Skip to content

Hausa Bible

Matiyu 12

1 Ana nan a Ranar Hutu ta Mako, Yesu da almajiransa suka bi ta gonakin hatsin alkama. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara cire tsabar alkamar suna ci.

2 Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce masa, “Ka gani, almajiranka suna yin abin da Koyarwar Musa ta hana a yi a Ranar Hutu ta Mako.”

3 Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku karanta abin da Dawuda ya yi lokacin da shi da abokan tafiyarsa suke jin yunwa ba?

4 Yadda ya shiga Gidan Allah ya ci Burodin da Aka Keɓe, wanda bai kamata ko shi ko abokan tafiyarsa su ci ba, sai dai firistoci kaɗai.

5 Ko ba ku karanta a cikin Koyarwar Musa ba, yadda firistoci a Haikali suke yin banza da Ranar Hutu ta Mako, kuma bai zama musu laifi ba?

6 Ina gaya muku, ga wanda ya fi Haikali a nan.

7 Amma da kun san abin da wannan ayar take nufi wato, ‘Jinƙai nake so, ba hadaya ba,’ da ba ku ga marasa laifi da laifi ba.

8 Gama Ɗan Mutum Ubangiji ne har ma da na Ranar Hutu ta Mako.”

9 Sai Yesu ya bar wurin ya shiga majamiˈarsu.

10 Akwai wani mutum a wurin mai shanyayyen hannu. Sai suka tambayi Yesu suka ce, “Koyarwar Musa ta yarda a yi warkarwa a Ranar Hutu ta Mako?” Sun yi wannan tambaya ne domin su same shi da laifi.

11 Sai ya ce musu, “A ce waninku yana da tunkiya ɗaya tak, sai ta fāɗi cikin rami a Ranar Hutu ta Mako, mai tunkiyar ba zai fitar da ita ba?

12 Ai, mutum ya fi tunkiya daraja sosai. Saboda haka ba a hana yin aikin alheri a Ranar Hutu ta Mako ba.”

13 Sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙo, nan da nan sai hannun ya warke ya zama kamar ɗayan hannun.

14 Amma Farisiyawa suka fita suka yi shawara yadda za su kashe Yesu.

15 Da Yesu ya gane haka, sai ya bar wurin. Sai mutane da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su duka.

16 Ya kuma ja musu kunne cewa kada su ba da labarinsa.

17 Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ne ta bakin annabi Ishaya cewa,

18 “Ga bawana wanda na zaɓa, shi ne nake ƙauna, wanda nake jin daɗinsa sosai. Zan cika shi da Ruhuna, zai sanar wa alˈummai shariˈar gaskiya.

19 Ba zai yi gardama, ko yă yi magana da ƙarfi ba, ba za a ji muryarsa a titi ba.

20 Karan da ya yi kusan karyewa, ba zai karya ba, fitilar da ta yi kusan mutuwa kuma, ba zai kashe ta ba, sai ya sa gaskiya ta ci nasara,

21 alˈummai kuma za su sa zuciya ga sunansa.”

22 Sai aka kawo masa wani beben makaho mai aljani. Yesu kuwa ya warkar da shi, har mutumin ya yi magana ya kuma iya gani.

23 Mutanen duka suka yi mamaki suka ce, “Shin, ba wannan shi ne Ɗan Dawuda ba?”

24 Amma da Farisiyawa suka ji haka sai suka ce, “Ai, da ikon Baˈalzabul sarkin aljanu ne wannan mutumin yake fitar da aljanu.”

25 Da yake Yesu ya san abin da suke tunani sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu kashi biyu suna gāba da juna, mulkin ba zai tsaya ba. Kuma gari ko gidan da mutanen sun rabu kashi biyu suna gāba da juna, ba zai tsaya ba.

26 Idan Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, yana faɗa da kansa ke nan. To, yaya mulkinsa zai tsaya?

27 Idan kuwa da ikon Baˈalzabul nake fitar da aljanu, to almajiranku fa? Da ikon wa suke fitar da su? Almajiranku ne za su yi muku shariˈa a kan wannan.

28 Idan ni kuwa da ikon Ruhun Allah nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan.

29 “Ba za a iya shiga gidan mutum mai ƙarfi a kwashi kayansa ba, sai dai idan an ɗaure shi tukuna, saˈan nan za a iya kwashi kayan gidansa.

30 “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ke nan, wanda bai taimake ni tarawa ba kuwa, yana watsarwa ne.

31 Domin haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane irin zunubi da maganar saɓo, amma wanda ya yi maganar saɓo game da Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.

32 Idan wani ya yi maganar reni ga Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya yi maganar reni ga Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafarta masa ba, ko yanzu ko a zamani mai zuwa.”

33 “Itace mai kyau yakan ba da ˈyaˈya masu kyau. Itace marar kyau kuma yakan ba da ˈyaˈya marasa kyau. Itace dai, da irin ˈyaˈyansa ne ake gane shi.

34 Ku ƙungiyar mugayen macizai! Yaya za ku iya faɗa abu mai kyau tun da ku mugaye ne? Ai, abin da yake cikin zuciya, shi yake fitowa a baki.

35 Mutumin kirki, daga ajiyarsa na kirki, yakan fitar da abin kirki. Mugun mutum, daga cikin ajiyar muguntarsa, yakan fitar da mugun abu.

36 “Ina gaya muku, duk maganar banza da mutane suka yi, za su ba da lissafinta a Ranar Shariˈa.

37 A kan maganarka ne za a yi maka shariˈa, ko ta sa ka zama marar laifi ko mai laifi.”

38 Sai waɗansu daga cikin malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa suka ce masa, “Malam, muna so ka nuna mana wata babbar alamar da za ta bayyana ikonka.”

39 Sai ya amsa musu ya ce, “Mutanen zamanin nan marasa aminci ga Allah ne, mugaye ne kuma! Suna so su ga alama, amma ba za a nuna musu wata alama ba, sai dai alama ta annabi Yona.

40 Gama yadda Yona ya yi kwana uku, dare da rana a cikin ciki na babban kifi, haka ma Ɗan Mutum zai yi kwana uku, dare da rana a cikin ƙasa.

41 A Ranar Shariˈa mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su nuna wa mutanen zamanin nan ba su yi daidai ba, domin su sun tuba saboda waˈazin Yona. Ga shi kuwa wanda ya fi Yona yana a nan.

42 A Ranar Shariˈa, Sarauniyar Sheba za ta tashi tare da mutanen zamanin nan, ta nuna musu ba su yi daidai ba, domin ta zo ne daga wuri mai nisa sosai, domin ta ji koyarwar hikima ta Sarki Solomon. Ga shi kuwa wanda ya fi Solomon yana a nan.”

43 “Idan ƙazamin ruhu ya fita daga jikin mutum, yakan yi ta yawo a wuraren da ba ruwa domin yă sami wurin hutawa. Amma idan bai samu ba,

44 sai yă ce, ‘Zan koma gidana na dā inda na fito.’ Idan ya zo ya samu ba kowa ya kuma ga an share, an gyara gidan,

45 sai yă koma yă kwaso waɗansu ƙazaman ruhohi guda bakwai, waɗanda suka fi shi mugunta, su zo su shiga su zauna a wurin. A ƙarshe, zaman mutumin nan zai fi na farkon muni. Haka ma zai zama ga mutanen wannan zamani.”

46 Yana kan magana da jamaˈa ke nan, sai ga mamarsa da ˈyanˈuwansa suna tsaye a waje suna so su yi magana da shi.

47 Sai aka ce masa, “Ga mamarka da ˈyanˈuwanka suna tsaye a waje suna so su yi magana da kai.”

48 Sai ya ce wa wannan da ya faɗa masa, “Wace ce mamata, kuma su wane ne ˈyanˈuwana?”

49 Sai ya nuna almajiransa da hannunsa ya ce, “Ga mamata da ˈyanˈuwana a nan.

50 Gama duk wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin sama yake so, shi ne ɗanˈuwana, da ˈyarˈuwata da kuma mamata.”

Open Bible reader