Hausa Bible
Yahaya 6
1 Bayan wannan sai Yesu ya ƙetare Tekun Galili, wato Tekun Tibariya.
2 Sai mutane da yawa suka bi shi, domin sun ga alamun ban mamakin da yake yi wa masu ciwo.
3 Sai Yesu ya hau tudu ya zauna a can tare da almajiransa.
4 To, lokacin Bikin Ƙetarewa, wato bikin Yahudawa ya yi kusa.
5 Da Yesu ya ɗaga ido ya ga taro mai yawa suna ta zuwa wurinsa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayo isasshen abincin da mutanen nan za su ci?”
6 Yesu ya yi wa Filibus wannan tambaya ne domin dai yă gwada shi, gama Yesu ya riga ya san abin da zai yi.
7 Filibus ya amsa ya ce, “Ai, ko abinci na yawan kuɗin da lebura zai samu a ranaku ɗari biyu ma ba zai isa kowannensu yă sami kaɗan ba.”
8 Sai ɗaya daga cikin almajiran mai suna Andarawus, ɗanˈuwan Siman Bitrus, ya ce wa Yesu,
9 “Ga wani ɗan yaro nan da dunƙulen burodi biyar na garin bale da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?”
10 Yesu ya ce wa almajiransa, “Ku faɗa wa mutane su zauna.” A wannan wuri kuwa akwai ciyawa da yawa. Sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar.
11 Yesu ya ɗauki dunƙulen burodin, bayan da ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya rarraba wa mutanen da suke zaune, ya ba su duk abin da zai ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.
12 Da suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka ragu domin kada kome yă lalace.”
13 Sai almajiran suka tattara gutsattsarin burodin suka cika kwanduna goma sha biyu, wato gutsattsarin nan daga dunƙulen burodi biyar na bale nan waɗanda suka rage bayan da mutane suka ci.
14 Da jamaˈa suka ga wannan alamar ban mamakin da Yesu ya yi, sai suka ce, “Ba shakka, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya.”
15 Da Yesu ya gane mutanen suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan babban tudu shi kaɗai.
16 Da yamma ta yi, sai almajiran Yesu suka gangara zuwa teku.
17 A lokacin ne wuri ya fara duhu, kuma Yesu bai riga ya zo wurinsu ba tukuna. Sai almajiransa suka shiga jirgin ruwa suka fara ƙetare tekun zuwa Kafarnahum.
18 Sai tekun ta fara hauka saboda wata iska mai ƙarfi take busawa.
19 Bayan sun yi tuƙi wajen kilomita biyar ko shida, sai suka ga Yesu yana tafiya a kan ruwa, yana ta zuwa kusa da jirgin. Sai almajiran suka firgita.
20 Amma Yesu ya ce musu, “Ni ne, kada ku ji tsoro.”
21 Saˈan nan suka yarda suka karɓe shi cikin jirgin. Nan da nan jirgin ya kai wurin da za su.
22 Da gari ya waye sauran mutanen da suke zaune a ƙetaren tekun suka lura cewa dā ma jirgi ɗaya ne kurum ya zo wurin, suka kuma lura Yesu bai shiga cikin jirgin tare da almajiransa ba, almajiransa ne kaɗai suka tafi.
23 Amma akwai waɗansu jiragen da suka zo daga Tibariya suka tsaya kusa da wurin da mutanen suka ci burodi bayan da Yesu ya yi godiya ga Allah.
24 Da mutanen suka ga cewa Yesu da almajiransa ba sa nan a wurin, sai suka shiga jiragen ruwan, suka tafi Kafarnahum suna neman Yesu.
25 Da suka same shi a ƙetaren tekun, suka ce masa, “Malam, yaushe ka zo nan?”
26 Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne don kun ci burodi nan kun ƙoshi, amma ba domin kun gane alamun ban mamaki da na yi ba ne.
27 Kada ku yi wahalar aiki a kan neman abinci mai lalacewa, amma ku yi aiki a kan abincin da zai dawwama zuwa ga rai na har abada. Wannan shi ne abincin da Ɗan mutum zai ba ku. Domin a kan Ɗan Mutum ne Allah Uba ya riga ya sa alamar shaidarsa ta nuna yarda.”
28 Sai mutanen suka tambayi Yesu suka ce, “Me za mu yi don mu cika ayyukan da Allah yake so?”
29 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Wannan shi ne abin da Allah yake so ku yi, wato ku ba da gaskiya ga wanda ya aiko.”
30 Sai mutanen suka tambayi Yesu kuma suka ce, “To, wace alamar ban mamaki ce za ka yi domin mu gani mu ba da gaskiya gare ka? Me za ka yi?
31 Kakannin kakanninmu sun ci manna a daji, yadda yake a rubuce a cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, ‘Ya ba su abinci daga sama domin su ci.’ ”
32 Saˈan nan Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ba Musa ne ya ba ku abincin nan daga sama ba, Ubana ne yake ba ku abinci na gaskiya daga sama.
33 Ai, abincin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama yana ba duniya rai.”
34 Sai suka ce masa, “Maigirma, ka dinga ba mu irin wannan abinci kullum!”
35 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ni ne abinci mai ba da rai, wanda ya zo wurina ba zai ƙara jin yunwa ba, wanda ya gaskata da ni kuma ba zai taɓa jin ƙishin ruwa ba.
36 Amma kamar yadda dai na faɗa muku, kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.
37 Duk waɗanda Uba ya ba ni, za su zo wurina, wanda kuma ya zo wurina kuwa ba zan kore shi ba.
38 Gama na sauko daga sama, ba domin in yi nufina ba, sai dai in yi nufin wanda ya aiko ni.
39 Kuma nufin wanda ya aiko ni shi ne, kada in ɓatar da ko ɗaya daga cikin dukan waɗanda ya ba ni, amma dai in tashe su a ranar ƙarshe.
40 Domin wannan shi ne nufin Ubana cewa, duk wanda yake duban Ɗan, yake kuma gaskatawa da shi yana da rai na har abada, ni kuma zan tashe shi a ranar ƙarshe.”
41 Sai Yahudawa suka yi gunaguni game da Yesu domin ya ce, “Ni ne abincin da ya sauko daga sama.”
42 Yahudawan suka ce, “Ashe, wannan ba Yesu ne ba, ɗan Yusuf, wanda mun san duk babansa da mamarsa? To, yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko ne daga sama’?”
43 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku bar yin gunaguni a tsakaninku.
44 Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uba wanda ya aiko ni ne ya jawo shi, ni kuwa zan tā da wannan mutum a ranar ƙarshe.
45 An rubuta a cikin littattafan annabawa cewa, ‘Dukansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya a wurin Uban, yakan zo wurina.
46 Ba wanda ya taɓa ganin Uban sai dai wanda ya fito daga wurin Allah, shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban.
47 Hakika, ina gaya muku, duk wanda ya ba da gaskiya yana da rai na har abada.
48 Ni ne abinci mai ba da rai.
49 Kakannin kakanninku sun ci manna a daji, amma duk da haka suka mutu.
50 Amma ga abinci mai saukowa daga sama, domin duk wanda ya ci wannan abinci, ba zai mutu ba.
51 Ni ne abincin rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci wannan abinci, zai rayu har abada. Wannan abinci naman jikina ne, wanda zan bayar domin duniya ta sami rai.”
52 Sai Yahudawa suka shiga gardama mai zafi a tsakaninsu, suna cewa, “Yaya mutumin nan zai ba mu naman jikinsa mu ci?”
53 Sai Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, in ba kun ci naman jikin Ɗan Mutum kun kuma sha jininsa ba, ba ku da rai a cikinku ke nan.
54 Duk wanda yake cin naman jikina, yake shan jinina kuma, yana da rai na har abada, zan kuwa tashe shi a ranar ƙarshe.
55 Domin naman jikina abinci ne na gaskiya, jinina kuma, abin sha ne na gaskiya.
56 Duk wanda yake cin naman jikina, yake kuma shan jinina, yana rayuwa a cikina, ni kuwa a cikinsa.
57 Kamar yadda Uba mai rai ya aiko ni, saboda shi ne kuma nake rayuwa, haka ne kuma wanda ya mai da ni abincinsa zai rayu saboda ni.
58 Ni ne abincin da ya sauko daga sama. Kakannin kakanninku sun ci manna, amma duk da haka suka mutu, amma duk mutumin da ya ci wannan abinci zai rayu har abada.”
59 Yesu ya faɗa dukan waɗannan abubuwa ne a lokacin da yake koyarwa a cikin majamiˈa a Kafarnahum.
60 Da jin haka, sai da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan magana mai wuya ce, wa zai iya yă karɓe ta?”
61 Yesu kuwa da yake ya sani cewa almajiransa suna gunaguni a kan wannan koyarwa, sai ya ce musu, “Wannan koyarwa ta ɓata muku rai ne?
62 To, yaya ranku zai zama ke nan in kuka ga Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda ya fito?
63 Ruhu ne yake ba da rai. Jiki ba shi da ikon yin kome. Kalmomin da na faɗa muku Ruhu ne, da kuma rai.
64 Amma akwai waɗansunku da ba su ba da gaskiya ba.” Gama tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bashe shi.
65 Sai Yesu ya ƙara da cewa, “Shi ya sa na gaya muku cewa, ‘Babu wanda zai iya zuwa wurina, sai dai Uban ya ba shi iko.’ ”
66 Bayan wannan maganar da Yesu ya yi, sai da yawa daga cikin mutanen da suke binsa suka bar shi, suka kuma daina binsa.
67 Sai Yesu ya tambayi sha biyun nan ya ce, “Ku ma kuna so ku tafi ne?”
68 Siman Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ubangiji, wurin wane ne za mu je? Ai, kai ne kake da magana mai ba da rai na har abada.
69 Mu kuwa mun ba da gaskiya, mun kuma sani cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”
70 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Na zaɓi dukanku goma sha biyu, amma ɗayanku shaiɗan ne.”
71 Wato, yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyoti, don shi ne zai bashe shi, ko da yake shi ɗaya daga cikin sha biyun nan ne.