Hausa Bible
Romawa 15
1 Mu da muke masu ƙarfi cikin bangaskiyarmu ya kamata mu ɗauki nauyin waɗanda ba su da ƙarfi, don mu taimake su cikin kāsawarsu. Kada kuma mu nuna halin sonkai.
2 Bari kowa a cikinmu yă faranta wa ɗanˈuwansa rai saboda amfaninsa da kuma ginawar bangaskiyarsa.
3 Gama ko Almasihu ma bai yi sonkai ba. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zage-zagen masu yi maka zagi sun fāɗo a kaina.”
4 Gama duk abin da aka rubuta tun dā a cikin Rubutacciyar Maganar Allah an rubuta ne domin a koyar da mu, domin mu zama da sa zuciya ta wurin jimrewa da ƙarfafawa waɗanda Rubutacciyar Maganar Allah sukan ba mu.
5 Bari Allah mai ba da jimrewa da ƙarfafawa yă kai ku ga yadda za ku yi haƙuri da juna a saˈad da kuna bin gurbin Almasihu Yesu.
6 Ta haka dukanku za ku kasance da baki ɗaya, da nufi ɗaya kuma, kuna ɗaukaka Allah wanda shi ne Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu.
7 Ku karɓi juna hannu biyu-biyu kamar yadda Almasihu ya karɓe ku hannu biyu-biyu don ku sa a ɗaukaka Allah.
8 Gama ina dai gaya muku cewa dalilin da Almasihu ya zama mai yin hidima ga Yahudawa shi ne domin a nuna gaskiyar kalmar Allah, a kuma tabbatar da alkawaran da aka yi wa kakannin kakanninsu,
9 don kuma waɗanda ba Yahudawa ba su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Saboda wannan, ya Ubangiji, zan yabe ka a cikin alˈummai, zan rera waƙar yabo ga Sunanka.”
10 Rubutacciyar Maganar Allah ta sāke cewa, “Ya ku waɗanda ba Yahudawa ba, ku yi farin ciki tare da mutanen Allah.”
11 An ƙara da cewa, “Ku yabi Ubangiji, ya ku waɗanda ba Yahudawa ba duka, ku yi masa yabo, ya ku kabilu duka.”
12 Kuma Ishaya ya ce, “Wani daga tushen Yesse zai bayyana, Zai tashi yă yi mulkin waɗanda ba Yahudawa ba, a gare shi ne kabilu za su sa zuciya.”
13 Bari Allah mai kawo sa zuciya yă ba ku cikakken farin ciki da salama a saˈad da kuke ba da gaskiya gare shi, domin ku yalwata da sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
14 ˈYanˈuwana, ni da kaina na amince cewa ku da kanku kuna cike da kirki kuna kuma cike da cikakken sani, har kun isa ku koya wa junanku.
15 A rubutun nan nawa na fita a fili sosai ina magana a kan waɗansu abubuwa don in tuna muku da su. Na yi wannan kuwa bisa ga alherin nan wanda Allah ya yi mini,
16 wanda ya sa ni in zama mai hidimar Almasihu Yesu ga waɗanda ba Yahudawa ba. Ina aikin firist ta wurin hidimar shelar labari mai daɗi na Allah don waɗanda ba Yahudawa ba su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, waɗanda aka tsarkake su ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
17 Saboda haka ina iya yin taƙama cikin Almasihu Yesu game da aikin da nake yi wa Allah.
18 Ba zan yi ƙarfin hali in yi magana game da wani abu ba, sai dai abin da Almasihu ya aikata ta wurina. Wannan abu kuwa shi ne yadda aka jawo waɗanda ba Yahudawa ba ga yin biyayya ga Allah ta wajen maganata da aikina,
19 ta wajen ikon alamu da ayyukan ban mamaki, duka kuwa ta wurin ikon Ruhun Allah ne. Wato, daga Urushalima na kewaye har zuwa Ilirikum na yi shelar labari mai daɗi na Almasihu, har na cika aikin nan duka.
20 A koyaushe niyyata ita ce in yi waˈazin labari mai daɗi a duk inda ba a san Almasihu ba, domin kada yă zama cewa ina yin gini a kan tushen da wani ne dabam ya kafa.
21 A maimakon haka, sai dai kamar yadda yake a rubuce cewa, “Waɗanda ba a taɓa faɗa musu labarinsa ba, za su gani, waɗanda ba su taɓa ji labarinsa ba, za su gane.”
22 Wannan ne ya sa sau da yawa aka hana ni zuwa wurinku.
23 Yanzu kam na riga na gama aikina a wuraren nan. Tun da yake tun shekaru masu yawa ina marmarin zuwa wurinku domin in gan ku,
24 na shirya in ziyarce ku yanzu. Ina fata cewa a lokacin da zan wuce zuwa ƙasar Sifen, zan bi ta wurinku in kawo ziyara. Ina fata kuma bayan da na ji daɗin zama tare da ku na ɗan lokaci, zan ci gaba da tafiyata zuwa can tare da taimakonku.
25 Yanzu kam za ni Urushalima don in kai taimako wa tsarkakan da suke wurin.
26 Jamaˈar masu bi wadda take a Makidoniya da kuma a Akaya sun ji daɗin ba da kyautai domin taimakon waɗanda suke da rashi cikin tsarkakan Urushalima.
27 Sun ji daɗin yin haka, ko da yake lallai wannan kamar hakki ne a kansu. Da yake waɗanda ba Yahudawa ba sun sami nasu rabon albarkun ruhaniya daga Yahudawa, ya zama musu kamar bashi ke nan su yi amfani da albarkunsu na duniya domin su biya bukatar Yahudawa.
28 In kuwa na gama wannan aiki, na kuma tabbata cewa na danƙa musu wannan taimakon da aka bayar saboda su, zan kama hanya zuwa Sifen, in kuma kawo ziyara saˈad da zan wuce zuwa can.
29 Na tabbata cewa in na zo wurinku, zan zo ne da cikakkiyar albarkar Almasihu.
30 ˈYanˈuwa, saboda Ubangijinmu Yesu Almasihu da kuma bisa ga ƙaunar da Ruhu yake bayarwa, ina roƙonku cewa ku taimake ni cikin famata ta wurin yin adduˈa ga Allah saboda ni.
31 Ku yi adduˈa don in sami tsira daga hannun marasa bi a yankin Yahudiya, domin kuma taimakon da zan bayar a Urushalima yă zama abin karɓa ga tsarkakan da suke a wurin.
32 Ta haka kuwa, idan nufin Allah ne, zan iso wurinku da farin ciki, in kuma sami hutawa tare da ku.
33 Allah mai ba da salama yă kasance tare da ku duka. Amin.