Skip to content

Hausa Bible

Luka 11

1 Wata rana Yesu yana adduˈa a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yadda za mu yi adduˈa, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa mana.”

2 Yesu ya ce musu, “In za ku yi adduˈa, ku ce, “ ‘Ya Uba, a kiyaye sunanka da tsarki, mulkinka yă zo.

3 Ka ba mu abinci na yau da na kowace rana.

4 Ka gafarta mana zunubanmu, gama mu ma muna gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi. Kada ka kai mu cikin jarraba.’ ”

5 Yesu ya sāke ce wa almajiransa, “A ce ɗayanku yana da aboki, ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, ‘Aboki, ka ba ni bashin burodi guda uku mana.

6 Ga shi wani abokina wanda ya fito tafiya ya sauka a wurina yanzu-yanzun nan. Kuma ba ni da abincin da zan ba shi.’

7 Saˈan nan a ce abokin nan da an je neman bashi a wurinsa yă amsa daga cikin ɗaki yă ce, ‘Kada ka dame ni! Ai, na riga na kulle ƙofa, da ni da yarana duk mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka wani abu ba.’

8 Ina gaya muku, ko da ba zai tashi yă ba shi wani abu don shi abokinsa ba ne, zai tashi yă ba shi ko nawa yake so domin abokin bai ji kunya yă yi ta roƙo ba.

9 “Ina dai gaya muku, ku yi ta roƙo za a ba ku. Ku yi ta nema za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a buɗe muku.

10 Gama duk wanda ya roƙa, za a ba shi, duk wanda ya nema zai samu, kuma duk wanda ya ƙwanƙwasa za a buɗe masa.

11 Akwai wani a cikinku wanda in yaronsa ya roƙe shi kifi sai yă ba shi maciji?

12 Ko kuwa yaron yă roƙi ƙwai sai a ba shi kunama?

13 Idan ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba ˈyaˈyanku abubuwa masu kyau, balle Ubanku na sama, zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.”

14 Ana nan Yesu yana fitar da beben aljani daga wani mutum. Da aljanin ya fita, sai mutumin ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.

15 Amma waɗansu mutane suka ce, “Ahab! Ai, Baˈalzabul, sarkin aljanu ne ya ba shi wannan iko na fitar da aljanu.”

16 Waɗansu suna so su gwada Yesu, sai suka ce masa yă yi wata babbar alamar da za ta bayyana ikonsa.

17 Amma Yesu ya gane tunanin da suke ciki, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu kashi biyu suna gāba da juna, mulkin ba zai tsaya ba. Haka ma in gida ya rabu kashi biyu, suna gāba da juna, zai rushe.

18 In kuma Shaiɗan ya rabu kashi biyu yana gāba da kansa, yaya mulkinsa zai yi ƙarfi? Kun ce da ikon Baˈalzabul nake fitar da aljanu.

19 Idan da ikon Baˈalzabul nake fitar da aljanu, to, almajiranku fa? Da ikon wa suke fitarwa? Almajiranku ne za su yi muku shariˈa a kan wannan.

20 Amma, idan da ikon Allah nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan.

21 “Idan mutum mai ƙarfi ya yi shiri sosai, yana gadin gidansa, kayan gidansa za su zauna lafiya lau.

22 Amma idan wanda ya fi shi ƙarfi ya zo ya hau shi da faɗa ya kuma sha ƙarfinsa, sai yă ƙwace duk makaman da mutumin ya dogara da su, yă kuma rarraba kayayyakin da ya ƙwace a yaƙi.

23 “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ke nan. Wanda bai taimake ni tarawa ba kuwa, yana watsarwa ne.”

24 “Idan ƙazamin ruhu ya fita daga jikin mutum, yakan yi ta yawo a wuraren da ba ruwa, domin yă sami wurin hutawa. Idan bai samu ba, sai yă ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’

25 Idan ya zo ya samu an share, an kuma gyara gidan,

26 sai yă koma yă kwaso waɗansu ƙazaman ruhohi bakwai waɗanda suka fi shi mugunta, su zo su zauna a wurin. A ƙarshe, zaman mutumin nan zai fi na farkon muni.”

27 Da Yesu ya faɗa haka, sai wata mace daga cikin jamaˈa ta ɗaga murya ta ce masa, “Allah yă albarkaci matar da ta haife ka, ta kuma goye ka har ka yi girma!”

28 Yesu ya amsa ya ce, “I, amma albarka ta fi tabbata ga waɗanda suke jin kalmar Allah, suke kuma kiyaye ta!”

29 Saˈad da mutane suka dinga ƙaruwa wurin Yesu, sai ya fara cewa, “Wannan zamani mugun zamani ne. Suna nema a nuna musu wata alama, amma babu wata alamar da za a nuna musu sai dai ta Yona.

30 Kamar yadda Yona ya zama alama ga mutanen Nineba, haka ma Ɗan Mutum zai zama ga mutanen zamanin nan.

31 A Ranar Shariˈa, Sarauniyar Sheba za ta tashi tare da mutanen zamanin nan ta nuna musu ba su yi daidai ba, gama ta zo ne daga wuri mai nisa sosai don ta ji koyarwar hikimar Solomon. Amma ga wanda ya fi Solomon a nan.

32 A Ranar Shariˈa, mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su nuna musu ba su yi daidai ba, domin su sun tuba saboda waˈazin Yona. Ga shi kuwa wanda ya fi Yona a nan!

33 “Ba wanda zai kunna fitila saˈan nan yă ɓoye ta, ko kuma yă rufe ta da kwano. Aˈa, sai dai yă ajiye ta a kan sanda mai riƙe fitilu, inda kowa da ya shiga zai ga hasken.

34 Ido shi ne fitilar jiki. In idonka yana da lafiya, dukan jikinka zai cika da haske. Amma idan idonka ba lafiya, sai dukan jikinka yă rasa haske.

35 Ka lura fa, ko hasken da kake da shi duhu ne.

36 In dukan jikinka yana da haske, ba inda yake da duhu, ai, duk sai yă haskaka gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila yake ba ka haske.”

37 Da Yesu ya gama magana, sai wani Bafarisiye ya gayyaci Yesu gidansa su ci abinci. Sai Yesu ya je ya zauna don cin abinci.

38 Da Bafarisiyen ya ga cewa Yesu bai wanke hannu kafin yă fara cin abincin ba, sai mamaki ya kama shi.

39 Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa kukan wanke bayan kwaf da kuma ƙwarya, amma a cikinku kuna cike da cuce-cuce da mugunta.

40 Wawaye kawai! Ashe, ba Allahn da ya yi wajen ne ya yi cikin ma ba?

41 Amma da za ku yi sadaka da abubuwan da suke a ciki, da kome zai zama marar ƙazanta a gare ku.

42 “Kaitonku, Farisiyawa! Kuna ba Allah zakkar kayan yaji na ganye da kuma sauran ganyen miya duka. Amma kun ƙi kula da aikata gaskiya da ƙaunar Allah. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da kun ƙyale sauran ba.

43 “Kaitonku, Farisiyawa! Kun cika so a ba ku wuraren zama masu daraja a majamiˈu, a kuma dinga gaishe ku a kasuwa.

44 Kaitonku! Kun yi kama da kaburburan da ba a gani, waɗanda mutane suke tafiya a kai don rashin sani.”

45 Sai ɗaya daga cikin malaman Koyarwar Musa ya ce wa Yesu, “Malam, in ka faɗa haka, ai, mu ma, ka zage mu!”

46 Yesu ya amsa, ya ce, “Kaitonku, ku ma malaman Koyarwar Musa! Kun jibga wa mutane kaya wato, dokoki masu nauyi su ɗauka, amma ku kanku ba ku taɓa kayan ko da yatsa ɗaya, domin ku taimake su ba.

47 Kaitonku! Kun gina kaburbura masu kyau wa annabawan Allah waɗanda kakanninku suka kashe.

48 Wato ku da kanku kun shaida kun kuma yarda da yadda kakanninku suka yi. Sun kashe annabawan, ku kuma kuka gina kaburburan.

49 Shi ya sa Hikimar Allah ta ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’

50 Saboda haka za a hukunta mutanen zamanin nan saboda kashe-kashen da aka yi wa dukan annabawa tun kafawar duniya,

51 wato, tun daga jinin Habila, har zuwa na Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagaden hadaya da Wuri Mai Tsarki cikin Haikali. I, ina gaya muku, za a hukunta mutanen zamanin nan saboda waɗannan duka!

52 “Kaitonku malaman Koyarwar Musa! Kun riƙe mabuɗin gidan ilimi, ku kanku ba ku shiga ba, ba ku kuma bar masu son shiga su shiga ba.”

53 Da Yesu ya bar wurin, sai malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa suka fara matsa masa, suna tsokanarsa da tambayoyi a kan abubuwa da yawa,

54 suna ƙoƙari su sa masa tarko domin yă faɗa wani abin da ba daidai ba.

Open Bible reader