈyan iska a kasuwa. Da dukansu suka taru sai suka tā da hankalin mutanen garin. Suka ruga cikin gidan Yason suna neman Bulus da Sila domin su kawo su gaban jamaˈa.
6 Da ba su same su ba, sai suka jawo Yason da waɗansu masu bi, suka kai su har gaban masu shariˈa, suna ihu suna cewa, “Mutanen nan da suke tā da hankali a koˈina a duniya, ga su sun zo har nan ma.
7 Har ma Yason ya ba su masauki. Dukansu kuwa suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wai sunansa Yesu.”
8 Da mutanen garin da shugabannin gari suka ji wannan, sai hankalinsu ya tashi.
9 Ba su saki Yason da sauransu ba, sai da suka karɓi kuɗin beli a hannunsu.
10 Da dare ya yi, masu bi suka sallami Bulus da Sila su tafi Biriya. Da suka kai can, suka shiga majamiˈar Yahudawa.
11 To, waɗannan Yahudawa sun fi na Tasalonika hankali, domin sun karɓi maganar hannu biyu-biyu. Suna ta binciken Rubutacciyar Maganar Allah kullum, su gani ko abin da Bulus ya faɗa gaskiya ne.
12 Saboda haka da yawa daga cikin Yahudawa suka ba da gaskiya, har da waɗansu matan Helenawa masu matsayi da kuma mazan Helenawa da yawa.
13 Amma da Yahudawan da suke a Tasalonika suka ji cewa Bulus yana yin shelar kalmar Allah a Biriya ma, suka je suka zuga jamaˈa a can suna tā da hankalinsu.
14 Nan da nan kuwa masu bi suka sa Bulus yă tafi bakin teku, amma Sila da Timoti suka tsaya tukuna a nan.
15 Waɗanda suka yi wa Bulus rakiya kuwa suka kai shi har Atina. Da za su dawo sai Bulus ya ba su saƙo zuwa wurin Sila da Timoti cewa su zo su same shi da sauri, sai suka tafi.
16 To, saˈad da Bulus yake jiran Sila da Timoti a Atina, ya yi baƙin ciki ƙwarai da ya ga garin ya cika da gumaka.
17 Domin haka yakan yi muhawara a cikin majamiˈa da Yahudawa, da waɗansu Helenawa masu yi wa Allah sujada. Kowace rana kuwa yakan yi muhawara da waɗanda yake samuwa a kasuwa.
18 Haka kuma waɗansu Abikuriyawa da Sitokiyawa masu ilimi suka yi muhawara da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne wannan mai surutu yake so ya ce?” Waɗansu suka ce, “Kamar mai yin waˈazin waɗansu alloli ne da ba na nan ba.” Sun faɗa haka gama Bulus yana yin waˈazi a kan Yesu da kuma tashinsa daga matattu.
19 Saboda haka suka kai shi Tudun Arasa, inda majalisarsu take taruwa, suka ce masa, “Ko za ka bayyana mana wannan sabuwar koyarwar da kake yi?
20 Don ba mu taɓa jin irin waɗannan maganganu ba. Muna so mu san abin da suke nufi.”
21 Duk Atinawa da baƙin da suke zama a Atina kuwa sun fi so su ji sabon abu su kuma yi magana a kai, fiye da kome.
22 Sai Bulus ya tashi tsaye a gaban majalisar, ya ce, “Ku mutanen Atina, na lura cewa ku masu son bin addini ne sosai ta kowane gefe.
23 Lokacin da nake zagawa cikin garin, na duba abubuwan da kuke yi wa sujada, na kuwa ga wani bagaden hadaya da rubutu a kansa mai cewa, ‘Domin Allahn da ba a sani ba.’ To, shi wannan da kuke yi wa sujada da ba ku san shi ba, shi ne nake sanar muku.
24 Allahn nan da ya halicci duniya da dukan abin da yake cikinta, shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da mutum ya gina.
25 Haka kuma ba ya neman taimako daga wurin mutum, ba ya bukatar wani abu, tun da yake shi ne yake ba dukan mutane rai, da numfashi da dukan abubuwan da suke bukata.
26 Shi ne kuma ya halicci dukan alˈumma daga mutum guda, domin su zauna a dukan fuskar duniya. Ya shirya iyakar lokacinsu, da kuma wuraren da kowace alˈumma za ta kasance.
27 Allah ya yi haka domin su neme shi, ko wataƙila za su laluba su same shi, ko da yake bai yi nesa da kowannenmu ba.
28 Ai, “ ‘Ta gare shi ne muke rayuwa, muke motsi, muka kuma kasance.’ “Yadda waɗansu mawaƙanku ma suka faɗa cewa, ‘Hakika, mu ma zuriyarsa ce.’
29 “To, da yake mu zuriyar Allah ne, ai, bai kamata mu yi tsammani Allah yana kama da wata siffar zinariya, ko ta azurfa, ko ta dutse ba, wadda mutum ya ƙera da dabararsa.
30 A dā kam, Allah ya kawar da fuska daga ayyukan jahilci. Amma yanzu ya umarci dukan mutane a koˈina su tuba,
31 gama ya shirya ranar da zai zo yă yi wa duniya shariˈa ta gaskiya ta wurin mutumin da ya zaɓa. Allah ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin tā da mutumin nan daga matattu.”
32 Da suka ji maganar tashi daga matattu, sai waɗansu suka yi masa baˈa, amma waɗansu suka ce, “Muna so mu sāke jin abin da za ka faɗa game da wannan magana.”
33 A nan ne Bulus ya rabu da su.
34 Amma waɗansunsu suka koma wajen Bulus, suka ba da gaskiya. A cikinsu akwai Diyonisiyus, ɗan majalisa, da wata mace mai suna Damaris, da waɗansu kuma tare da su.