Skip to content

Hausa Bible

Ayyukan Manzanni 25

1 To, bayan kwana uku da Festus ya iso domin yă kama aikin gwamna, sai ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima.

2 Sai manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka kai ƙarar Bulus a wurinsa. Suka roƙe shi,

3 yă sa a mai da Bulus Urushalima domin sun shirya waɗansu su jira su kashe shi a hanya.

4 Festus ya amsa ya ce, “Ana gadin Bulus a Kaisariya, ni da kaina zan je can ba da jimawa ba.

5 Saboda haka sai manyanku su zo tare da ni, idan kuwa mutumin nan yana da wani laifi sai su kawo ƙararsa.”

6 Bai fi kwana takwas ko goma a wurinsu ba, sai ya koma Kaisariya. Washegari kuma ya zauna a kujerar shariˈa, ya sa a kawo Bulus a gabansa.

7 Da Bulus ya zo, Yahudawan da suka zo daga Urushalima suka tashi suka kewaye shi, suna ta kawo ƙara masu yawa, masu tsanani a kansa, waɗanda ma ba su iya tabbatarwa ba.

8 Amma Bulus ya kāre kansa ya ce, “Ni ban yi wa Koyarwar Yahudawa laifi ba, ban kuma yi wa Haikali, ko Kaisar laifi ba ko kaɗan.”

9 Amma Festus yana so ya faranta wa Yahudawa rai, ya tambayi Bulus, “Ko ka yarda ka je Urushalima a yi maka shariˈa a gabana a can game da waɗannan abubuwa?”

10 Amma Bulus ya ce, “Ina gaban kotun Kaisar, a nan ne ya kamata a yi mini shariˈa. Ban yi wa Yahudawa wani laifi ba, kai ma ka san da haka sosai.

11 Idan ni mai laifi ne, har na yi laifin da ya isa a kashe ni, ai, ba zan ƙi a kashe ni ba. Amma idan ba wata gaskiya a cikin ƙarar da suke yi, to, ba mai iya ba da ni gare su. Na roƙa a ɗaukaka ƙarata zuwa gaban Kaisar.”

12 Bayan da Festus ya yi shawara da majalisarsa, sai ya amsa ya ce, “To, ka roƙa a ɗaukaka ƙararka zuwa gaban Kaisar, wurin Kaisar kuwa za ka tafi.”

13 Bayan ˈyan kwanaki, Sarki Agiriffa da Banis suka zo Kaisariya domin su marabci Festus.

14 Tun da za su yi kwanaki da dama a wurin, sai Festus ya kawo maganar Bulus ga sarki. Festus ya ce, “Akwai wani mutumin da Felis ya bar mini a kurkuku.

15 Lokacin da nake Urushalima manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka kawo mini ƙarar mutumin nan, suka roƙe ni in yanke masa hukunci.

16 Amma na gaya musu cewa mu Romawa ba mu saba yi wa mai laifi shariˈa ba, sai an kawo shi a gaban masu ƙararsa fuska da fuska, sai an kuma ba shi zarafi domin yă kāre kansa game da ƙarar da aka yi.

17 Saboda haka da suka zo nan tare da ni, ban ɓata lokaci ba, washegari kawai na hau kujerar shariˈa, na kuma sa a kawo mutumin.

18 Da masu ƙarar suka tashi, ba su kawo ƙararsa a kan wani mummunan laifin da nake tsammani ya yi ba.

19 Sai dai suna da waɗansu maganganun da ba su yarda da Bulus a kai ba, game da addininsu, da wani Yesu wanda ya mutu, wanda Bulus ya nace cewa yana da rai.

20 Ni kuwa da na rasa yadda zan bincike waɗannan abubuwa, sai na tambayi Bulus ko ya yarda yă je Urushalima a yi masa shariˈa a can game da abubuwan nan.

21 Amma da ya nema a tsayar da maganarsa domin babban Sarki Kaisar yă yanke masa shariˈa, sai na ba da umarni a yi gadinsa har zuwa lokacin da zan aika da shi wurin Kaisar.”

22 Sai Sarki Agiriffa ya ce wa Festus, “Ni ma dai zan so in saurari mutumin nan da kaina.” Festus ya ce, “Za ka kuwa ji shi gobe.”

23 To, washegari sai Agiriffa da Banis suka shigo da daraja irin ta sarakuna, sun zo tare da shugabannin yaƙi da kuma manyan garin. Sai Festus ya ba da umarni a shigo da Bulus.

24 Sai Festus ya ce, “Sarki Agiriffa, da dukan mutanen da suke nan tare da mu, ga mutumin da duk jamaˈar Yahudawa suka kawo mini ƙararsa a Urushalima, da kuma a nan, har suna ihu wai bai kamata a bar shi da rai ba.

25 Amma ni ban ga ya yi wani abin da ya isa a kashe shi ba. Tun da kuma shi da kansa ya nema a kai shariˈarsa gaban mai girma Kaisar, na ce to zan aika da shi wurinsa.

26 Amma ba ni da wata tabbatacciyar maganar da zan rubuta wa mai girma sarkin Roma a kansa. Saboda haka na kawo shi gabanku, musamman gabanka, Sarki Agiriffa, domin bayan da muka bincike shi, ko zan sami abin da zan rubuta.

27 Don ni a ganina, wawanci ne a aika da ɗan kurkuku, ba tare da an nuna laifofin da ya yi ba.”

Open Bible reader