Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 23
1 Sai Bulus ya zuba wa ˈyan majalisar ido ya ce, “Ku ˈyanˈuwana, har wa yau, a cikin zuciyata ba ni da shakka ko wani abin damuwa a kan rayuwar da na yi a gaban Allah.”
2 Da jin wannan sai Hananiya babban firist ya sa waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge shi a baki.
3 Sai Bulus ya ce masa, “Kai munafuki! Kai bango ne da aka shafe da farin fenti, kai ma Allah zai buge ka! Ka zauna kana yi mini hukunci bisa ga Koyarwar Musa, amma ga shi kuwa kana sa a buge ni, abin da bai yi daidai ba bisa ga Koyarwa.”
4 Waɗanda suke tsaye a wurin suka ce wa Bulus, “Babban firist na Allah za ka yi masa zagi?”
5 Bulus kuwa ya ce, “ˈYanˈuwana, ban san shi ne babban firist ba. Gama an rubuta cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, ‘Kada ka zagi shugaban jamaˈa.’ ”
6 Da Bulus ya kula cewa waɗansunsu Sadukiyawa ne, waɗansu kuma Farisiyawa ne, sai ya tā da murya a majalisar ya ce, “ˈYanˈuwa, ni ma Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ga shi kuwa saboda na sa zuciya ga tashin matattu shi ya sa ake yi mini shariˈa.”
7 Da ya faɗa haka sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, har taron ya rabu kashi biyu.
8 Gama Sadukiyawa suna riƙe da raˈayi cewa babu tashin matattu, babu malaˈiku, ko ruhohi. Farisiyawa kuwa sun yarda akwai duka uku.
9 Sai babban rikici ya tashi, waɗansu malaman Koyarwar Musa na ƙungiyar Farisiyawa suka tashi tsaye, suka yi ta gardama suka ce, “Mu ba mu sami mutumin nan da laifin kome ba. Mai yiwuwa wani ruhu, ko malaˈika ne ya yi masa magana.”
10 Da gardamar ta yi tsanani sai shugaban ya ji tsoro kada su yi kaca-kaca da Bulus. Sai ya ba da umarni cewa sojojin su sauko su ƙwace Bulus da ƙarfi daga wurinsu, su kai shi barikin soja.
11 Da dare ya yi sai Ubangiji ya tsaya kusa da Bulus ya ce, “Ka ci gaba da ƙarfin zuciyarka, domin kamar yadda ka shaide ni a Urushalima, haka kuma lallai ne za ka shaide ni a Roma.”
12 Da gari ya waye, Yahudawa suka yi shiri su kashe Bulus. Suka yi rantsuwa cewa ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe Bulus.
13 Waɗanda suka yi wannan mugun shiri kuwa sun fi mutum arbaˈin.
14 Sai suka je wurin manyan firistoci da shugabanni, suka ce, “Mun yi babbar rantsuwa cewa ba za mu ci ba, ba za mu sha ba sai mun kashe mutumin nan.
15 Saboda haka yanzu ku da majalisa ku roƙi shugaban sojoji yă kawo muku shi, kamar kuna so ne ku ƙara bincike maganarsa sosai, mu kuwa a shirye muke mu kashe shi kafin yă iso.”
16 To, da ɗan ˈyarˈuwar Bulus ya ji labarin shirin da suke yi, sai ya je ya shiga barikin ya faɗa wa Bulus.
17 Bulus kuwa ya kira wani babban sojan Roma ya ce, “Ka kai saurayin nan wurin shugaba, yana da wata maganar da zai gaya masa.”
18 Sai babban sojan Roma ya ɗauki saurayin ya kai shi wurin shugaban. Babban sojan Roma ya ce, “Ɗan kurkukun nan Bulus, ya kira ni, ya roƙe ni in kawo saurayin nan a wurinka, don saurayin yana da abin da zai gaya maka.”
19 Sai shugaban ya kama hannun saurayin, ya ja shi gefe ɗaya, ya tambaye shi, shi kaɗai, “Me za ka gaya mini?”
20 Saurayin ya ce, “Shugabannin Yahudawa sun shirya za su roƙe ka ka kai Bulus majalisa gobe, kamar suna so su ƙara bincike maganarsa sosai.
21 Amma kada ka yarda musu, don fiye da mutum arbaˈin daga cikinsu suna nema su kashe shi, sun kuma yi rantsuwa cewa ba za su ci ba, ba za su sha ba sai sun kashe shi. Yanzu kuwa a shirye suke, suna jira ne kawai ka yarda.”
22 Sai shugaban ya ja masa kunne ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka gaya mini wannan magana.” Saˈan nan ya sallame shi.
23 Saˈan nan shugaban ya kira manyan sojojin Roma biyu ya ce musu, “Ku shirya don za ku tashi zuwa Kaisariya da ƙarfe tara na dare, tare da sojoji ɗari biyu, da sojoji sabaˈin masu hawan dawaki, da sojoji ɗari biyu masu faɗa da māshi.
24 Ku kuma samo dawakin da Bulus zai hau. Sai ku kai shi wurin Gwamna Felis lafiya lau.”
25 Shugaban sojan kuma ya rubuta wasiƙa haka,
26 “Daga Kalaudiyus Lisiyas, zuwa ga Maigirma Gwamna Felis. Gaisuwa mai yawa.
27 “Mutumin nan, Yahudawa sun kama shi, sun kusa su kashe shi, sai na yi sauri da sojojina na ƙwato shi, domin na ji shi mai ˈyancin Roma ne.
28 Tun da ina so in ji laifin da suke zarginsa da shi, sai na kai shi majalisarsu.
29 Na kuwa samu suna zarginsa a kan maganar koyarwarsu, amma laifin da suka ɗora masa bai isa a ɗaure shi ko a kashe shi ba.
30 “Da aka sanar mini cewa akwai wani mugun shirin da aka ƙulla masa, nan da nan na aika da shi wurinka. Na kuma umarci masu ƙararsa su faɗa a gabanka laifin da suka ga ya yi.”
31 Saboda haka sojojin suka ɗauki Bulus, kamar yadda aka umarce su, suka kai shi Antifatiris da dare.
32 Washegari suka bar sojoji masu hawan dawaki su ci gaba da shi, su kuwa suka koma barikinsu.
33 Da sojoji masu hawan dawakin suka isa Kaisariya, sai suka ba gwamna wasiƙar, suka kuma bar Bulus a hannunsa.
34 Da gwamna ya karanta wasiƙar, ya tambayi Bulus ko shi daga wane yanki ne. Da ya ji daga Kilikiya yake,
35 sai ya ce, “Zan saurari maganarka, lokacin da masu ƙararka sun zo.” Sai gwamnan kuma ya ba da umarni a tsare shi a fādar da Sarki Hirudus ya gina.