Hausa Bible
Yahaya 4
1 Ana nan sai Farisiyawa suka ji labari cewa Yesu yana samun almajirai, yana kuma yi musu baftisma fiye da Yohanna.
2 Amma dai ba Yesu ne da kansa yake yin baftismar ba, almajiransa ne.
3 Da Yesu ya sami labari game da wannan sai ya bar Yahudiya, ya koma Galili.
4 Ya zama dole ne Yesu ya bi ta cikin Samariya.
5 Sai ya zo wani gari a cikin Samariya mai suna Saikar. Garin yana kusa da yankin ƙasar da Yakub ya ba ɗansa Yusuf tun dā.
6 A wannan wuri ne rijiyar Yakub take. Da Yesu ya gaji da tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wannan ya faru wajen tsakar rana ne.
7 Sai ga wata mace ˈyar Samariya ta zo ɗiban ruwa. Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha.”
8 Almajiransa kuwa sun shiga cikin gari domin sayen abinci.
9 Sai macen nan Basamariya ta ce wa Yesu, “Yaya kai Bayahude za ka roƙe ni ruwan sha, ni da nake mace daga Samariya?” Gama Yahudawa ba sa haɗa ido da Samariyawa.
10 Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda yake ce miki, ‘Ba ni ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwa mai ba da rai.”
11 Sai macen ta ce wa Yesu, “Maigirma, ai, ba ka da guga, rijiyar kuwa da zurfi. To, a ina ne za ka sami wannan ruwa mai ba da rai?
12 Ko ka fi ubanmu Yakub ne, wanda ya bar mana rijiyar, har shi da kansa, da ˈyaˈyansa, da dabbobinsa, suka sha ruwa daga ciki?”
13 Yesu ya amsa ya ce, “Duk wanda ya sha wannan ruwa zai sāke jin ƙishi.
14 Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishi ba har abada. Ruwan da zan ba shi zai zama masa maɓuɓɓugar ruwa wadda take ɓulɓullowa zuwa ga rai na har abada.”
15 Sai macen ta ce masa, “Maigirma, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishi, domin kada kuma in dinga zuwa nan domin ɗiban ruwa.”
16 Sai Yesu ya ce mata, “Ki je ki kira mijinki ku zo nan.”
17 Sai ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Yesu ya ce mata, “Kin faɗa gaskiya da kika ce ba ki da miji.
18 Don ainihin gaskiyar kuwa shi ne, kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne.”
19 Sai macen ta ce wa Yesu, “Maigirma, ina gani kai annabi ne.
20 Kakanninmu sun yi wa Allah sujada a babban tudun nan. Amma ku Yahudawa kun ce a Urushalima ne ya kamata a yi wa Allah sujada.”
21 Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Uwargida, ki ba da gaskiya ga abin da nake faɗi, gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su yi wa Uba sujada a babban tudun nan, ko a Urushalima ba.
22 Ku mutanen Samariya kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada. Amma mu Yahudawa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto ya fito daga Yahudawa ne.
23 Amma lokaci yana zuwa, har ma ya riga ya zo, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada cikin ruhu, da kuma gaskiya, gama Uba yana neman irin waɗannan ne su yi masa sujada.
24 Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuma sai su yi masa sujada cikin ruhu, da cikin gaskiya kuma.”
25 Sai macen ta ce wa Yesu, “Na sani Almasihu wanda ake ce da shi Kiristi yana zuwa. Idan ya zo zai bayyana mana dukan kome.”
26 Yesu ya ce mata, “Ni mai magana da ke, ni ne shi.”
27 Suna gama magana ke nan sai ga almajiransa suka dawo, suka kuwa yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma babu wanda ya ce mata, “Me kike bukata?” ko kuma yă tambaye shi, “Me ya sa kake magana da ita?”
28 Sai macen nan ta bar tulunta a wurin ta je cikin gari ta ce wa mutane,
29 “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Ko ya yiwu wannan shi ne Almasihun?”
30 Sai mutane suka fiffito daga cikin gari suka zo wurin Yesu.
31 Ana cikin wannan ke nan, sai almajiran Yesu suka roƙe shi suka ce, “Malam, ka ci abinci.”
32 Amma Yesu ya ce musu, “Ina da wani abincin da ba ku san kome a kai ba.”
33 Sai almajiransa suka tambayi juna suka ce, “Ko wani ya kawo masa abinci ne?”
34 Amma Yesu ya ce, “Abincina shi ne in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.
35 Ba kuna cewa sauran watanni huɗu a yi girbi ba? Amma ina gaya muku fa, ku dubi gonaki da kyau, sun nuna, sun kuma isa girbi.
36 Mai girbi yana samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai na har abada, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.
37 A nan kam, karin maganar nan gaskiya ne, cewa, ‘Wani ya yi shuka, wani ya yi girbi.’
38 Na aike ku girbin abin da ba ku yi wahalarsa ba. Waɗansu sun yi wahala, ku kuwa kun mori ribar wahalarsu.”
39 Mutanen Samariya da yawa daga wannan gari suka ba da gaskiya ga Yesu saboda maganar matan nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.”
40 Da mutanen Samariya suka zo wurin Yesu, sai suka roƙe shi yă zauna tare da su, sai ya kuwa zauna kwana biyu.
41 Mutane da yawa kuma suka ba da gaskiya ga Yesu saboda maganarsa.
42 Saˈan nan mutanen Samariya suka ce wa macen, “Yanzu kam, mun ba da gaskiya, ba don ma abin da kika faɗa kawai ba, amma saboda mu ma mun ji da kanmu, mun kuma tabbata lallai wannan mutum ne Mai Ceton duniya.”
43 Bayan kwana biyun nan sai Yesu ya tashi daga yankin Samariya zuwa Galili.
44 Gama Yesu da kansa ya taɓa faɗa cewa, “Annabi ba shi da daraja a ƙasarsa”.
45 Da ya kai Galili, sai mutanen Galili suka karɓe shi hannu biyu-biyu domin su ma sun je Bikin Ƙetarewa a Urushalima, suka kuma ga duk abin da Yesu ya yi.
46 Sai Yesu ya sāke koma garin Kana ta Galili, wato inda ya mai da ruwa ya zama ruwan inabi. A wurin kuwa akwai wani maˈaikacin hukuma wanda yaronsa a Kafarnahum ba shi da lafiya.
47 Da wannan mutumin ya ji cewa Yesu ya dawo Galili daga Yahudiya, sai ya tafi wurinsa ya roƙe shi yă je yă warkar da ɗansa wanda yake bakin mutuwa.
48 Yesu ya amsa masa ya ce, “Idan ba ku ga alamu da ayyukan ban mamaki ba, ba za ku ba da gaskiya ba ko kaɗan.”
49 Sai maˈaikacin hukumar nan ya ce wa Yesu, “Maigirma, ka zo mu tafi kafin yarona ya mutu.”
50 Yesu ya ce masa, “Ka tafi, gama yaronka zai rayu.” Mutumin kuwa ya gaskata da abin da Yesu ya faɗa masa, sai ya yi tafiyarsa.
51 Yana kan hanyarsa zuwa gida ke nan, sai ga bayinsa suka gamu da shi, suka ce masa, “Yaronka yana samun sauƙi.”
52 Sai ya tambaye su ainihin lokacin da ya fara samun sauƙin. Sai suka ce masa, “Jiya da ƙarfe ɗaya na rana ne zazzaɓin ya sake shi.”
53 Sai baban yaron ya gane cewa a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ka tafi, gama yaronka zai rayu.” Sai mutumin da dukan iyalinsa suka ba da gaskiya ga Yesu.
54 Wannan ne aikin ban mamaki na biyu da Yesu ya yi bayan da ya bar Yahudiya ya tafi Galili.