Skip to content

Hausa Bible

Luka 5

1 Wata rana Yesu yana tsaye a gefen Tekun Janisarat. Mutane suka yi ta matsawa kusa da shi domin su ji kalmar Allah.

2 Yesu ya ga jirage biyu a ajiye a bakin tekun. Masu kamun kifin kuwa sun fita suna wanke ragarsu ta kamun kifi.

3 Sai Yesu ya shiga ɗaya daga cikin jiragen, wanda yake na Bitrus, ya kuma roƙe shi yă tura jirgin zuwa cikin ruwa kaɗan. Sai ya zauna a ciki yana koya wa mutane.

4 Da ya gama magana, sai ya ce wa Bitrus, “Ka ƙara tura jirgin zuwa inda akwai zurfi, ku saki ragar kamun kifinku, ku jawo kifi.”

5 Bitrus ya ce masa, “Ya maigirma, ai, tun da dare muna a nan muna fama ba mu kama kome ba, amma in ka ce haka, to, zan yi.”

6 Da suka sa ragar kamun kifin, sai suka kama kifi da yawa har ragar kamun kifin ta fara tsintsinkewa.

7 Ganin haka, sai suka kira abokansu na ɗayan jirgin su zo su taimake su. Suka zo suka ciccika jiragen biyu da kifi, har jiragen suka kusa nutsewa saboda nauyi.

8 Da Bitrus ya ga abin da ya faru, sai ya durƙusa a gaban Yesu ya ce, “Rabu da ni, ya Ubangiji! Gama ni mai zunubi ne!”

9 Gama shi da waɗanda suke tare da shi duka, mamaki ya kama su sosai saboda yawan kifin nan da suka kama,

10 haka ma Yakub da Yohanna, ˈyaˈyan Zabadi, abokan aikin Bitrus. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Kada ka ji tsoro, daga yanzu mutane ne za ka dinga kamowa, ba kifi ba.”

11 Sai suka jawo jiragensu zuwa gefen tekun, suka bar kome da kome, suka bi Yesu.

12 Wata rana Yesu yana a wani gari, sai ga wani mutumin da cutar fatar jiki ta ci ƙarfinsa ya zo. Da ganin Yesu, sai ya durƙusa, ya roƙe shi, yana cewa, “Ya maigirma, idan ka yarda, kana iya ka tsabtace ni in zama marar ƙazanta!”

13 Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa shi, yana cewa, “Na yarda, na tsabtace ka, ka zama marar ƙazanta!” Nan da nan, sai cutar fatar jikinsa ta bar shi.

14 Sai Yesu ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka je ka nuna kanka a wurin firist, ka kuma yi hadaya kamar yadda Musa ya ce a yi don tsabtacewa. Ka yi haka don ka tabbatar wa jamaˈa cewa an tsabtace ka.”

15 Amma duk da haka sai gaba-gaba labarin Yesu yake ta yi, mutane da yawa suka dinga zuwa domin su ji shi, suna neman warkewa daga dukan cututtukansu.

16 Amma Yesu yakan tafi wani wurin da babu kowa domin yin adduˈa.

17 Wata rana Yesu yana koyarwa sai waɗansu Farisiyawa da malaman Koyarwar Musa waɗanda suka zo daga kowane ƙauye da yake a yankin Galili, da na Yahudiya, da kuma daga birnin Urushalima, suna zaune a wurin. Ikon Ubangiji kuwa yana tare da shi domin yă warkar da masu ciwo.

18 Ana nan sai ga waɗansu mutane sun kawo wani shanyayye kwance a kan tabarma. Suna ƙoƙari su kai shi cikin gida domin su kwantar da shi a gaban Yesu,

19 amma ba su sami hanya ba saboda yawan mutane. Da suka ga babu dama, sai suka hau kan rufin ɗakin, suka ɓalle rufin suka saukar da shi duk da tabarmar da yake kwance a kai, suka ajiye shi a tsakiyar mutane a gaban Yesu.

20 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa mutumin da yake kwance, “An gafarta maka zunubanka, abokina.”

21 Malaman Koyarwar Musa tare da Farisiyawa suka fara ce wa junansu, “Wane ne wannan da yake yin maganar saɓo wa Allah haka! Allah ne kaɗai yake da iko yă gafarta zunubai!”

22 Da Yesu ya gane abin da suke tunani, sai ya ce musu, “Don me kuke wannan tunani?

23 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’?

24 Amma ina so ku sani cewa Ɗan mutum yana da iko yă gafarta zunubai a duniya.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ka ɗauki tabarmarka ka tafi gida!”

25 Nan da nan mutumin nan ya tashi a idon kowa, ya ɗauki tabarmar da dā yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.

26 Dukansu suka kama baki suna mamaki! Cike da tsoro, suka yabi Allah, suna cewa, “Yau mun ga abin mamaki!”

27 Bayan haka, Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji mai suna Lawi, yana zaune a wurin karɓar haraji. Sai Yesu ya ce masa, “Bi ni!”

28 Sai Lawi, ya bar kome da kome, ya tashi, ya bi shi.

29 Sai Lawi ya shirya babban biki a gidansa, ya kuma gayyaci Yesu. Masu karɓar haraji da yawa tare da waɗansu mutane suna nan suna cin abinci tare da su.

30 Amma Farisiyawa da malaman Koyarwar Musa suka fara gunaguni, suna ce wa almajiran Yesu, “Don me kuke ci, kuke kuma sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Masu lafiyar jiki ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.

32 Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai don masu zunubi su tuba, su kuma canja rayuwarsu.”

33 Waɗansu suka ce wa Yesu, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi a kai a kai sukan kuma yi adduˈa, haka ma na Farisiyawa, amma naka sai ci da sha suke yi kullum.”

34 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Kuna tsammani za ku iya hana abokan ango abinci, in suna tare da angon?

35 Lokaci yana zuwa da za a ɗauki angon a bar su. To, a lokacin ne za su yi azumi.”

36 Sai Yesu ya ba su wani misali ya ce, “Ba wanda zai yage ƙyalle daga sabuwar riga yă yi wa tsohuwar riga faci da shi. Idan ya yi haka, sai yă zama ya naɗe sabuwar rigarsa, kuma facin ba zai yi wa tsohuwar rigar kyau ba.

37 Kuma ba wanda zai zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. Idan ya yi haka, sai sabon ruwan inabi yă farfashe salkunan ruwan inabin yă zube salkuna kuma su lalace.

38 Sabon ruwan inabi dai sai a zuba shi a cikin sababbin salkuna!

39 Ba wanda zai so shan sabon ruwan inabi bayan da ya sha tsohon. Ai, yakan ce tsohon ya fi daɗi!”

Open Bible reader