Hausa Bible
Yahuza 1
1 Daga Yahuda bawan Yesu Almasihu, ɗanˈuwan Yakub, zuwa gare ku, ku waɗanda Allah ya kira, waɗanda Allah Uba yake ƙauna, Yesu Almasihu kuma yake kiyayewa.
2 Bari jinƙai, da salama, da ƙauna su zama naku a yalwace.
3 Ya ku waɗanda nake ƙauna, dā ma na yi marmarin rubuta muku game da ceton nan namu duka. Amma daga baya na ga ya zama dole ne in rubuta muku in gargaɗe ku ku dage sosai ku kiyaye bangaskiyarmu wadda Allah ya danƙa wa tsarkakansa, sau ɗaya tak, ba ƙari.
4 Na faɗi wannan ne saboda waɗansu mutanen da suka shiga cikinku a ɓoye, waɗanda tun dā aka ƙaddara su ga hukunci. Ba su da hali irin na Allah, suna kuma mai da alherin Allah ya zama hanyar neman jin daɗi na rashin kunya. Suna yin musūn Yesu Almasihu wanda shi ne kaɗai Shugabanmu da kuma Ubangijinmu.
5 Ko da yake kun riga kun sani, ina so in tuna muku yadda Ubangiji ya ceci mutanensa daga ƙasar Masar, amma duk da haka daga baya ya halaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.
6 Ku tuna kuma da malaˈikun da ba su kiyaye matsayinsu na iko ba, amma suka bar ainihin wurin zamansu. Waɗannan fa Ubangiji ya tsare su a duhu, a ɗaure da sarƙa ta har abada su jira shariˈa ta babbar Ranar nan.
7 Kada ku manta da yadda Sodom da Gomora da garuruwan da suke kewaye da su, su ma sun ba da kansu ga rayuwar lalata, da mummunar shaˈawar jiki kamar wadda ba ta yi daidai da halittar Allah ba. Garuruwan nan sun zama misalin masu shan hukunci a wuta ta har abada.
8 Haka yake da masu dogara a kan mafarkai, sukan ƙazantar da jikinsu, sukan ƙi miƙa kansu ga masu iko, su kuma yi wa halittu masu daraja a sama baƙar magana.
9 Ko Mikayel, shugaban malaˈiku ma bai yi irin wannan ba. A saˈad da yake jayayya da Shaiɗan, suna gardama a kan gawar Musa, shi Mikayel bai yi ƙarfin hali yă yanke masa hukunci da baƙar magana ba. Ya ce kawai, “Ubangiji yă tsawata maka!”
10 Amma waɗannan mutane suna zagi da baƙar magana a kan dukan abin da ba su gane ba, kuma waɗannan abubuwan da suka sani bisa ga jiki, kamar dabbobi marasa hankali, irin waɗannan abubuwa ne za su kai su ga halaka.
11 Kaitonsu! Sun bi hanyar Kayinu. Domin neman riba sun fāɗi cikin kuskure irin na Balaˈam, sun kuma halaka ta wurin tawaye irin na Kora.
12 Waɗannan mutane kuwa zamansu a cikin taronku na ƙauna abin tabo ne, saˈad da suke ci suke kuma sha tare da ku ba kunya ba tsoro. Su makiyaya ne waɗanda suke ciyar da kansu kawai. Suna nan kamar hadarin da iska takan kora, amma babu ruwa a ciki. Suna kamar itatuwa marasa ˈyaˈya da rani, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke, kuma sun mutu gaba ɗaya.
13 Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu tashi sama cikin hauka, suna taƙama da abubuwan kunya waɗanda kumfa suke kawai. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka yi musu ajiyar baƙin duhu na har abada.
14 Enok ma, wanda yake na tsara ta bakwai daga Adam, shi ma ya yi annabci a kan waɗannan mutane cewa, “Duba dai, Ubangiji yana zuwa da dubban malaˈikunsa masu tsarki,
15 domin yă aikata hukuncinsa a kan kowa. Zai nuna wa marasa hali iri na Allah dukan aikinsu na rashin halin Allah. Zai tone dukan mugayen maganganun da masu zunubi marasa hali iri na Allah suka faɗa game da shi.”
16 Waɗannan mutane dai masu gunaguni ne, masu ganin laifin waɗansu, masu bin muguwar shaˈawarsu, masu cike da yabon kansu, masu zaƙin baki domin samun riba ta kansu.
17 Amma ya ku waɗanda nake ƙauna, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Almasihu suka faɗa a dā cewa zai faru.
18 Sun faɗa muku cewa, “A zamanin ƙarshe za a yi waɗansu mutane masu baˈa, waɗanda za su bi irin tasu shaˈawa wadda ba ta hali iri na Allah ba.
19 Su ne mutane waɗanda sukan kawo rabuwa, masu bin shaˈawar jiki, saboda ba su da Ruhun Allah.”
20 Amma ya ku waɗanda nake ƙauna, ku yi ta gina kanku a kan bangaskiyarku nan mafi tsarki. Ku kuma yi adduˈa ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
21 Ku kiyaye kanku cikin ƙaunar Allah, kuna jiran Ubangijinmu Yesu Almasihu wanda cikin jinƙansa zai kai ku ga rai na har abada.
22 Ku dinga nuna jinƙai ga waɗanda suke yin shakka.
23 Ku cece waɗansu kamar kuna fizge su daga cikin wuta. Waɗansu kuwa ku nuna musu jinƙai, amma tare da tsoro, har ma kuna ƙyamar tufafin da halin mutuntakarsu ya ƙazantar.
24 To, yabo ya tabbata ga wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa tabo a gaban ɗaukakarsa da farin ciki sosai.
25 Gare shi kuma, wanda shi kaɗai yake Allah mai cetonmu, ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, ɗaukaka da daraja da mulki da iko su tabbata tun daga farkon zamanai, da yanzu, da kuma har abada! Amin.