Hausa Bible
Yahuza 1:12
Waɗannan mutane kuwa zamansu a cikin taronku na ƙauna abin tabo ne, saˈad da suke ci suke kuma sha tare da ku ba kunya ba tsoro. Su makiyaya ne waɗanda suke ciyar da kansu kawai. Suna nan kamar hadarin da iska takan kora, amma babu ruwa a ciki. Suna kamar itatuwa marasa ˈyaˈya da rani, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke, kuma sun mutu gaba ɗaya.
Open Bible reader