Skip to content

Hausa Bible

Luka 12

1 Ana nan sai dubban mutane suka tattaru har suna tattaka juna, sai Yesu ya yi wa almajiransa magana da farko ya ce, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato munafuncinsu.

2 Ba abin da yake a rufe da ba za a bayyana ba, kuma ba abin da yake a ɓoye wanda ba za a sani ba.

3 Saboda haka, duk abin da kuka faɗa a ɓoye, za a ji shi a fili. Abin da kuka kuma faɗa a asirce, ko a cikin ɗakin da kuka rufe ƙofofinsa ma, za a yi shelarsa a kan rufin ɗakuna.

4 “Ku abokaina, ina gaya muku, kada ku ji tsoron masu kisan jiki amma bayan da suka kashe shi ba abin da za su iya yi kuma.

5 Zan faɗa muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron Allah, wanda bayan da ya kashe, yana da iko yă jefa a cikin gidan wuta kuma. Hakika ina gaya muku, shi ne wanda za ku ji tsoronsa!

6 “Ba akan sayar da ˈyan tsuntsu biyar kobo biyu ba? Duk da haka Allah bai manta da ko ɗayansu ba.

7 Kai! Har gashin kanku ma an ƙirga su duka. Saboda haka, kada ma ku ji tsoro, don kun fi ɗan tsuntsu daraja sau barkatai!”

8 “Ina kuma faɗa muku, duk wanda ya shaida a gaban mutane cewa ya yarda da ni, Ɗan Mutum ma zai shaida ya yarda da shi a gaban malaˈikun Allah.

9 Wanda kuma ya yi musūn sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musūn saninsa a gaban malaˈikun Allah.

10 “Duk wanda ya yi maganar saɓo game da Ɗan Mutum, za a yafe masa, amma duk wanda ya yi maganar saɓo game da Ruhu Mai Tsarki, ba za a yafe masa ba.

11 “Idan kuma an kawo ku a gaban majamiˈu, ko gaban masu hukunci, ko kuma gaban shugabanni, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku ce,

12 domin Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya kamata ku faɗa a lokacin.”

13 Sai wani mutum daga cikin jamaˈa ya ce wa Yesu, “Malam, ka ce wa ɗanˈuwana yă ba ni rabona na gādon da babanmu ya mutu ya bar mana.”

14 Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai! Wa ya mai da ni alƙali ko in zama mai raba muku kayan da babanku ya mutu ya bar muku?”

15 Ya ci gaba da yi wa mutane magana, ya ce musu, “Ku lura fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne samun rai ba.”

16 Sai ya ba su wani misali ya ce, “An taɓa yin wani mai arziki wanda gonarsa ta yi amfani sosai.

17 Ya fara tunani a ransa, ya ce, ‘Ba ni da inda zan sa amfanin gonata duka. Me zan yi ke nan?’

18 “Ya ce wa kansa, ‘Yawwa! Na san abin da zan yi. Zan rushe waɗannan rumbunana, in gina waɗansu manya, in zuba dukan amfanin gonata da kayana a ciki.

19 Zan kuma ce wa raina, “Haba! Kana da kaya masu yawa wanda za ka mora a shekaru masu yawa. Bari ka huta, ka yi ta ci, ka yi ta sha, kana jin daɗinka.” ’

20 Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za ka mutu. Saˈan nan in ga ko wane ne zai ci duk kayan nan da ka tara wa kanka.’ ”

21 Yesu ya gama maganar nan da cewa, “Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa kaya, amma a gaban Allah ba shi da arziki.”

22 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Domin haka ina gaya muku, kada ku damu da yadda za ku rayu, ko kuma yadda za ku sami riguna don jikinku.

23 Domin rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi riguna.

24 Ku dubi tsuntsaye mana! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da ɗakunan ajiyar abinci ko rumbuna, amma duk da haka Allah yana ba su abinci. Darajarku kuwa ta fi ta tsuntsaye sau barkatai!

25 Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa, zai iya ƙara ko awa ɗaya ga kwanakin rayuwarsa?

26 To, idan ba za ku iya yin ƙanƙanin abu irin wannan ba, don me kuke damuwa a kan sauran?

27 Ku dubi yadda su fulawa suke girma mana. Ba sa aiki, ba sa saƙar kome, ba sa yi wa kansu riguna, duk da haka ina gaya muku ko Sarki Solomon da dukan girmansa bai taɓa yin ado kamar ɗaya daga cikinsu ba.

28 To, idan har Allah zai yi wa ciyawar daji ado haka, ciyawa waɗanda suke nan yau, gobe kuwa a ƙone su, balle ku? Ya ku masu ƙanƙantar bangaskiya!

29 “Kada ku dinga tunani a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ma ku damu.

30 Ai, mutanen duniya waɗanda ba su san Allah ba suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa. Ku kuwa, Ubanku ya san kuna bukatarsu.

31 Ku dai ku sa ranku ga mulkin Allah, za a ba ku dukan waɗannan abubuwa kuma.

32 “Ya ku ƙaramin garkena, kada ku ji tsoro, gama Ubanku yana jin daɗi yă ba ku mulkinsa.

33 Ku sayar da dukan abin da kuke da shi, ku ba talakawa sadaka. Ku yi wa kanku ajiyar da ba za ta tsufa ba, wato dukiyar da ba za ta lalace ba ke nan a sama, inda ba ɓarawon da zai sace su, ba kuma garar da za ta lalatar da su.

34 Gama inda dukiyar mutum take, a nan ne zuciyarsa ma take.

35 “Ku zauna a shirye, fitilunku a kunne.

36 Ku zama kamar bayin da suke jiran maigidansu yă dawo daga bikin aure. Da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, nan da nan sai su buɗe masa.

37 Zai zama abin farin ciki ga bayin nan in har maigidan ya dawo ya same su ba su yi barci ba. Hakika ina gaya muku, zai cire babbar rigar da ya sa, yă ce musu su zazzauna, su ci abinci, saˈan nan yă bi kan kowane ɗayansu yă kawo masa abinci.

38 Bayin nan masu albarka ne in ya dawo ko da tsakar dare, ko kuma da sassafe, ya same su a shirye.

39 Ku dai sani cewa in maigida ya san lokacin da ɓarawo zai zo masa, ba zai bar shi yă shiga yă yi masa ɓarna a gida ba.

40 Sai ku zauna da shiri, domin Ɗan Mutum zai zo a lokacin da ba ku yi tsammani zai zo ba.”

41 Bitrus ya ce, “Ubangiji, wannan misali a kanmu aka yi ko kuwa ya shafi kowa?”

42 Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Wane ne bawan nan mai aminci mai hikima kuma, wanda maigidansa zai sa shi yă lura da gidansa, yă kuma ba sauran bayi abinci a daidai lokaci?

43 Mai albarka ne bawan da maigidansa zai zo yă same shi yana yin aikinsa.

44 Hakika ina gaya muku, zai sa wannan bawa yă lura masa da kayansa duka.

45 Amma idan bawan nan ya ce a ransa, ‘Ai, maigidana ya yi lattin zuwa,’ saˈan nan ya fara dūkan sauran bayin, maza da mata, ya kuma shiga ci da sha, har yana buguwa,

46 maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bawan bai yi tsammani ba, kuma a lokacin da bai sani ba. Maigidan nan zai yi masa mugun dūka yă kuma hukunta shi tare da marasa aminci.

47 “Bawan da ya san abin da maigidansa yake so yă yi, amma bai yi shiri ba, bai kuma yi abin da ake so yă yi ba, za a yi masa bulala sosai.

48 Wanda kuwa bai san abin da maigidansa yake so yă yi ba, ya kuma yi abin da ya isa a dūke shi, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi abu mai yawa, za a nemi abu mai yawa daga gare shi. Wanda kuma aka ba shi abu mai yawa sosai, za a nemi abu mai yawa sosai daga gare shi.

49 “Wuta ce na zo in sa wa duniya. Da sona ne, da an kunna ta ko!

50 Ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa matsu a zuciya sosai har sai an yi mini ita!

51 Kuna tsammani zaman lafiya ne na kawo wa duniya? A ina! Ina gaya muku, rabuwa ce na kawo.

52 Daga yanzu, a gida ɗaya, mutum biyar za su rabu kashi biyu, uku suna gāba da biyu, biyu kuma suna gāba da uku.

53 Baba zai yi gāba da ɗansa, ɗan kuma yă yi gāba da babansa. Mama za ta yi gāba da ˈyarta, ˈyar kuma ta yi gāba da mamarta. Mamar miji za ta yi gāba da matar ɗanta, matar ɗan kuma ta yi gāba da mamar mijinta.”

54 Yesu ya kuma ce wa mutane, “In kun ga hadari ya taso daga yamma, kukan ce ai, za a yi ruwan sama, sai kuwa a yi.

55 Idan kuma kun ji iska tana hurawa daga kudu, sai ku ce za a yi zafi, sai kuma a yi.

56 Munafukai! Kun iya gane yanayin ƙasa da na sararin sama, amma ganewar alamun zamanin nan ya gagare ku.

57 “Me ya sa ku kanku ba ku iya tunani ku gane abin da ya fi kyau ku yi?

58 Idan wani ya kai ƙararka a kotu, ka yi ƙoƙari ku shirya tun kuna a kan hanya. In ka ƙi, zai kai ka gaban alƙali. Alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan doka. Ɗan doka kuma yă sa ka a kurkuku.

59 Ina gaya maka, ba za ka fita a wurin ba sai ka biya dukan abin da aka yanka maka, ba ko sauran kobo.”

Open Bible reader