Hausa Bible
Yahaya 12
1 Bikin Ƙetarewa ya rage sauran kwana shida ke nan, sai Yesu ya je Betani, wato, inda Liˈazaru, mutumin da Yesu ya tā da shi daga matattu yake da zama.
2 Nan aka yi masa abincin dare, Marta ce kuwa ta raba abincin, Liˈazaru kuwa yana ɗaya daga cikin mutanen da suka ci abincin tare da Yesu.
3 Sai Maryamu ta ɗauki kwalaba cike da wajen rabin lita na nardi, man ƙanshi mai tsada, ta juya a ƙafafun Yesu, saˈan nan ta share ƙafafun da gashin kanta. Ƙanshi mai daɗi na wannan mai ya cika dukan gidan.
4 Amma Yahuda Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa, wato wanda zai bashe shi, ya ce,
5 “Me ya sa ba a sayar da man nan a kan yawan kuɗin da lebura zai samu a ranaku ɗari uku, saˈan nan a ba masu bukata kuɗin ba?”
6 Yahuda ya faɗa wannan magana ne ba domin yana kula da masu bukata ba, amma domin shi ɓarawo ne. Gama shi ne mai riƙe jakar kuɗinsu, kuma yakan sata daga ciki.
7 Sai Yesu ya ce, “Ƙyale ta, dā ma ta ajiye shi domin shirin ranar da za a binne ni.
8 Ai, kullum masu bukata suna tare da ku, amma ba kullum kuke tare da ni ba.”
9 Da taron Yahudawa mai yawa suka ji labari cewa Yesu yana a nan, sai suka zo, ba don Yesu shi kaɗai ba, amma domin su ga Liˈazaru ma wanda Yesu ya tashe shi daga matattu.
10 Sai manyan firistoci suka yi shawara su kashe Liˈazaru shi ma,
11 domin ta dalilin Liˈazaru ne Yahudawa da yawa suna rabuwa da firistocin suna ba da gaskiya ga Yesu.
12 Washegari mutane da yawa waɗanda suka zo Bikin Ƙetarewa, suka ji cewa Yesu yana kan hanya zuwa Urushalima.
13 Sai suka ɗaɗɗauki rassan itatuwan dabino suka fiffita, suka karɓe shi, suna tā da murya suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa a cikin sunan Ubangiji! Albarka ta tabbata ga Sarkin Israˈila!”
14 Da Yesu ya sami wani ɗan jaki sai ya hau, kamar yadda aka rubuta cewa,
15 “Kada ku ji tsoro, ya ke zuciyata Sihiyona. Ga Sarkinku yana zuwa a kan ɗan jaki!”
16 Da farko almajiransa ba su gane abin nan ba, amma bayan da aka ɗaukaka Yesu, suka tuna cewa an yi wannan rubutu a kansa, kuma abubuwan sun faru daidai kamar yadda aka rubuta.
17 Mutanen da suke tare da shi a lokacin da ya kira Liˈazaru yă fito daga kabari, ya kuma tashe shi daga matattu, suka yi ta faɗa wa mutane abin da Yesu ya yi.
18 Mutane da yawa sun tafi su karɓi Yesu ne domin sun ji wannan alamar ban mamakin da ya yi.
19 Sai Farisiyawa suka yi magana da juna suka ce, “Ku duba fa, ba ku yi nasara ko kaɗan, ga shi dukan duniya tana binsa!”
20 To, a cikin waɗanda suka zo bikin domin yin sujada akwai waɗansu Helenawa.
21 Sai suka zo wurin Filibus, mutumin Betsaida ta Galili, suka ce masa, “Maigirma, muna bukata mu tattauna da Yesu.”
22 Filibus ya je ya gaya wa Andarawus, sai su biyu suka tafi suka faɗa wa Yesu.
23 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum.
24 Hakika, ina gaya muku, in ba dai an binne ƙwayar alkama ta mutu ba, za ta zauna ita kaɗai. Amma in ta mutu sai ta ba da ˈyaˈya da yawa.
25 Duk wanda yake ƙaunar ransa zai rasa shi. Duk wanda ya ƙi ransa a duniyar nan, zai kiyaye shi ke nan ga rai na har abada.
26 Duk wanda zai yi mini hidima, dole ne yă bi ni. A duk inda nake kuwa mai yi mini hidima zai kasance tare da ni. Ubana kuwa zai girmama duk wanda yake yi mini hidima.”
27 “Yanzu ina jin nauyi a raina. Me zan ce ke nan? In ce, ‘Ya Uba, ka ɗauke mini wannan lokaci?’ Aˈa, ai, dā ma na zo musamman domin wannan lokaci ne.
28 Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai murya ta fito daga sama ta ce, “Ai, na riga na ɗaukaka shi, zan ƙara ɗaukaka shi kuma.”
29 Da mutanen da suke tsaye a wurin suka ji muryar, suka ce, “An yi tsawa.” Waɗansu kuwa suka ce, “Malaˈika ne ya yi masa magana.”
30 Yesu ya ce musu, “Wannan murya ta zo dominku ne, amma ba saboda ni ba.
31 Yanzu ne za a yi wa duniyar nan shariˈa, yanzu ne kuma za a tumɓuke mai mulkin duniyar nan.
32 Saˈad da an ɗaga ni daga ƙasa kuwa, zan jawo dukan mutane zuwa wurina.”
33 Yesu ya faɗa wannan ne domin yă nuna irin mutuwar da zai yi.
34 Sai mutanen suka ce wa Yesu, “Ai, Koyarwarmu ta gaya mana cewa, Almasihun zai rayu har abada. To, yaya za ka ce lallai ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?”
35 Yesu ya ce musu, “Hasken yana tare da ku na ɗan ƙaramin lokaci. Ku yi tafiya tun hasken yana tare da ku, kada duhu ya same ku. Mai tafiya cikin duhu bai san inda za shi ba.
36 Ku gaskata da hasken, tun kuna tare da shi, domin ku zama ˈyaˈyan haske.” Bayan da Yesu ya yi wannan magana, sai ya tafi ya ɓoye kansa daga gare su.
37 Ko da yake Yesu ya sha yin alamun ban mamaki da yawa a gabansu, duk da haka ba su ba da gaskiya gare shi ba.
38 Wannan ya faru ne domin a cika abin da annabi Ishaya ya faɗa cewa, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu, ga wa kuma aka bayyana masa abin da hannun Ubangiji ya aikata?”
39 Shi ya sa ba su iya ba da gaskiya ba, kamar yadda Ishaya ya kuma faɗa a wani wuri cewa,
40 “Ya mai da su makafi, ya kuma taurara zuciyarsu, domin kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuciya, har su juyo wurina in warkar da su.”
41 Ishaya ya faɗa haka ne domin ya ga ɗaukakar Yesu, ya kuma ba da labarinsa.
42 Duk da haka mutane da yawa sun ba da gaskiya ga Yesu, har ma da yawa daga cikin shugabanninsu suka ba da gaskiya gare shi. Amma don tsoron Farisiyawa ba su ce sun gaskata ba domin kada a kore su daga majamiˈa.
43 Gama sun fi son yabo daga bakin mutane fiye da yabo daga wurin Allah.
44 Sai Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Duk wanda yake ba da gaskiya gare ni, ba gare ni yake ba da gaskiya kaɗai ba, amma ga wanda ya aiko ni ne.
45 Duk wanda yake dubana, yana kuma ganin wanda ya aiko ni ne.
46 Na zo kamar haske ne a cikin duniya domin kada duk wanda yake ba da gaskiya gare ni yă zauna a cikin duhu.
47 “Duk wanda ya ji koyarwata, bai kuwa kiyaye ta ba, ba ni ne mai yi masa hukunci ba. Gama ba don in yi wa duniya hukunci na zo ba, amma domin in ceci duniya ne.
48 Wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi maganata ba, yana da mai yi masa hukunci, maganar da na faɗa, ita za ta hukunta shi a ranar ƙarshe.
49 Abubuwan da nake koyarwa ba daga wurina ba ne, Ubana da ya aiko ni ne ya umarce ni game da abin da zan faɗa da maganar da zan yi.
50 Na kuma sani rai na har abada ana samunsa ne daga umarnin da Uba ya bayar. Saboda haka duk abin da na faɗa, na faɗa daidai yadda Uba ya gaya mini in faɗa ne.”