Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 16

1 Sai Bulus ya je Darbe da Listira. Akwai wani almajiri a Listira mai suna Timoti, ɗan wata Bayahudiya mai bi. Babansa kuwa Bahelene ne.

2 Masu bin da suke a Listira da Ikoniya kuwa suna yabon Timoti.

3 Bulus ya so Timoti yă raka shi. Domin haka ya ɗauke shi ya yi masa kaciya saboda Yahudawan da suke waɗannan wuraren duk sun san babansa Bahelene ne.

4 Lokacin da Bulus da Sila suke tafiya suna bin gari-gari, suka dinga bayyana wa jamaˈa ƙaˈidodin da manzanni da dattawan jamaˈar masu bi suka yarda a kai a Urushalima, suka gaya wa masu bi su kiyaye su.

5 Ta haka jamaˈar masu bi suka ƙara ƙarfi cikin bangaskiya, suna ƙara yawa kowace rana.

6 Sai suka zazzaga ƙasashen Firijiya da Galatiya, don Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin maganar Ubangiji a Asiya.

7 Da suka zo kan iyakar ƙasar Misiya, suka yi ƙoƙari su je ƙasar Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba.

8 Suka kuwa bi ta gefen ƙasar Misiya, suka gangara zuwa Toruwas.

9 Da dare Bulus ya ga ruˈuya. A ruˈuyar kuwa ya ga wani mutumin ƙasar Makidoniya yana tsaye, yana roƙonsa yana cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.”

10 Da Bulus ya ga ruˈuyar nan kuwa, nan take muka yi ƙoƙari mu ƙetare zuwa Makidoniya, don mun tabbata cewa Allah ne ya kira mu mu yi musu waˈazin labari mai daɗi.

11 Sai muka tashi a cikin jirgin ruwa daga Toruwas muka miƙe har Samotiras. Washegari kuma sai Niyafolis.

12 Daga nan kuma sai muka wuce ta ƙasa zuwa birnin Filibi a ta yankin Makidoniya, wadda take ƙarƙashin mulkin Roma. Muka yi ˈyan kwanaki a nan.

13 Ranar Hutu ta Mako muka fita ƙofar gari, muka je bakin kogi inda muke tsammani akwai wurin yin adduˈa na Yahudawa, muka zauna muka yi magana wa matan da suka taru a wurin.

14 Akwai wata mace mai suna Lidiya, mai bautar Allah, tana sauraronmu. Ita ˈyar garin Tayatira ce, tana sayar da yadunan jar garura masu tsada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta, har ta sa hankali ta saurari abin da Bulus ya faɗa.

15 Da aka yi mata baftisma tare da mutanen gidanta, sai ta roƙe mu ta ce, “Idan kun yarda ni mai ba da gaskiya ga Ubangiji ce, to, sai ku zo gidana ku sauka.” Ta lallashe mu, sai muka yarda.

16 Wata rana za mu je wurin yin adduˈa sai muka gamu da wata yarinya mai aljani mai dūba. Masu yarinyar kuwa suna samun kuɗi sosai ta wurin dūban da take yi.

17 Sai ta dinga binmu, mu da Bulus, tana ihu tana cewa, “Mutanen nan bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto!”

18 Ta yi ta yin haka kwanaki da yawa. Sai Bulus ya ɓata rai sosai, ya juya ya ce wa aljanin, “Na umarce ka cikin sunan Yesu Almasihu, ka rabu da ita.” Nan take kuwa ya rabu da ita.

19 Da masu yarinyar suka ga hanyar da suke samun kuɗi ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su har cikin kasuwa gaban masu shariˈa.

20 Da suka kai su gaban alƙalai, suka ce, “Waɗannan Yahudawa ne fa, kuma suna rikitar da garinmu.

21 Suna koyar da alˈadun da bai kamata mu karɓa ko mu bi ba, gama mu Romawa ne.”

22 Sai jamaˈa suka taru a kansu gaba ɗaya, alƙalan kuma suka yayyage musu tufafinsu, suka tuttuɓe su, suka ba da umarni a dūke su.

23 Da aka dūke su sosai, aka sa su cikin kurkuku, aka umarci maigadin kurkukun yă yi gadinsu da kyau.

24 Shi kuwa da ya karɓi wannan umarni, sai ya sa su can ciki-cikin kurkuku, ya sa ƙafafunsu a cikin katakon riƙe ƙafafu ya kulle.

25 Wajen tsakar dare, Bulus da Sila suna adduˈa suna waƙoƙin yabon Allah, sauran ˈyan kurkukun kuwa suna sauraronsu.

26 Ba labari sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, har tushen ginin kurkukun ya girgiza. Nan da nan ƙofofin duka suka buɗe, sarƙoƙin dukan ˈyan kurkukun suka kunce.

27 Da maigadin ˈyan kurkukun ya tashi daga barci ya ga ƙofofin kurkukun a buɗe, sai ya zaro takobinsa, yana shiri yă kashe kansa, domin yana tsammani ˈyan kurkukun sun gudu.

28 Amma Bulus ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Kada ka yi wa kanka ciwo, ai, dukanmu muna nan!”

29 Sai maigadin ˈyan kurkuku ya ce a kawo fitilu. Sai ya yi wuf ya shiga ciki, ya fāɗi a gaban Bulus da Sila, yana rawar jiki don tsoro.

30 Saˈan nan ya fito da su waje ya ce, “Shugabanni, me zan yi in sami ceto?”

31 Su kuwa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, kai da iyalinka za ku sami ceto.”

32 Saˈan nan suka gaya masa kalmar Ubangiji, shi da mutanen da suke gidansa duka.

33 A cikin daren nan ya ɗauke su, ya wanke musu mikinsu. Nan da nan kuwa aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa.

34 Saˈan nan ya shigo da su cikin gidansa, ya kawo musu abinci. Shi da iyalinsa duka suka cika da farin ciki don dukansu sun ba da gaskiya ga Allah.

35 Da gari ya waye, alƙalan suka aiko ˈyan sanda da umarni cewa, “A saki mutanen nan.”

36 Sai maigadin ˈyan kurkukun ya kawo wa Bulus saƙon ya ce, “Alƙalai sun aiko a sake ku. Domin haka yanzu sai ku fito ku tafi lafiya.”

37 Amma Bulus ya ce musu, “Ai, a gaban mutane suka yi mana bulala, ba tare da an yi mana shariˈa ba, ko da yake mu Romawa ne. Suka kuma jefa mu cikin kurkuku, yanzu kuma za su fitar da mu a ɓoye? Ina! Sai dai su zo da kansu su fitar da mu.”

38 Sai ˈyan sandan suka je suka faɗa wa alƙalan wannan magana. Alƙalan kuwa suka ji tsoro da suka ji wai Bulus da Sila Romawa ne.

39 Saˈan nan suka zo suka roƙi gafara a wurin Bulus da Sila. Bayan haka sai suka fitar da su suka roƙe su su bar garin.

40 Bayan da Bulus da Sila suka fito daga kurkukun, sai suka tafi wurin Lidiya. Bayan da suka ga masu bi, suka kuma ƙarfafa musu zuciya, sai suka tafi.

Open Bible reader