Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 19

1 A lokacin da Afollos yake a Korinti, Bulus ya zazzaga cikin ƙasar har ya kai Afisa, inda ya tarar da waɗansu almajirai.

2 Sai ya ce musu, “Kun karɓi Ruhu Mai Tsarki lokacin da kuka ba da gaskiya?” Suka ce masa, “Ba mu ma san akwai Ruhu Mai Tsarki ba.”

3 Sai ya ce, “Zuwa cikin me aka yi muku baftisma?” Suka ce, “Zuwa cikin baftisma ta Yohanna ce.”

4 Bulus ya ce, “Ai, Yohanna ya yi baftisma domin a tuba ne, yana faɗa wa mutane su gaskata da wanda zai zo bayansa, wato Yesu.”

5 Da suka ji haka, sai aka yi musu baftisma cikin sunan Ubangiji Yesu.

6 Da Bulus ya sa musu hannun albarka, Ruhu Mai Tsarki kuwa ya sauko musu, suka kuwa yi magana da waɗansu harsuna, suna annabci.

7 Su wajen mutum goma sha biyu ne duka.

8 Sai Bulus ya shiga majamiˈa yana waˈazi babu tsoro, ya kuma yi wata uku yana kawo musu dalilai, yana rinjayarsu a kan shaˈanin mulkin Allah.

9 Amma waɗansunsu suka nuna taurin kai suka ƙi su gaskata, har suka yi wa wannan Hanyar Ubangiji baƙar magana a gaban jamaˈa. Domin haka Bulus ya rabu da su, ya tafi da masu bi, yana ta koyarwa kowace rana a makarantar Tiranus.

10 Haka ya yi ta yi har shekara biyu, har dukan masu zama a ƙasar Asiya suka ji kalmar Ubangiji, Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba duka.

11 Ta hannun Bulus kuma Allah ya yi waɗansu manyan ayyukan ban mamakin da ba a saba gani ba,

12 yadda har ma idan aka ɗauki hankici nasa ko rigar da ta taɓa jikinsa, aka kai wa waɗanda ba su da lafiya, sai su warke, mugayen ruhohi kuma su rabu da su.

13 Sai waɗansu Yahudawa masu yawo gari-gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan masu mugayen ruhohi. Suna cewa, “Na umarce ku da sunan Yesun nan da Bulus yake waˈazinsa.”

14 A cikinsu akwai waɗansu ˈyaˈya bakwai maza, na wani babban firist na Yahudawa, mai suna Sikeba, dukansu suna yin haka.

15 Amma mugun ruhun ya amsa musu ya ce, “Yesu dai na san shi, na kuma san Bulus, to, ku kuma ku wane ne?”

16 Sai mutumin nan mai mugun ruhu ya yi tsalle, ya hau musu, ya sha ƙarfinsu dukansu, har suka fita daga gidan a guje tsirara, da jikinsu duk rauni.

17 Da dukan masu zama a Afisa, Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba, suka ji labarin wannan abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuwa ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu.

18 Da yawa kuma da suka ba da gaskiya suka zo suna faɗin mugayen ayyukansu a fili.

19 Mutane da yawa kuwa masu yin sihiri, suka tattaro littattafansu suka ƙone su a gaban jamaˈa duka. Da suka yi lissafin kuɗin littattafan, sai suka ga ya kai azurfa dubu hamsin.

20 Ta haka kalmar Ubangiji ta ƙara bazuwa, ta kuma yi ƙarfi sosai.

21 Bayan waɗannan abubuwa, Bulus ya shirya a ransa cewa idan ya zazzaga ƙasar Makidoniya da ta Akaya, zai je Urushalima. Ya kuma ce, “Bayan da na tafi can kuwa dole ne in je in ga birnin Roma.”

22 Bayan da ya aika da masu taimakonsa biyu, wato Timoti da Erastus, zuwa Makidoniya, shi kuwa ya ɗan tsaya a ƙasar Asiya.

23 A lokacin nan aka yi wani babban tashin hankali game da wannan Hanya.

24 Wannan tashin hankali ya fara da wani maƙeri mai suna Dimitiriyus wanda yake amfani da azurfa yana ƙera siffar haikalin Artemis. Shi da maˈaikatansa suna samun kuɗi ta wannan sanaˈarsu ba kaɗan ba.

25 Sai ya tara su da duk masu yin irin wannan aiki, ya ce, “Ku jamaˈa, kun sani fa da sanaˈar nan muke yin arziki.

26 Kuma kuna ji kuna gani, ba a nan Afisa kaɗai ba, kusan duk ƙasar Asiya ma, Bulus ɗin nan ya rinjayi mutane da yawa sosai. Ya juyar da su, yana cewa allolin da aka yi da hannu ba alloli ba ne.

27 To, akwai hatsari fa. Za a ɓata sunan aikinmu. Ban da haka ma, har da haikalin babban alliya Artemis za a mai da shi banza, har kuma a raba alliyar da darajarta, ita wadda duk ƙasar Asiya, kai, har ma dukan duniya take bauta mata.”

28 Da suka ji haka, sai suka cika da fushi sosai, suka ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa, “Girma ya tabbata ga Artemis ta Afisawa!”

29 Sai garin duk ya ruɗe, jamaˈa suka ruga zuwa filin taro, suka kama Gayus da Aristarkus, mutanen Makidoniya, waɗanda suke abokan tafiyar Bulus.

30 Bulus ya so yă shiga taron nan, amma masu bi suka hana shi.

31 Waɗansu manyan hakimai na ƙasar Asiya, waɗanda suke abokansa, su ma suka aika masa, suka roƙe shi kada yă kuskura yă shiga wajen taron nan.

32 Mutanen da suka taru kuwa duk ma a rikice suke, gama ba su ma san abin da ya sa suka taru ba. Waɗansu suna tā da murya suna faɗin wannan abu, waɗansu kuma suna faɗin wancan.

33 Waɗansu Yahudawa suka tura wani mai suna Alekzanda gaba, shi kuwa ya ɗaga hannu a yi shiru domin yă yi musu bayani.

34 Amma da suka gane cewa shi Bayahude ne, suka ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa, “Girma ya tabbata ga Artemis ta Afisawa!” Sun yi haka har wajen awa biyu.

35 A ƙarshe, da marubucin garin ya sa suka yi shiru, sai ya ce, “Ku mutanen Afisa! Ai, kowa ya san cewa birnin Afisa ne take kula da haikalin mai girma Artemis, da kuma dutse mai tsarkin nan da ya fāɗo daga sama.

36 To, tun da yake ba dama a yi musūn waɗannan abubuwa, ai, ya kamata ku natsu, kada ku yi kome da garaje.

37 Ga shi kuwa mutanen nan da kuka kawo a nan, ba su yi sata a haikalin alliyarmu Artemis ba, ba su kuma yi mata maganar saɓo ba.

38 Amma idan Dimitiriyus da abokan sanaˈarsa suna da wata damuwa game da wani, ai, ga ɗakin shariˈa a buɗe, ga kuma masu shariˈa, sai su kai ƙara.

39 Amma idan akwai wani abu dabam da kuke so ku sani, ai, sai a daidaita a majalisa.

40 Hakika muna cikin hatsarin amsar ƙara a kan tawayen yau, tun da yake ba za mu iya ba da dalilin da ya sa wani tashin hankali ya faru ba.”

41 Da ya faɗa haka sai ya sallami taron.

Open Bible reader