Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 9

1 Shawulu kuwa yana ci gaba da tsananta wa masu bin Ubangiji tsanani sosai, har da cewa zai kashe su. Sai ya je wurin babban firist,

2 ya roƙe shi yă ba shi wasiƙu zuwa majamiˈun Dimashƙu, don idan ya sami masu bin Hanyar Ubangiji, maza ko mata, yă kawo su a ɗaure a birnin Urushalima.

3 Yana cikin tafiya ke nan, ya yi kusa da Dimashƙu, ba labari, sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi.

4 Sai ya fāɗi a ƙasa, ya kuma ji wata murya tana ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”

5 Shi kuwa ya ce, “Wane ne kai, Maigirma?” Sai muryar ta amsa cewa, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta masa.

6 Ka tashi ka shiga cikin gari, a can za a faɗa maka abin da za ka yi.”

7 Abokan tafiyarsa kuwa suka kāsa magana, suna jin murya, amma ba su ga kowa ba.

8 Sai Shawulu ya tashi, amma da ya buɗe ido bai iya gani ba. Sai suka riƙe masa hannu suka kawo shi Dimashƙu.

9 Ya yi kwana uku, ba ya gani, ba ya ci, kuma ba ya sha.

10 To, akwai wani mai bi a Dimashƙu, mai suna Hananiya. Ubangiji ya yi masa magana cikin ruˈuya ya ce, “Hananiya!” Shi kuwa ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.”

11 Sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi ka tafi titin nan da ake ce da shi Miƙaƙƙe, ka je gidan Yahuda, ka tambaya ko akwai wani mutumin Tarsus, mai suna Shawulu. Ga shi nan yana adduˈa a wurin.

12 Har ma a cikin ruˈuya ya ga wani mutum mai suna Hananiya ya shigo, ya sa masa hannun albarka domin yă sāke samun ganin gari.”

13 Amma Hananiya ya amsa ya ce, “Ubangiji, na sha jin labarin mutumin nan wurin mutane da yawa a kan yawan muguntar da ya yi wa tsarkaka a Urushalima.

14 Ga shi kuma yana da izni daga manyan firistoci yă kama duk wanda yake kira ga sunanka.”

15 Amma Ubangiji ya ce masa, “Kai dai, ka je, domin shi mutum ne da na zaɓa yă yi aikina domin yă sanar da sunana ga waɗanda ba Yahudawa ba, da sarakuna, da kuma Israˈilawa.

16 Ni da kaina zan nuna masa wuyar da lallai zai sha saboda sunana.”

17 Sai Hananiya ya tafi ya shiga gidan. Ya sa hannuwansa a kan Shawulu, ya ce, “Ɗanˈuwana Shawulu, Ubangiji ne ya aiko ni, wato Yesu wanda ya bayyana a gare ka a kan hanyar da ka biyo. Ya aike ni domin ka sāke iya gani, a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”

18 Nan take, sai wani abu kamar ɓawo ya fāɗi daga idanun Shawulu, sai ya sāke gani. Saˈan nan ya tashi, aka yi masa baftisma.

19 Sai ya ci abinci, ya sāke samun ƙarfi. Shawulu kuwa ya yi ˈyan kwanaki tare da sauran masu bin da suke a Dimashƙu.

20 Ba da daɗewa ba, Shawulu ya fara waˈazin Yesu a majamiˈun Yahudawa cewa Yesu shi ne Ɗan Allah.

21 Duk waɗanda suka ji shi kuwa suka yi mamaki, suka ce, “Ashe, ba wannan ne ya kakkashe ya kuma watsar da masu kiran sunan nan cikin sujada a Urushalima ba? Ba ya zo nan da niyyar yă kai su gaban manyan firistoci a ɗaure ba ne?”

22 Amma Shawulu ya ƙara samun ƙarfi, yana ta rikitar da hankalin Yahudawan da suke zama a Dimashƙu, yana tabbatar musu cewa Yesu shi ne Almasihu.

23 Bayan ˈyan kwanaki, Yahudawa suka yi shawara su kashe Shawulu.

24 Amma shi kuwa ya ji labarin shirinsu. Dare da rana suna zuba ido a ƙofofin gari domin su kashe shi,

25 amma da dare almajiransa suka ɗauke shi, suka saukar da shi ta wata taga a jikin bangon birnin cikin babban kwando.

26 Da Shawulu ya zo Urushalima, ya yi ƙoƙari yă shiga cikin almajiran, amma duk suka ji tsoronsa, don ba su yarda shi almajiri ba ne.

27 Amma Barnaba ya ɗauke shi ya kai shi wurin manzanni. Ya faɗa musu yadda Shawulu ya ga Ubangiji a hanya, da yadda Ubangiji ya yi masa magana, da kuma yadda Shawulu ya yi waˈazi da sunan Yesu a Dimashƙu, ba tsoro.

28 Daga nan Shawulu ya dinga shiga da fita da su a Urushalima,

29 yana waˈazi da sunan Ubangiji ba tsoro. Ya kuma dinga yin magana da Yahudawa masu jin Helenanci, yana kuma gardama da su, amma suka yi ta neman hanya su kashe shi.

30 Da ˈyanˈuwa suka gane haka, sai suka kai shi Kaisariya, suka aika da shi zuwa Tarsus.

31 Saˈan nan ne jamaˈar masu bi na dukan yankin Yahudiya, da Galili, da Samariya, ta sami zaman salama. Jamaˈar masu bi ta sami ƙarfi ta kuma ƙaru sosai ta wurin taimakon Ruhu Mai Tsarki, yayin da take rayuwa a cikin tsoron Ubangiji.

32 To, da Bitrus ya zazzaga yankin duka, sai ya kuma je wurin tsarkakan nan da suke zama a Lidda.

33 A wurin ya sadu da wani mutum mai suna Iniyas, wanda yake a kwance shekara takwas don shi shanyayye ne.

34 Sai Bitrus ya ce masa, “Iniyas, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka naɗe abin kwanciyarka.” Nan da nan Iniyas ya tashi.

35 Duk mutanen garuruwan Lidda da na Sharon kuwa suka gan shi wanda ya warke, saˈan nan suka juyo ga Ubangiji.

36 A Yoffa kuwa akwai wata mai bi, mai suna Tabita, wato Dokas ke nan. Macen kuwa ta ba da kanta ɗungum cikin yin aikin kirki, da kuma yin sadaka.

37 A kwanakin nan ta yi rashin lafiya, ta mutu. Da suka yi mata wanka, suka kwantar da jikinta a ɗakin sama.

38 Da yake Lidda tana kusa da Yoffa, saˈad da masu bi suka ji Bitrus yana Lidda, sai suka aika mutum biyu zuwa wurinsa, su roƙe shi yă zo wurinsu da sauri.

39 Sai Bitrus ya tashi ya tafi tare da su. Da ya iso, suka kai shi ɗakin saman. Duk mata waɗanda mazansu suka mutu, suka tsaya kusa da shi, suna kuka, suna nuna riguna da sauran kayan da Dokas ta yi musu tun tana tare da su.

40 Bitrus ya fitar da su waje duka, ya durƙusa ya yi adduˈa. Ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Sai ta buɗe ido. Da ta ga Bitrus, sai ta tashi ta zauna.

41 Bitrus kuwa ya miƙa mata hannu ya taimake ta ta tashi. Sai ya kira masu bi, da matan nan waɗanda mazansu suka mutu, ya miƙa musu ita da rai.

42 Labarin nan ya bazu a dukan Yoffa, mutane da yawa kuwa suka gaskata da Ubangiji.

43 Bitrus ya zauna kwanaki da yawa a Yoffa, a gidan wani mai aikin fatun dabbobi, sunansa Siman ne.

Open Bible reader