Hausa Bible
Yahaya 18
1 Bayan da Yesu ya gama wannan adduˈa, sai ya ƙetare Rafin Kidron zuwa wancan ƙetare tare da almajiransa. A ƙetaren rafin kuwa akwai wata gona, sai Yesu da almajiransa suka shiga ciki.
2 Yahuda, almajirin da ya ba da Yesu ya san wurin domin Yesu ya saba haɗuwa da almajiransa a can.
3 Sai Yahuda ya ɗauko ƙungiyar soja da masu gadin Haikali waɗanda manyan firistoci da Farisiyawa suka aika, suka tafi gonar, suna riƙe da fitilu, da sanduna masu wuta, da kuma kayan yaƙi.
4 Yesu kuwa da ya san duk abin da zai same shi, sai ya fito, ya ce musu, “Wa kuke nema?”
5 Suka amsa suka ce, “Yesu Banazaret.” Yesu ya ce musu, “Ni ne.” Yahuda wanda ya ba da Yesu kuwa yana tsaye tare da su.
6 Da Yesu ya ce musu, “Ni ne”, sai mutanen suka ja da baya har suka fāɗi a ƙasa.
7 Yesu ya sāke tambayarsu ya ce, “Wa kuke nema?” Sai suka ce, “Yesu Banazaret.”
8 Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na gaya muku cewa ni ne shi. In kuwa ni kuke nema, to, ku bar waɗannan mutane su tafi.”
9 Wannan ya faru ne domin maganar da Yesu ya riga ya yi ta cika. Gama dā ya ce, “A cikin mutanen da ka ba ni ba wanda ya ɓace.”
10 Siman Bitrus kuwa wanda yake da takobi, ya zaro shi ya sari bawan babban firist, har ya yanke masa kunne na dama. Sunan wannan bawan kuwa Malkus ne.
11 Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Ka mai da takobinka cikin gidansa. Ba zan sha daga cikin kwaf da Uba ya ba ni in sha ba?”
12 Sai ƙungiyar soja da shugabansu, da masu gadin Haikalin nan na Yahudawa suka kama Yesu, suka ɗaure shi.
13 Da farko suka kai shi wurin Hannana, gama shi baban matan Kayafa ne. Kayafa kuwa shi ne babban firist a wannan shekara.
14 Shi ne ya ba Yahudawa shawara cewa ya fi kyau mutum ɗaya ya mutu saboda sauran mutane.
15 Sai Siman Bitrus da wani daga cikin almajiran Yesu suka bi Yesu a baya. Wannan almajirin kuwa babban firist ya san shi, shi kuma ya shiga filin gidan babban firist ɗin tare da Yesu.
16 Amma Bitrus ya tsaya a bakin ƙofa daga waje. Sai almajirin nan da babban firist ya waye shi ya fita ya yi magana da yarinya maigadin ƙofa, saˈan nan ya shigo da Bitrus.
17 Yarinyar da take gadin ƙofar ta ce wa Bitrus, “Anya! Ba kana cikin almajiran mutumin nan ba?” Bitrus ya amsa ya ce, “Aˈa, ba na ciki.”
18 Ana sanyi, saboda haka bayi da masu gadi suka hura wuta da gawayi, suna tsaitsaye, suna jin ɗumin wutar. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin ɗumin wutar.
19 Sai babban firist ya yi wa Yesu tambayoyi a kan almajiransa da kuma koyarwarsa.
20 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi magana a fili a gaban kowa, na kuma yi ta koyarwa a majamiˈu da Haikali, inda Yahudawa sukan taru duka. Ban taɓa faɗa kome a ɓoye ba.
21 To, me ya sa kake yi mini tambayoyi? Ai, sai ka yi wa mutanen da suka saurare ni tambayoyi a kan abin da na faɗa musu, gama sun san abin da na faɗa.”
22 Da ya faɗa haka, sai wani daga cikin mai gadin da yake tsaye ya mari Yesu, ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”
23 Yesu ya amsa ya ce, “In dai na faɗa wani abu ne wanda ba daidai ba, to, sai ka nuna yadda yake. Amma in abin da na faɗa gaskiya ne, to, me ya sa ka mare ni?”
24 Sai Hannana ya sa aka kai Yesu a ɗaure wurin Kayafa, babban firist.
25 Har yanzu Bitrus kuwa yana tsaye yana jin ɗumin wuta, sai waɗansu suka tambaye shi suka ce, “Anya! Kai ma ba cikin almajiransa kake ba?” Sai Bitrus ya yi musū ya ce, “Bāna ciki.”
26 Wani daga cikin bayin babban firist yana nan. Wannan bawa kuwa dangin wanda Bitrus ya yanke masa kunne ne, sai ya ce wa Bitrus, “Ashe, ban gan ka tare da shi a gonar ba?”
27 Sai Bitrus ya sāke yin musū. Nan da nan kuwa zakara ya yi cara.
28 Tun da sassafe suka fitar da Yesu daga gidan Kayafa zuwa fādar gwamnan Roma. Amma suka ƙi shiga cikin fādar, wai domin kada su ƙazantu a gaban Allah har su kāsa cin abincin Bikin Ƙetarewa.
29 Saboda haka Bilatus ya fito waje ya same su, ya ce, “Wacce ƙara ce kuka kawo game da mutumin nan?”
30 Sai suka amsa masa suka ce, “Da wannan ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu kawo shi wurinka ba.”
31 Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga koyarwarku.” Sai Yahudawa suka ce masa, “Ai, ba a ba mu ikon yanke wa wani hukuncin kisa ba.”
32 Wannan ya faru ne kuwa domin a cika maganar da Yesu ya yi wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi.
33 Sai Bilatus ya koma cikin fādar, saˈan nan ya kira Yesu ya tambaye shi ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?”
34 Yesu ya amsa ya ce, “Wannan tambaya a kanka ne, ko kuwa waɗansu ne suka yi maka magana a kaina?”
35 Bilatus ya amsa ya ce, “Ai, ni ba Bayahude ba ne, mutanenka ne da manyan firistoci suka kawo ka a wurina. Me ka yi?”
36 Yesu ya amsa ya ce, “Mulkina ba iri na duniya ba ne. Da mulkina iri na wannan duniya ne, da masu yi mini hidima za su yi yaƙi domin kada a bashe ni ga Yahudawa.”
37 Sai Bilatus ya ce, “Ashe, kai sarki ne?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai ne da kanka ka ce ni sarki ne. Wannan shi ne dalilin da aka haife ni, shi ne kuma dalilin da na shigo duniya, domin in ba da shaida ga gaskiya. Kuma duk wanda yake na gaskiya, yakan saurari muryata.”
38 Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?” Bayan da ya yi wannan tambaya, sai ya sāke fitowa wurin Yahudawa ya ce musu, “Ni kam, ban same shi da wani laifi ba.
39 Amma dai kuna da wata alˈada, in dai Bikin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku da ɗan kurkuku guda. To, kuna so in sakar muku da sarkin Yahudawa?”
40 Suka sāke amsa, suka yi ihu suna cewa, “Aˈa, ba wannan za ka sake ba, sai dai ka saki Barabbas!” Barabbas kuwa wani ɗan fashi ne.