Hausa Bible
Markus 12:1
Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai. Ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsewar ˈyaˈyan inabin, ya kuma gina ɗakin maigadi. Ya ba waɗansu manoma hayar gonar, saˈan nan ya tafi wata ƙasa.
Open Bible reader