Hausa Bible
Luka 23
1 Sai dukan taron majalisa suka tashi suka kai Yesu gaban Bilatus.
2 Sai suka fara zarginsa suna cewa, “Mun sami wannan yana rikitar da mutanenmu, yana ce musu wai kada su biya wa Kaisar haraji. Yana kuma cewa wai shi ne Almasihu, sarki.”
3 Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce, “Ka faɗa haka.”
4 Sai Bilatus ya ce wa manyan firistoci da jamaˈa, “Ni kam, ban sami mutumin nan da wani laifi ba.”
5 Sai suka fara matsa masa lamba suna cewa, “Da koyarwarsa ne yake tā da hankalin mutane a dukan yankin Yahudiya. Ya fara tun daga Galili, yanzu kuma har nan wurin.”
6 Da Bilatus ya ji haka, sai ya yi tambaya, ya ce, “Shi mutumin Galili ne?”
7 Da ya ji cewa Yesu ya fito daga sashen da Hirudus yake mulki ne, sai ya aika da Yesu zuwa wurin Hirudus, gama a lokacin Hirudus ma yana Urushalima.
8 Hirudus ya yi murna sosai da ganin Yesu, gama tun dā ma yana marmari yă gan shi, gama ya riga ya ji labarinsa yana kuma fata yă ga wani abin mamakin da Yesu zai yi.
9 Sai Hirudus ya yi masa tambayoyi masu yawa, amma Yesu bai ce kome ba.
10 Sai manyan firistoci da malaman Koyarwar Musa suka zo gaba suka kawo zargi masu ƙarfi a kan Yesu.
11 Hirudus da sojojinsa suka yi masa renin wayo, suka yi masa baˈa, saˈan nan suka sa masa babbar riga, suka mai da shi wurin Bilatus.
12 A ranar nan ne Hirudus da Bilatus suka zama abokan juna, don tun dā ba sa so su ga juna.
13 Bilatus ya tara manyan firistoci, da shugabannin jamaˈa da mutane duka,
14 ya ce musu, “Kun kawo mini wannan mutum, wai yana rikitar da mutane. Yanzu na bincike shi a gabanku, ban same shi da wani laifin da kuka kawo a kansa ba.
15 Haka ma Hirudus. Shi ya sa ya dawo da shi nan wurinmu. Ba abin da mutumin nan ya yi da ya isa a kashe shi.
16 Saboda haka zan yi masa bulala in sake shi.”
17 A kowane Bikin Ƙetarewa kuwa Bilatus yakan saki mutum ɗaya daga kurkuku, wanda mutane suka roƙa.
18 Amma duk suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da shi, a saki mana Barabbas!”
19 Dā ma an sa shi Barabbas a kurkuku saboda laifin tashin hankalin da ya jawo a garin, har aka kashe mutum.
20 Sai Bilatus ya sāke yi musu magana, gama yana so yă saki Yesu.
21 Amma sai ihu suke ta yi, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”
22 Bilatus ya sāke ce musu sau na uku, “Don me? Wane laifi ne mutumin nan ya yi? Ni dai ban same shi da wani laifin da ya isa a kashe shi ba. Zan sa a yi masa bulala, a sake shi.”
23 Amma suka tsaya dam! Suna matsa masa lamba, cewa sai an kashe shi. A ƙarshe dai suka ci nasara.
24 Bilatus kuwa ya yanke shariˈar da suke so.
25 Ya saki mutumin da suka ce a sake wato, wannan da aka jefa a kurkuku a kan laifin tā da hankali da kuma kisan kai. Amma Bilatus ya ba da Yesu gare su su yi masa abin da suke so.
26 Da sojoji suna tafiya da Yesu, sai suka sadu da wani da ake ce da shi Siman, mutumin Sayirin, yana zuwa daga ƙauye. Suka cafke shi, suka sa masa gicciye yă ɗauka yă bi Yesu a baya.
27 Mutane da yawa sosai suka yi ta binsa, a cikinsu kuwa har da waɗansu matan da suke kuka, suna ihu dominsa.
28 Amma Yesu ya juya wurinsu, ya ce, “Matan Urushalima! Kada ku yi kuka saboda ni, ku yi kuka domin kanku da ˈyaˈyanku.
29 Gama lokaci yana zuwa da mutane za su ce, ‘Abin farin ciki ne ga matan da ba su taɓa haifuwa ba, waɗanda ba sa haifuwa, waɗanda kuma ba su goyi yara ba.’
30 A wannan lokaci ne, “ ‘Mutane za su ce wa duwatsu “Ku fāɗo a kanmu!” Za su kuma ce wa tuddai, “Ku rufe mu!” ’ ”
31 “Idan fa suna yin irin waɗannan ga ɗanyen itace, yaya ke nan zai zama in ya bushe?”
32 Aka kuma kai waɗansu mutum biyu masu laifi don a kashe su tare da Yesu.
33 Da suka kai wurin da ake ce da shi “Ƙoƙon Kai”, suka gicciye shi a nan, tare da masu laifin nan, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa.
34 Sai Yesu ya ce, “Uba, bari ka gafarta musu, gama ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba wa juna rigunansa ta wurin jefa ƙuriˈa.
35 Mutane suka tsaya suna kallo. Shugabannin kuma suka yi masa baˈa, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, yă ceci kansa mana, in shi ne Almasihun da Allah ya zaɓa!”
36 Sojojin ma suka yi masa baˈa ta wurin zuwa wurinsa suna miƙa masa ruwan tsami daga ˈyaˈyan inabi.
37 Suna kuma cewa, “In kai ne Sarkin Yahudawa, to, ceci kanka mana!”
38 Sama da shi kuma aka yi wani rubutu cewa, “WANNAN SHI NE SARKIN YAHUDAWA.”
39 Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye ya yi masa maganar reni, ya ce, “Shin, in ce kai ɗin nan ne Almasihu? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!”
40 Amma ɗayan ya tsawata wa wancan ya ce, “Ba ka ma tsoron Allah? Kai da ka sami hukunci daidai da shi?
41 Mu kam, daidai aka yi mana, domin muna samun ladan abin da muka yi ne. Amma shi fa, wane laifi ya yi?”
42 Ya kuma ce, “Ya Yesu, ka tuna da ni saˈad da ka shiga mulkinka!”
43 Yesu ya ce masa, “Hakika ina gaya maka, yau ɗin nan za ka zauna tare da ni a Firdausi.”
44 Wajen tsakar rana, duhu ya rufe dukan ƙasar, har zuwa ƙarfe uku na yamma.
45 Rana ta daina haske. Labulen da yake cikin Haikali kuma ya yage kashi biyu.
46 Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Uba! A cikin hannuwanka nake ba da ruhuna.” Da ya faɗa haka, sai ya ja numfashinsa na ƙarshe ya mutu.
47 Da sojan Roma wanda yake wurin ya ga abin da ya faru, sai ya yabi Allah yana cewa, “Lallai, wannan mutum marar laifi ne!”
48 Da mutanen da suka taru a nan don shan kallo suka ga abin da ya faru, sai dukansu suka koma gida suna bugun ƙirjinsu cikin baƙin ciki.
49 Duk mutanen da suka san Yesu, da kuma matan da suka biyo shi tun daga yankin Galili, suka tsaya da nisa suna kallo.
50 -
51 Akwai wani mutum mai suna Yusuf, wanda shi daga wani garin Arimatiya a cikin yankin Yahuda. Shi wani mutumin kirki ne, mai adalci kuma. Yana marmarin mulkin Allah yă zo. Shi kuma ɗaya ne daga cikin ˈyan majalisa na Yahudawa, amma bai yarda da su a kan abin da suka shirya suka kuma yi ba.
52 Sai ya je wurin Bilatus domin yă roƙa a ba shi jikin Yesu.
53 Sai ya sauko da jikin, ya nannaɗe shi a cikin yadin lilin, ya sa shi a wani kabarin da aka haƙa a jikin dutse, wanda ba a taɓa sa kowa a ciki ba.
54 Ranar Shiri ce kuwa, ya rage kaɗan a shiga Ranar Hutu ta Mako.
55 Matan da suka bi Yesu daga Galili suka tafi tare da Yusuf domin su ga inda kabarin yake da kuma yadda aka sa jikin Yesu.
56 Saˈan nan suka koma gida, suka shirya turare da man shafawa. Ranar Hutu ta Mako kuwa, suka huta kamar yadda Koyarwar Musa ta umarta.