Skip to content

Hausa Bible

Markus 12

1 Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai. Ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsewar ˈyaˈyan inabin, ya kuma gina ɗakin maigadi. Ya ba waɗansu manoma hayar gonar, saˈan nan ya tafi wata ƙasa.

2 Da lokacin girbin inabin ya yi, sai ya aiki wani bawansa wurin waɗanda suka karɓi hayar gonar domin yă karɓo masa waɗansu ˈyaˈyan inabi daga gonar.

3 Amma ˈyan hayar suka kama shi, suka yi masa dūka, suka sallame shi hannu wofi.

4 Sai ya sāke aikar musu wani bawa. Suka bugi wannan mutum a kai, suka yi masa wulaƙanci.

5 Ya sāke aikar wani, wannan kuwa manoman suka kashe shi. Ya aika waɗansu kuma da yawa. Manoman suka dūke waɗansu, suka kashe waɗansu.

6 Har yanzu dai yana da sauran mutum ɗaya, wato ɗansa, wanda yake ƙauna. A ƙarshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ‘Ai, za su ba ɗana girma.’

7 Amma ˈyan hayar nan suka ce wa juna, ‘Yawwa! Ga wanda zai ci gādon gonar. Ku zo mu kashe shi, don gādonsa yă zama namu.’

8 Sai suka kama shi, suka kashe shi, suka jefar da gawar a bayan katangar gonar.”

9 Yesu ya tambaye su, ya ce, “To, me mai gonar nan zai yi? Ai, zai zo yă halaka ˈyan hayar nan, yă ba da gonar ga waɗansu.

10 Ashe, ba ku taɓa karanta wannan Rubutacciyar Maganar Allah ba? Don a rubuce yake cewa, “ ‘Dutsen da masu gini suka ƙi, Shi ne ya zama dutse mafi amfani a gini.

11 Wannan yin Ubangiji ne, abin mamaki ne kuwa a idanunmu.’ ”

12 Sai shugabannin Yahudawa suka nemi hanyar da za su kama shi, don sun gane a kansu ne ya yi misalin. Amma suka ji tsoron jamaˈa. Domin haka suka bar shi, suka tafi.

13 Ana nan, sai aka aika waɗansu Farisiyawa da mutanen Hirudus, domin su sa wa Yesu tarko a cikin maganar da zai faɗa.

14 Da suka iso, suka ce masa, “Malam, mun sani kai mai gaskiya ne. Mutane duk ɗaya ne a gare ka, gama ba ka nuna bambanci tsakanin mutane. Kuma kana koyar da hanyar Allah a cikin gaskiya. Kana gani daidai ne mu biya wa Kaisar wato, babban sarkin Roma haraji, ko aˈa?

15 Mu biya, ko kada mu biya?” Amma Yesu ya gane munafuncinsu, ya ce musu, “Me ya sa kuke gwada ni? Ku kawo mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.”

16 Sai suka kawo masa, sai ya ce musu, “Hoton nan da sunan nan na wane ne?” Suka ce masa, “Na Kaisar ne.”

17 Sai Yesu ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar. Ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” Sai suka yi mamakinsa ƙwarai.

18 Waɗansu Sadukiyawa suka zo wurin Yesu. Su ne suke cewa, wai ba tashin matattu. Suka tambaye shi suka ce,

19 “Malam, Musa ya rubuta mana cewa idan ɗanˈuwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba ɗa, dole ne mutumin yă auri matar, yă haifa wa ɗanˈuwansa ˈyaˈya.

20 To, akwai waɗansu ˈyanˈuwa maza guda bakwai. Na farkon ya yi aure, ya mutu bai bar ɗa ba.

21 Na biyun kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba ɗa. Na ukun ma haka.

22 Haka dai duka bakwai ɗin, ba wanda ya bar ɗa. A ƙarshe kuma ita matar ta mutu.

23 To, a tashin matattu za ta zama matar wane ne a cikinsu? Gama duk bakwai ɗin sun aure ta.”

24 Sai Yesu ya amsa, ya ce musu, “Ai, tunaninku ba daidai ba ne don ba ku san Rubutacciyar Maganar Allah ba, ba ku kuma san ikon Allah ba.

25 Lokacin da matattu za su tashi, maza ba za su yi aure ba, mata kuma ba za a ba da su ga aure ba, amma za su zama kamar malaˈikun da suke cikin sama ne.

26 Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku taɓa karanta wannan a littafin Musa ba, don an rubuta cikin labarin ƙaramin itacen da ya ci wuta, cewa, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, da na Ishaku, da kuma na Yakub?’

27 Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai. Kun yi babban kuskure.”

28 Wani malamin Koyarwar Musa ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da ya lura cewa Yesu ya ba su amsa mai kyau, sai ya tambaye shi ya ce, “Wace doka ce mafi girma duka?”

29 Yesu ya amsa, ya ce, “Mafi girma ita ce, ‘Ku ji, ya jamaˈar Israˈila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.

30 Sai ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’

31 Mai biye da ita ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar yadda kake ƙaunar kanka.’ Ba wata dokar da ta fi waɗannan girma.”

32 Sai malamin Koyarwa ya ce wa Yesu, “Daidai ne ka faɗa malam, Ubangiji ɗaya ne, ba kuwa wani sai shi.

33 A ƙaunace shi kuma da dukan zuciya, da dukan tunani, da dukan ƙarfi, ka kuma ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka, ai, ya fi dukan hadayar ƙone-ƙone da yanke-yanke girma.”

34 Da Yesu ya ga yadda ya yi masa magana da hikima, sai ya ce masa, “Kana kusa da mulkin Allah fa.” Bayan wannan kuma ba wanda ya yi ƙarfin hali yă ƙara tambayarsa wani abu.

35 Saˈad da Yesu yake koyarwa a Haikali sai ya yi tambaya ya ce, “Yaya malaman Koyarwar Musa suke cewa Almasihu ɗan Dawuda ne?

36 Dawuda da kansa, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, zauna a hannun damana, Sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin ƙafafunka.’ ”

37 “Dawuda da kansa ya ce da Almasihu ‘Ubangiji’. To, yaya Almasihu zai zama ɗa a wurin Dawuda?” Da jin irin wannan magana a bakin Yesu, jamaˈa suka ji daɗi.

38 A cikin koyarwarsa, Yesu ya ce, “Ku yi hankali da malaman Koyarwar Musa, su masu son sa manyan riguna suna yawo. Suna so a gaishe su a kasuwa.

39 Suna so kuma a ba su wuraren zama masu daraja a majamiˈu, da wuraren zama masu kyau a wurin biki.

40 Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu. Saˈan nan su yi doguwar adduˈa don a gan su. Ai, su za a yi musu hukunci mafi tsanani.”

41 Yesu yana zaune a Haikali wurin da ake zuba baiko, yana duban yadda jamaˈa suke zuba kuɗinsu a akwatin baiko. Waɗansu masu arziki da yawa suna zuba kuɗi mai yawa.

42 Sai ga wata matalauciya wadda mijinta ya mutu, ta zo ta zuba ˈyan tagulla biyu, da ba su kai kobo ba.

43 Sai Yesu ya kira almajiransa, ya ce musu, “Gaskiya, ina gaya muku, abin da matalauciyar nan wadda mijinta ya mutu, ta zuba cikin akwatin, ya fi na sauransu duka.

44 Dukansu sun bayar daga yawan abin da suke da shi ne, amma ita kuwa daga cikin talaucinta ta ba da dukan kome, har ma dukan abin da take dogara da shi.”

Open Bible reader