Hausa Bible
Luka 7
1 Da Yesu ya gama gaya wa mutane dukan waɗannan abubuwa, sai ya tafi Kafarnahum.
2 A can ɗin, akwai wani babban sojan Roma wanda bawansa yana ciwo sosai har yana gab da mutuwa. Wannan babban sojan Roma kuwa yana ƙaunar bawan nan sosai.
3 Da ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu shugabannin Yahudawa domin su roƙe shi yă zo yă warkar da bawansa.
4 Shugabannin suka je wurin Yesu, suka roƙe shi sosai, suna cewa, “Wannan mutum ai, ya cancanci ka taimake shi,
5 gama yana ƙaunar mutanenmu, har ya gina mana majamiˈa.”
6 Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya yi kusa da gidan, babban sojan Roman nan ya aika da waɗansu abokansa su gaya wa Yesu, “Ya maigirma, kada ka dame kanka saboda ni! Ban ma isa har da za ka zo gidana ba.
7 Shi ya sa ban ma ga na isa in zo wurinka ba, amma ka yi magana kawai, yarona kuwa zai warke.
8 Gama ni ma a ƙarƙashin ikon wani nake, kuma da sojoji a ƙarƙashina, nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă je. Wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai yă zo. In na ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai yă yi.”
9 Da Yesu ya ji haka, sai mamaki ya kama shi. Sai ya juya ya ce wa mutanen da suke binsa, “Ina gaya muku, a cikin Israˈila ban taɓa samun mai bangaskiya mai ƙarfi kamar wannan ba!”
10 Da waɗanda aka aika suka koma gidan babban sojan Roma, sai suka sami bawan ya warke.
11 Ba da daɗewa ba, sai Yesu ya tafi wani garin da ake ce da shi Nayin, almajiransa da mutane da yawa kuma suka tafi tare da shi.
12 Da suka yi kusa da ƙofar shiga garin, sai ga waɗansu mutane suna fitowa da gawar wani saurayi, wanda shi kaɗai mamarsa ta haifa, mijinta kuma ya mutu. Mutane da yawa daga garin suna mata rakiya.
13 Da Ubangiji ya ga matar, sai ya ji tausayinta, sai ya ce mata, “Kada ki yi kuka!”
14 Sai ya je ya taɓa akwatin gawar, sai mutanen da suke riƙe da shi suka tsaya. Yesu ya ce, “Saurayi, na ce maka ka tashi!”
15 Sai wannan da ya mutu ya tashi ya zauna, ya fara magana. Yesu kuma ya miƙa shi ga mamarsa.
16 Sai tsoro ya kama su duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Lallai, wani babban annabi ya tashi a cikinmu! Allah ya zo domin yă ceci mutanensa!”
17 Labarin abin nan da Yesu ya yi, ya kai koˈina a cikin yankin Yahudiya da kewayenta.
18 Da almajiran Yohanna Mai Baftisma suka gaya masa dukan abubuwan nan, sai ya kira biyu daga cikinsu,
19 ya aike su wurin Ubangiji, su tambaye shi, “Kai ne wanda zai zo, ko mu sa ido ga wani?”
20 Da suka kai wurin Yesu, sai suka ce, “Yohanna Mai Baftisma ne ya aike mu, mu tambaye ka, ‘Ko kai ne mai zuwan nan, ko kuma mu sa ido ga wani?’ ”
21 A daidai lokacin nan kuwa, Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cututtukansu, da kuma daga mugayen ruhohi. Makafi da yawa kuma ya ba su ganin gari.
22 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku koma ku gaya wa Yohanna abin da kuka ji, kuka kuma gani, wato makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, masu cutar fatar jiki suna samun warkewa, kurame suna jin magana, ana tā da waɗanda suka mutu, ana kuma yi wa talakawa waˈazin labari mai daɗi.
23 Allah zai albarkaci kowa da bai yi shakkar bangaskiyar da yake da ita a kaina ba!”
24 Bayan waɗanda Yohanna ya aika suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron mutane magana game da Yohanna, yana cewa, “Me kuka je gani a daji? Kun je ganin doguwar ciyawar da iska take kaɗawa ne?
25 To, kallon me ya kai ku? Wani mai cin ado ne? Masu sa kayan tsada suna kuma zaman jin daɗi, ai, a gidan sarki suke.
26 To, wai kallon me kuka je yi? Annabi? I, ina gaya muku, ya ma fi annabi.
27 Gama game da Yohanna ne Rubutacciyar Maganar Allah ta ce, “ ‘Ga shi, na aiko manzona yă riga ka gaba, wanda zai shirya maka hanya kafin ka zo.’
28 “Ina gaya muku, a cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yohanna girma. Amma duk da haka wanda ya fi ƙanƙani duka a mulkin Allah ya fi shi.”
29 Duka wanda ya ji wannan, har da masu karɓar haraji, suka tabbata cewa hanyar Allah ita ce daidai, saboda su ne aka yi musu baftisma ta Yohanna.
30 Amma Farisiyawa da malaman Koyarwar Musa suka ƙi abin da Allah ya nufe su da shi, suka kuma ƙi Yohanna yă yi musu baftisma.
31 Yesu ya ci gaba da cewa, “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Yaya suke?
32 Su kamar yara ne da suke zama a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa, “ ‘Mun hura muku sarewa, kun ƙi ku yi rawa! Mun rera waƙar mutuwa, kun ƙi ku yi kuka!’
33 “Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin abinci, ba ya shan ruwan inabi, amma kuna cewa, ‘Ai, yana da aljani!’
34 Ɗan Mutum ya zo kuma yana ci, yana sha, kuna cewa, ‘Kun gan shi mai yawan ci da sha, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’
35 Duk da haka waɗanda suka yarda da hikimar Allah, suna nuna cewa tana da gaskiya.”
36 Wani Bafarisiye ya gayyaci Yesu cin abinci a gidansa, sai Yesu ya je ya zauna don cin abinci.
37 A wannan gari, akwai wata mace mai zunubi. Da ta ji cewa Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo wata ˈyar kwalabar da aka yi da dutsen onis cike da man ƙanshi mai tsada sosai.
38 Ta zo ta tsaya a bayansa, wajen ƙafafunsa, tana kuka. Da hawayenta ya fara zuba a ƙafafunsa, sai ta goge ƙafafun da gashinta, ta yi ta yin musu sumba, saˈan nan ta shafa musu man ƙanshin nan.
39 Da Bafarisiyen nan ya ga abin da macen nan take yi, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san kowace ce macen nan da take taɓa shi! Kuma da ya san cewa ita mai zunubi ce.”
40 Yesu ya ce wa Bafarisiyen nan, “Siman, ina da abin da zan faɗa maka.” Shi kuma ya ce, “Faɗa, malam.”
41 Yesu ya ce, “An yi wani mutumin da yake bin waɗansu mutane biyu bashi, ɗaya ana binsa yawan kuɗin da lebura zai samu cikin shekara ɗaya da rabi, ɗayan kuma yawan kuɗin da lebura zai samu cikin kwana hamsin.
42 Da suka gagara biya, sai ya yafe musu dukansu biyu. To, a ganinka wa zai fi ƙaunarsa?”
43 Siman ya ce masa, “A ganina, wanda aka yafe masa mai yawan ne.” Sai Yesu ya ce masa, “Yawwa! Ka faɗa daidai.”
44 Sai ya dubi macen, ya ce wa Siman, “Ka ga macen nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwa in wanke ƙafafuna ba, amma ta wanke ƙafafuna da hawayenta, ta kuma goge su da gashin kanta.
45 Ba ka sumbace ni da na shigo gidanka ba, amma tun shigowata a nan macen nan ba ta daina sumbar ƙafafuna ba.
46 Ba ka shafa mai a kaina ba, amma ita ta shafa man ƙanshi a ƙafafuna.
47 Saboda haka ina gaya maka, zunuban nan nata masu yawa an yafe mata su, gama ta yi ƙauna mai yawa. Wanda aka yafe wa kaɗan kuwa, ƙauna kaɗan yake nunawa.”
48 Sai ya ce wa macen, “An gafarta miki zunubanki.”
49 Mutanen da suke cin abinci tare da shi suka fara ce wa junansu, “Wane ne wannan, wanda har yana yafe zunubai?”
50 Sai Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki sauka lafiya.”