Skip to content

Hausa Bible

Yahaya 21

1 Bayan haka Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa a bakin Tekun Tibariya. Kuma ga yadda ya bayyana kansa.

2 Siman Bitrus, da Toma wanda ake ce da shi ˈYan Biyu, da Nataniyel daga Kana ta Galili, da ˈyaˈyan Zabadi, da kuma waɗansu almajiran biyu duk suna nan tare.

3 Sai Bitrus ya ce, “Za ni kamun kifi.” Sauran almajiran suka ce, “Mu ma za mu tafi tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgin ruwa suka tafi. Amma a wannan dare ba su kama kome ba.

4 Gari yana wayewa ke nan, sai ga Yesu a tsaye a bakin tekun, amma almajiran ba su gane Yesu ne ba.

5 Sai Yesu ya ce musu, “Samari, kuna da kifi?” Suka amsa masa suka ce, “Aˈa.”

6 Yesu ya ce musu, “Ku jefa ragar kamun kifinku a hannun dama na jirgin, za ku samu.” Suka jefa shi kamar yadda Yesu ya faɗa, suka kama kifi da yawa har suka kāsa jawo ragar kamun kifin zuwa cikin jirgin.

7 Sai almajirin nan da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Da Siman Bitrus ya ji cewa Ubangiji ne, sai ya ɗauki rigarsa ya sa, domin tun dā ma a tuɓe yake. Saˈan nan ya yi tsalle ya shiga cikin ruwan.

8 Sauran almajiran kuwa suka zo bakin tekun a cikin jirgin, suna jan ragar kamun kifin cike da kifi. Don dā ma ba su da nisa da bakin tekun, misali ƙafa ɗari uku ne.

9 Da fitowarsu bakin ruwa, sai suka ga garwashin wuta a wurin, da kifi a kai, da burodi kuma.

10 Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifi daga cikin waɗanda kuka kama yanzu.”

11 Sai Siman Bitrus ya hau jirgin ruwan, ya jawo ragar kamun kifin zuwa bakin ruwa. Ragar kamun kifin yana kuwa cike da manyan kifaye ɗari da hamsin da uku. Amma duk da yawansu haka, ragar kamun kifi bai yage ba.

12 Sai Yesu ya ce musu, “Ku zo ku ci abincin safe.” A cikin almajiran kuwa ba wanda ya yi ƙarfin hali yă tambaye shi kowane ne shi, domin sun san cewa Ubangiji ne.

13 Sai Yesu ya zo ya ɗauki burodin ya ba su, ya kuma ɗauki kifin ya ba su.

14 Wannan shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiran bayan da aka tashe shi daga matattu.

15 Da suka gama cin abincin safe, sai Yesu ya tambayi Siman Bitrus ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata fiye da waɗannan?” Sai Bitrus ya amsa masa ya ce, “I, Ubangiji, ai, ka san yadda nake sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka ciyar da tumakina.”

16 Sai Yesu ya sāke tambayarsa sau na biyu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ai, ka san ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina.”

17 Yesu ya tambaye shi sau na uku ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki, don a tambaya ta uku Yesu ya ce “Kana sona?” Sai shi kuwa ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, ai, ka san dukan kome, ka san ina sonka.” Yesu ya ce masa, “To, ka ciyar da tumakina.

18 Hakika, ina gaya maka, lokacin da kake saurayi kakan sa wa kanka sutura ka je duk inda ka ga dama, amma in ka tsufa za ka miƙe hannuwanka, wani yă sa maka sutura, yă kai ka inda ba ka so ka tafi.”

19 Yesu ya faɗa wannan ne domin yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi don yă ɗaukaka Allah. Bayan wannan magana, Yesu ya ce wa Bitrus, “Bi ni.”

20 Bitrus ya juya ya dubi baya, sai ya ga almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. Wannan shi ne almajirin da ya jingina a ƙirjin Yesu a lokacin cin abincin Bikin Ƙetarewa. Shi ne wanda ya tambayi Yesu ya ce, “Ya Ubangiji, wane ne zai bashe ka?”

21 Da Bitrus ya gan shi, sai ya tambayi Yesu ya ce, “Ubangiji, wannan mutum fa?”

22 Sai Yesu ya ce masa, “Idan nufina ne yă rayu har in dawo, ina ruwanka? Kai dai, ka bi ni!”

23 Saboda haka wannan labari ya yi ta bazuwa cikin masu bin Yesu cewa almajirin nan ba zai mutu ba. Amma Yesu bai ce ba zai mutu ba. Ya dai ce, “Idan nufina ne yă rayu har in dawo, ina ruwanka?”

24 Wannan shi ne almajirin da yake ba da shaida a kan waɗannan abubuwa, ya kuma sa su a rubuce. Mun kuma san cewa shaidarsa gaskiya ce.

25 Akwai waɗansu abubuwa da yawa kuma waɗanda Yesu ya yi, da a ce za a rubuta duka, ina tsammani ko duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba.

Open Bible reader