Hausa Bible
Romawa 1
1 Daga Bulus, bawan Almasihu Yesu, wanda aka kira shi yă zama manzonsa, aka kuma keɓe shi domin yin shelar labari mai daɗi na Allah.
2 Labari mai daɗin nan ne Allah ya yi alkawarinsa tun dā ta wurin annabawansa, kamar yadda yake a rubuce cikin Rubutacciyar Maganar Allah mai tsarki.
3 Wannan labari mai daɗi kuwa game da Ɗansa wanda bisa ga mutuntaka shi daga zuriyar Dawuda ne,
4 amma bisa ga tsarkinsa na ruhu, da iko an tabbatar da shi Ɗan Allah ne ta wurin tashinsa daga matattu. Shi Yesu Almasihu kuwa an tabbatar shi Ubangijinmu ne.
5 Ta wurin Almasihu Yesu da kuma domin a girmama sunansa ne na sami alheri da kiran zaman manzonsa domin in kira mutane daga cikin alˈummai duka domin su gaskata su kuma yi biyayya.
6 Wannan kuwa ya shafe ku, ku waɗanda Allah ya kira ku ku zama na Yesu Almasihu.
7 Ga dukanku da kuke a Roma, waɗanda Allah yake ƙauna, ya kuma kira ku ku zama tsarkaka, Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Almasihu su kasance tare da ku.
8 Da farko dai ina yi wa Allahna godiya ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana ba da labarin bangaskiyarku koˈina a cikin duniya.
9 Allah wanda nake yi masa hidima da dukan zuciyata ta wurin shelar labari mai daɗi na Ɗansa, shi ne shaidata cewa ina tunawa da ku ba fasawa,
10 a duk lokacin da nake adduˈa. Ina roƙon Allah cewa, idan nufinsa ne, ko ta yaya in sami dama yanzu in zo wurinku.
11 Gama ina marmari in gan ku domin in ba ku wata kyauta ta ruhu wadda za ta ƙarfafa ku.
12 Nufina shi ne, ni da ku mu ƙarfafa juna, wato in ƙarfafa ku da bangaskiyata, ku kuma ku ƙarfafa ni da taku.
13 ˈYanˈuwa, ina so ku sani cewa sau da yawa na yi shiri in zo wurinku, amma har yanzu an hana ni yin haka. Dalilin son zuwana kuwa shi ne domin in yi girbi a cikinku kamar yadda na yi a cikin sauran waɗanda ba Yahudawa ba.
14 Akwai hakkin kowa a kaina, na mutanen birni da na mutanen ƙauye, na masu ilimi da na marasa ilimi.
15 Shi ya sa na yi niyya sosai in shaida muku labari mai daɗi, ku ma da kuke a Roma.
16 Labari mai daɗin nan ba abin kunya ba ne a gare ni, gama shi ne ikon Allah wanda yake kai kowane mutum wanda ya gaskata ga samun ceto, da farko ga Yahudawa, saˈan nan ga waɗanda ba Yahudawa ba.
17 Gama ta wurin labarin nan mai daɗi ne ana bayyana adalcin nan wanda daga wurin Allah yake, kuma ana samun adalcin nan ta wurin bangaskiya daga farko har zuwa ƙarshe. Kamar yadda yake a rubuce cikin Maganar Allah cewa, “Mai adalci, ta wurin bangaskiya ne zai rayu.”
18 Gama ana bayyana yadda Allah daga sama zai hukunta mutane cikin fushinsa a kan dukan rashin halin Allah da aikin mugunta na mutane waɗanda suke danne gaskiya ta wurin aikin muguntarsu.
19 Gama abin da ana iya sani game da Allah yana nan a fili a gare su, domin Allah ne ya bayyana musu shi.
20 Halin Allahntaka na Allah da kuma ikonsa na har abada ba abubuwan da aka iya gani da ido ba ne. Amma tun halittar duniya an bayyana waɗannan abubuwa a fili, ana kuma iya gane su bisa ga abubuwan da aka halitta. Saboda haka mutane ba su da wata hujja!
21 Gama ko da yake sun san Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a matsayinsa na Allah ba, ba su kuma nuna masa godiya ba. A maimakon haka sai tunaninsu ya zama banza, zukatansu marar tunani kuwa suka duhunta.
22 Ko da yake sun ce wai su masu hikima ne, amma su wawaye ne.
23 Suka canja ɗaukakar Allah marar mutuwa da gunki mai kamannin mutum mai mutuwa, da kuma gumaka masu kamannin tsuntsaye, da dabbobi, da dangin macizai da ƙadangaru.
24 Saboda haka Allah ya bashe su ga aikata mugayen shaˈawace-shaˈawacen zukatansu, da jikinsu kuma suna yin abin kunya da juna.
25 Sun mai da gaskiyar Allah ta zama ƙarya. Suna bauta wa abubuwan da aka halitta, har suna yi musu hidima a maimakon su yi wa Mahalicci da kansa, shi wanda ya isa a yabe shi har abada. Amin.
26 Saboda haka Allah ya bashe su ga shaˈawace-shaˈawacen masu ban kunya. Matansu kuwa suka canja daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa irin haɗuwar da ba daidai ba.
27 Haka kuma da shaˈawar junansu ta sha kansu, sai maza suka bar haɗuwa da mata wadda ita ce daidai bisa ga halitta. Maza da maza suna aikata abin kunya, ta haka suka kuma jawo wa kansu hukuncin da ya yi daidai da mugayen ayyukansu.
28 Da yake sun ƙi su kasance da sanin Allah, sai Allah ya bashe su ga tunanin banza da wofi domin su aikata abin da bai kamata a yi ba.
29 Suna cike da kowane irin rashin adalci, da mugunta, da kwaɗayi, da ƙiyayyar zuciya. Suna cike da kishi, da kisan kai, da faɗa, da ruɗu, da baƙar zuciya. Su masu gulma ne,
30 masu ɓata suna, masu gāba da Allah, masu zagi, masu ɗaga kai, masu girmama kansu, masu ƙulla mugunta, masu rashin biyayya ga iyaye.
31 Su marasa hankali ne, marasa cika alkawari, marasa ƙauna, da marasa tausayi.
32 Sun san ƙaˈidar Allah cewa duk masu aikata halayen nan sun cancanci mutuwa, amma ba wai suna aikata abubuwan nan kaɗai ba, har suna goyon bayan waɗanda su ma suna aikata haka.