Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 7

1 Sai babban firist ya tambayi Istifanus ya ce, “Abubuwan nan, gaskiya ne?”

2 Sai Istifanus ya ce, “Ku ˈyanˈuwa da ubanni, ku saurare ni. Allah Maɗaukaki ya bayyana ga kakanmu Ibrahim saˈad da yake a ƙasar Mesofotamiya, tun bai zauna a Haran ba.

3 Allah ya ce masa, ‘Ka tashi daga ƙasarku, ka bar ˈyanˈuwanka, ka je ƙasar da zan nuna maka.’

4 Sai kakanmu ya tashi daga ƙasar Kaldiyawa, ya je ya zauna a Haran. Daga can kuma, bayan da babansa ya mutu, Allah ya kawo shi ƙasar nan da kuke zama a ciki yanzu.

5 Amma kuwa Allah bai ba shi gādon ƙasar ba, ko da taki ɗaya. Sai dai ya yi masa alkawari zai sa ƙasar ta zama tasa, shi da zuriyarsa da za su zo bayansa, ko da yake ba shi da yaro a lokacin.

6 Allah kuwa ya faɗa cewa, zuriyar Ibrahim za su yi baƙunci a wata ƙasa, mutanen ƙasar kuwa za su mai da su bayi, za su ba su wahala har shekara ɗari huɗu.

7 Allah ya ce zai hukunta ƙasar da za su bauta wa, bayan haka kuma zuriyar Ibrahim za su fito su bauta wa Allah a wannan wuri.

8 Allah kuma ya ba Ibrahim ƙaˈidar kaciya, alama ce ta yarjejeniya. Shi ya sa da Ibrahim ya haifi Ishaku, ya yi masa kaciya a rana ta takwas. Ishaku ya haifi Yakub, Yakub kuma ya haifi kakanninmu goma sha biyun nan.

9 “Kakannin nan kuwa, da yake suna kishin ɗanˈuwansu Yusuf, suka sayar da shi, aka kai shi Masar. Amma Allah yana tare da shi,

10 ya kuma fitar da shi daga dukan wahalarsa. Allah kuma ya sa ya zama mai hikima, mai farin jini a gaban Sarki Firˈauna na Masar. Firˈauna kuwa ya mai da Yusuf gwamna na ƙasar Masar da kuma shugaban dukan jamaˈar gidansa.

11 Ana nan, sai yunwa ta shigo a duk ƙasar Masar da Kanˈana, tare da wahala mai tsanani, har kakanninmu suka rasa abinci.

12 Amma da Yakub ya ji akwai hatsi a Masar, ya aiki yaransa wato, kakanninmu zuwa Masar. Wannan ya zama tafiyarsu ta farko.

13 A tafiyarsu ta biyu Yusuf ya sanar da kansa ga ˈyanˈuwansa, Firˈauna kuma ya gane asalinsa.

14 Sai Yusuf ya aika wa babansa Yakub yă zo, da kuma dukan ˈyanˈuwan Yusuf. Dukansu kuwa mutum sabaˈin da biyar ne.

15 Sai Yakub ya tafi Masar. A can ne ma ya mutu, shi da kakanninmu.

16 Sai aka kwaso su aka mai da su Shekem, aka sa su a kabarin da Ibrahim ya saya da kuɗin azurfa a wurin ˈyaˈyan Hamor a nan Shekem.

17 “Amma da lokacin cikar alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim ya yi kusa, jamaˈarmu ta ƙaru, ta yi yawa sosai a ƙasar Masar.

18 Saˈan nan aka yi wani sarki a Masar, wanda bai ma san ko wane ne Yusuf ba.

19 Wannan sarki kuwa ya cuci kabilarmu, ya yi wa kakanninmu tsanani yana sa a yar da jariransu, domin kada su rayu.

20 A lokacin nan ne aka haifi Musa, yaro mai kyan gaske. An yi renonsa wata uku a gidan babansa.

21 Da aka yar da shi, ˈyar Firˈauna ta ɗauke shi, ta lura da shi kamar ɗanta.

22 Sai aka koya wa Musa dukan hikimar Masarawa, shi kuwa mutum ne mai iko cikin magana da ayyukansa.

23 Da ya kai shekara arbaˈin ke nan, sai ya yi tunani yă je yă ziyarci ˈyanˈuwansa Israˈilawa.

24 Da ya ga wani mutumin Masar yana cutar ɗayansu, ya je ya taimaki mutumin Israˈilan nan, ya rama masa, ya bugi mutumin Masar, ya kashe shi.

25 Ya yi tsammani ˈyanˈuwansa za su gane Allah zai yi amfani da shi domin yă cece su. Amma mutanen ba su gane ba.

26 Washegari kuma ya ga waɗansu Israˈilawa suna faɗa, sai ya so yă shirya su, ya ce, ‘Ku jamaˈa, ku ˈyanˈuwa ne fa, don me kuke cutar juna?’

27 Amma mai cutar ɗanˈuwansa ya ture Musa gefe, ya ce, ‘Wa ya sa ka ka zama shugabanmu da alƙalinmu?

28 Ashe, kana so ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan na jiya?’

29 Da Musa ya ji haka, sai ya gudu ya yi zaman baƙunci a ƙasar Midiyan, a can ya haifi ˈyaˈya biyu maza.

30 “To, bayan shekara arbaˈin, wani malaˈika ya bayyana ga Musa a harshen wuta, a ƙaramin itace a wani daji kusa da Babban Tudun Sinai.

31 Da Musa ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya zo kusa domin yă duba, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,

32 ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakub.’ Sai jikin Musa ya fara rawa, bai ma iya ƙarfin halin dubawa ba.

33 “Sai Ubangiji ya ce masa, ‘Ka cire takalmanka, domin wurin nan da kake tsaye wuri mai tsarki ne.

34 Lallai, na ga wahalar da ake ba jamaˈata da suke Masar, na ji kukansu, na kuma sauko in cece su. To, yanzu sai ka yi shiri in aike ka zuwa Masar.’

35 “To, shi Musan nan ne suka ƙi, suna cewa, ‘Wa ya sa ka ka zama shugabanmu da alƙalinmu?’ Shi ne Allah ya aiko yă zama shugaba, da mai ceto, ta wurin malaˈikan nan da ya bayyana a gare shi a ƙaramin itacen nan.

36 Shi ne kuwa ya fito da su, bayan ya yi ayyukan ban mamaki, da kuma alamu a ƙasar Masar, da Tekun Ciyawar Iwa, da kuma a cikin daji har shekara arbaˈin.

37 Musan nan shi ne wanda ya ce wa Israˈilawa, ‘Allah zai aiko muku da wani annabi daga cikin mutanenku, kamar yadda ya aike ni.’

38 Musa shi ne mutumin da ya tattara jamaˈar Israˈila a cikin daji. Ya kasance a can tare da kakanninmu da kuma malaˈikan nan da ya yi magana da shi a kan Babban Tudun Sinai. Shi ne kuma ya karɓo kalma mai ba da rai daga wurin Allah ya kawo mana.

39 Amma kakanninmu suka ƙi yi masa biyayya, suka ƙi jin kalmarsa, suka yi marmarin komawa ƙasar Masar.

40 “Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana allolin da za su yi mana jagora, don Musan nan kam, da ya fito da mu daga ƙasar Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.’

41 A lokacin nan, suka yi siffar ɗan bijimi, suka miƙa wa gunkin nan hadaya, suka dinga murna da aikin da suka yi da hannunsu.

42 “Saboda haka Allah ya juya musu baya, ya miƙa su ga bautar rana da wata da taurarin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a littafin annabawa cewa, “ ‘Ku jamaˈar Israˈila, ni ne kuka yanka wa dabbobi, kuka miƙa wa hadaya, har shekara arbaˈin a cikin daji?

43 Ai, da tentin gunki Molek kuka dinga yawo, da tauraron gunkinku Refan, wato, gumakan nan da kuka yi don ku yi musu sujada. Ni kuwa zan kawar da ku can gaba da Babila.’

44 “A dā kakanninmu suna da Tentin Shaidar Kasancewar Allah a daji. Wannan ne tentin da Allah ya umarci Musa yă yi, kuma an yi shi daidai kamar yadda Allah ya nuna wa Musa.

45 Tentin nan ne kakanninmu suka gāda, suka kuma kawo a ƙasar nan a zamanin Yoshuwa, saˈad da suka karɓi ƙasar a hannun alˈumman da Allah ya kora a idonsu. Tentin nan kuwa yana nan har zuwa zamanin Dawuda.

46 Dawuda kuwa ya sami farin jini a gaban Allah, har ya yi roƙo domin yă gina wurin zama domin Allahn kakanmu Yakub.

47 Amma Solomon ne ya yi wa Allah ginin.

48 “Duk da haka, Mafi Ɗaukaka ba ya zama a gidajen da mutum ya gina. Yadda annabi ya ce,

49 “ ‘Sama shi ne kujerar mulkina, ƙasa kuwa wurin sa ƙafata ne, Wane irin gida ne za ku gina mini? in ji Ubangiji. Ko kuwa wane wuri ne wurin hutuna?

50 Ba ni ne na halicci duk waɗannan abubuwan ba?’ ”

51 “Ku masu taurin kai, masu taurin zuciya, masu kunnen ƙashi, kullum kuna ƙin biyayya da Ruhu Mai Tsarki. Yadda kakanninku suka yi, haka ku ma kuke yi.

52 Cikin annabawa, akwai wanda kakanninku ba su tsananta masa ba? Sun kashe waɗanda suka yi magana a kan zuwan Mai Adalcin nan. Ku kuwa, kuka bashe shi, kuka kashe shi.

53 Ku ne kuwa kuka karɓi Koyarwar ta wurin malaˈiku, amma ba ku kiyaye ta ba!”

54 Da suka ji haka, suka yi fushi sosai, har suka ciji baki don haushi.

55 Amma Istifanus cike da Ruhu Mai Tsarki, ya zuba ido yana kallon sama, ya ga ɗaukakar Allah, da kuma Yesu a tsaye a hannun dama na Allah.

56 Sai Istifanus ya ce, “Duba, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗan Mutum a tsaye a hannun dama na Allah.”

57 Amma suka fara ihu sosai, suka tottoshe kunnuwansu, suka hau masa gaba ɗaya.

58 Suka fitar da shi bayan gari, suka yi ta jifarsa da duwatsu. Shaidu kuwa suka ajiye tufafinsu wurin wani saurayi mai suna Shawulu.

59 Suna ta jifar Istifanus, shi kuwa ya yi adduˈa ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi raina.”

60 Sai ya durƙusa, ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ubangiji, kada ka lissafta wannan zunubi a kansu.” Da faɗin haka, sai ya yi barci.

Open Bible reader