Skip to content

Hausa Bible

Matiyu 21

1 Saˈad da Yesu da almajiransa suka kai ƙauyen Betafaji kusa da Urushalima, wajen Tudun Itatuwan Zaitun, sai ya aiki almajirai biyu,

2 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen nan na gabanku. Da shigarku za ku ga wata jaka a ɗaure tare da ɗanta. Ku kunce su ku kawo mini.

3 Idan wani ya yi muku magana ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsu.’ Zai kuwa mai da su an jima.”

4 Wannan ya faru ne domin a cika abin da annabi ya faɗa cewa,

5 “Ku ce wa zuciyata Urushalima, ‘Ga sarkinku nan zuwa gare ku! Mai sauƙin kai ne shi. Yana tafiya a kan jaki, a kan ɗan jaki ne yake tafiya.’ ”

6 Sai almajiran suka je, suka yi yadda Yesu ya ce su yi.

7 Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa musu rigunansu, shi kuwa ya hau ya zauna.

8 Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunansu a kan hanya, waɗansu kuma suka karya ganye daga itatuwa suka shimfiɗa a kan hanya.

9 Mutanen da suke gabansa da waɗanda suke binsa a baya suka ɗaga murya suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin Sunan Ubangiji! Hosanna ga Mafi Ɗaukaka!”

10 Da Yesu ya shiga Urushalima, duk birnin ya ruɗe, ana ta tambaya ana cewa, “Wane ne wannan?”

11 Sai mutanen da suke bin Yesu suka ce, “Ai, wannan shi ne annabi Yesu daga Nazaret na Galili.”

12 Sai Yesu ya shiga Haikali ya kori dukan masu saya da sayarwa a ciki, ya tutture teburan masu canjin kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru.

13 Ya ce musu, “A rubuce yake, “ ‘Za a ce da gidana gidan adduˈa,’ amma kun mai da shi wurin ɓuyan ˈyan fashi.”

14 Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Haikalin, ya kuwa warkar da su.

15 Amma da manyan firistoci da malaman Koyarwar Musa suka ga ayyukan ban mamaki da ya yi, har yara suna ihu cikin Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji fushi.

16 Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke cewa kuwa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, ashe, ba ku taɓa karanta cikin Rubutacciyar Maganar Allah ba cewa, “ ‘Daga bakin yara da jarirai ka sa yabonka yă fita?’ ”

17 Daga nan sai ya bar su ya fita daga birnin, ya tafi Betani, ya kwana a can.

18 Da gari ya waye yana dawowa, sai yunwa ta kama shi.

19 Da ya ga wani itacen ɓaure a gefen hanya, sai ya je wurin itacen, amma bai sami kome ba sai ganye. Ya ce wa itacen, “Kada ka ƙara yin ˈyaˈya har abada.” Nan take kuwa itacen ya bushe.

20 Da almajiran suka ga haka, suka yi mamaki sosai. Suka ce, “Yaya itacen ya bushe haka nan take?”

21 Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika ina gaya muku, idan kuna da bangaskiya, kuma ba ku yi shakka ba ko kaɗan, za ku iya yin fiye da abin da na yi wa wannan ɓaure, har ma idan kuka ce wa babban tudun nan, ‘Tashi ka fāɗa cikin teku,’ zai faru.

22 Idan kun ba da gaskiya, duk iyakar abin da kuka roƙi Allah cikin adduˈa, za ku samu.”

23 Saˈad da Yesu ya shiga Haikali, yana cikin koyarwa ke nan, sai manyan firistoci da shugabannin jamaˈa suka zo wurinsa suka ce, “Da wane izni kake yin abubuwan nan, kuma wa ya ba ka wannan izni?”

24 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Idan kun ba ni amsa, ni ma zan faɗa muku ko da wane iko nake yin abubuwan nan.

25 Daga ina ne Yohanna ya sami iznin baftismar da ya yi, Allah ne ya ba shi ko mutum?” Sai suka fara gardama a tsakaninsu suna cewa, “Idan muka ce daga wurin Allah ne, zai ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

26 Amma idan muka ce, ‘Daga wurin mutum ne’, muna jin tsoron abin da mutane za su yi mana, gama kowa ya ɗauki Yohanna annabi ne.”

27 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Sai ya ce musu, “Ni ma ba zan faɗa muku ko da wane izni nake yin abubuwan nan ba.”

28 “To, me kuka gani? Akwai wani mutum yana da ˈyaˈya biyu maza, ya je wurin na farkon ya ce, ‘Ɗana, yau ka je ka yi aiki a gonar inabi.’

29 Sai ɗan ya ce, ‘Ba zan je ba,’ amma daga baya ya sāke tunani ya je.

30 Sai baban ya je wurin na biyun, ya faɗa masa abin da ya faɗa wa na farkon. Sai ɗan ya amsa ya ce, ‘To, zan je, baba,’ amma bai je ba.

31 Cikinsu biyun nan, wane ne ya yi abin da babansa yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu kuwa ya ce musu, “Hakika ina gaya muku masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin sama.

32 Gama Yohanna ya zo ya nuna muku hanyar adalci, ba ku ba da gaskiya ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun ba da gaskiya gare shi. Duk da ganin haka ma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”

33 “To, ga wani misali kuma. Akwai wani mutumin da ya yi gonar inabi, ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsewar ˈyaˈyan inabi a ciki, ya kuma gina rumfar maigadi. Ya ba waɗansu manoma hayar gonar, saˈan nan ya tafi wata ƙasa.

34 Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki bayinsa su je wurin waɗanda suka karɓi hayar gonar su karɓo masa nasa rabon amfanin gonar.

35 Amma masu hayar suka kama bayin, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jejjefi ɗaya.

36 Sai ya sāke aika waɗansu bayi fiye da na farko. Masu hayar gonar suka yi musu yadda suka yi wa na farkon.

37 Daga ƙarshe sai mai gonar ya aiki ɗansa zuwa wurinsu yana cewa, ‘Ba shakka za su ba ɗana girma.’

38 Amma da masu hayar suka ga ɗan, sai suka ce wa junansu, ‘Yawwa! Ai, wannan shi ne zai gāji gonar. Mu kashe shi, gādonsa yă zama namu!’

39 Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan katangar gonar, suka kashe shi.

40 “To, idan mai gonar nan ya zo, me zai yi wa masu hayar nan?”

41 Sai suka ce masa, “Ai, lallai zai kakkashe mugayen nan, ya ba waɗansu hayar gonar, waɗanda za su dinga ba shi nasa rabon amfanin gonar.”

42 Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Rubutacciyar Maganar Allah ba? Cewa, “ ‘Dutsen da masu gini suka ƙi, shi ne ya zama dutse mafi amfani a gini. Wannan aikin Ubangiji ne, abin mamaki ne kuwa a idanunmu.’ ”

43 “Saboda haka ina gaya muku, za a karɓi mulkin Allah daga wurinku, a ba wata alˈummar da za ta haifar da halaye masu kyau na mulkin.

44 Wanda ya fāɗi a kan wannan dutse zai halaka, kuma wanda dutsen nan ya fāɗi masa, zai niƙa shi kamar gari.”

45 Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan nan da ya bayar, sai suka gane cewa yana magana a kansu ne.

46 Sun so su kama shi, amma suna tsoron jamaˈa, gama jamaˈa sun ɗauka shi annabi ne.

Open Bible reader