Hausa Bible
Ibraniyawa 12
1 Saboda haka, da yake taron shaidu masu yawa ƙwarai sun kewaye mu, bari mu tuɓe dukan abin da zai hana mu, da kuma kowane zunubin da ya riƙe mu kam-kam, bari kuma mu yi tseren nan da aka sa a gabanmu cikin naciya.
2 Bari mu kafa ido ga Yesu wanda shi ne tushen bangaskiyarmu da kuma mai kawo cikawar bangaskiyarmu. Saboda farin cikin da aka sa a gabansa, ya jimre wa gicciye, ya mai da abin kunya ba kome ba, a yanzu kuma yana zaune a hannun daman kujerar mulkin Allah.
3 Ku lura fa da wannan mutumin da ya yi haƙuri da irin ƙiyayyar da masu zunubi suka yi masa, domin kada ku gaji, ko kuwa ku fid da zuciya.
4 A cikin kokawarku gāba da zunubi, famar da kuka yi ba ta kai ku ga zub da jininku ba.
5 Ko kun mance ne da maganar ƙarfafawa wadda Allah ya yi, wadda kuma take ce da ku ˈyaˈyansa? “Ya ɗana, kada ka mai da horon Ubangiji abin banza, kada ka fid da zuciya idan ya tsawata maka.
6 Gama Ubangiji yakan horar da duk wanda yake ƙauna, yakan kuma hori duk ɗan da ya karɓa.”
7 Ku jimre da wuyar da kuke sha, ku ɗauka horarwa ce. Ta haka, Allah yana yi da ku kamar ˈyaˈyansa ke nan. Wane ɗa ne babansa ba ya yi masa horo?
8 Idan ba a yi muku horon nan da ake yi wa dukan ˈyaˈyan Allah ba, to, ku shegu ne ke nan, ba ˈyaˈyan gida ba.
9 Ban da haka ma, muna da ubanninmu na jiki waɗanda suke yi mana horo, mu kuwa muna girmama su. Ashe, ba za mu fi yarda da horon Ubanmu na ruhaniya, domin mu rayu ba?
10 Ubanninmu na jiki sukan yi mana horo na ɗan lokaci ta hanyar da ta fi kyau a ganinsu, amma Allah yakan yi mana horo saboda amfaninmu ne, domin mu sami rabonmu cikin tsarkinsa.
11 Duk horon da akan yi mana yakan kawo zafi a lokacin, ba jin daɗi ba. Amma daga baya yakan haifar da adalci da salama ga duk waɗanda suka yi koyi da horon.
12 Saboda haka, ku miƙe hannuwanku da suka gaji, ku kuma ƙarfafa gwiwoyinku marasa ƙarfi.
13 Ku miƙe hanyoyi domin ƙafafunku, domin kada mai ciwon ƙafa yă sami damuwa, maimakon warkewa.
14 Ku yi iyakacin ƙoƙari ku zauna lafiya da kowa, ku kuma zama da tsarki, gama ba wanda zai ga Ubangiji idan ba tare da tsarki ba.
15 Ku lura fa kada kowa yă kāsa samun alherin Allah. Ku yi hankali kada wani yă zama kamar tushen ɗacin rai wanda yakan kawo ɓarna, yă kuma ƙazantar da alˈumma gaba ɗaya.
16 Ku lura fa, kada wani yă zama mai lalata, ko marar halin Allah kamar Isuwa, wanda ya sayar da gādonsa na ɗan fari saboda ƙwarya ɗaya tak na abinci.
17 Daga baya, kamar yadda kun sani, saˈad da ya so yă karɓi gādon albarkar nan, sai aka ƙi shi. Bai kuwa sami zarafin yin gyara ba, ko da yake ya nemi albarkar nan da hawaye.
18 Ba ku zo wurin Babban Tudun Sinai wanda ana iya taɓawa ba, ko wurin wuta mai ci sosai, ko wurin duhu baƙi ƙirin, ko babban hadari,
19 ko busar ƙaho, ko kuwa murya mai yin magana yadda masu jinta suka yi roƙo cewa kada a ci gaba da yi musu maganar.
20 Suka yi roƙon ne domin ba su iya jimre wa umarnin nan da aka bayar ba cewa, “Ko da dabba ce ta taɓa babban tudun, sai a jejjefe ta har ta mutu.”
21 Wannan abin da suka gani ya zama abin tsoro ƙwarai, har ma Musa ya ce, “Jikina yana rawa saboda tsoro.”
22 Amma kun zo wurin Babban Tudun Sihiyona ne, da birnin Allah Mai Rai, wato Urushalima ta sama, da taron farin ciki na malaˈiku masu ɗumbun yawa.
23 Kun zo ga jamaˈar masu bi ˈyaˈyan fari waɗanda sunayensu suna a rubuce a sama. Kun zo wurin Allah wanda shi ne mai yi wa kowa shariˈa, da wurin ruhohin mutane masu adalci waɗanda aka mai da su cikakku.
24 Kun zo wurin Yesu wanda shi ne mai tsayawa tsakanin Allah da mutanensa a cikin sabuwar yarjejeniya, da kuma wurin jinin nan da aka yayyafa wanda yake yin magana mafi kyau fiye da jinin Habila.
25 Ku lura fa, kada ku ƙi shi wanda yake magana. Ku sani cewa su waɗanda suka ƙi su karɓi wanda ya yi musu gargaɗi a nan duniya ba su tsira ba, balle fa mu! Ta yaya mu za mu tsira idan mun ƙi wanda yake yi mana gargaɗi daga sama?
26 A lokacin kuwa muryar Allah ta girgiza duniya. Amma yanzu ya yi alkawari cewa, “Zan girgiza duniya sau ɗaya kuma, ba duniya kaɗai ba, amma har da sammai.”
27 Wannan magana, “Sau ɗaya kuma,” ta nuna za a kawar da abin da aka girgiza, wato, za a kawar da abubuwan da aka halitta, domin abubuwan da ba za a iya girgiza su ba su kasance.
28 To, da yake muna karɓar mulkin da ba za a iya girgiza ba, bari mu yi godiya, mu kuma miƙa wa Allah sujadar da ta dace a cikin tsoro da ban girma,
29 gama Allahnmu wuta ne mai cinyewa.