Hausa Bible
Yahaya 5
1 Bayan wannan, Yesu ya tafi Urushalima domin wani bikin Yahudawa.
2 A Urushalima kuwa akwai wani tafkin ruwa wanda ake kewaye shi da rumfuna guda biyar. Da Yahudanci ana ce da shi Betasda. Wannan tafki yana kusa da Ƙofar Tumaki ne.
3 A rumfuna nan ne marasa lafiya, da makafi, da guragu, da shanyayyu da yawa sun saba kwanciya.
4 Suna jira a motsa ruwan. Gama a lokaci-lokaci malaˈikan Ubangiji yakan sauko yă motsa ruwan. Duk kuwa wanda ya fara shiga bayan da aka motsa ruwan, sai yă warke daga duk irin ciwon da yake da shi.
5 A nan kuwa akwai wani mutumin da ya yi shekara talatin da takwas a cikin rashin lafiya.
6 Da Yesu ya gan shi kwance, ya kuma sani mutumin ya daɗe da wannan ciwo, sai Yesu ya ce wa mutumin, “Kana so ka warke?”
7 Mai ciwon ya amsa masa ya ce, “Maigirma, ai, ba ni da wanda zai taimake ni in shiga cikin tafkin lokacin da aka motsa ruwan. Idan na yi ƙoƙari in shiga, sai wani yă riga ni.”
8 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka ɗauki tabarmarka, ka yi tafiyarka!”
9 Nan da nan, mutumin ya warke, ya kuma ɗauki tabarmarsa ya tafi. Wannan abin ya faru a Ranar Hutu ta Mako wadda Yahudawa ba sa yin aiki.
10 Saboda haka Yahudawa suka ce wa mutumin da aka warkar, “Yau Ranar Hutu ne, kuma bisa ga Koyarwar Musa ba daidai ba ne ka ɗauki tabarmarka.”
11 Sai mutumin ya amsa musu ya ce, “Ai, wanda ya warkar da ni, shi ne ya ce mini in ɗauki tabarmata in yi tafiya.”
12 Suka tambaye shi suka ce, “Wane ne wannan mutumin da ya ce maka ka ɗauki tabarmarka ka yi tafiya?”
13 Mutumin da aka warkar ɗin kuwa bai san ko wane ne ma ya warkar da shi ba, domin akwai mutane da yawa a wurin, kuma Yesu ya ɓace cikin jamaˈa.
14 Bayan ɗan lokaci, Yesu ya same shi a cikin Haikali, ya ce masa, “Ka ga fa, ka warke! To, ka daina yin zunubi, domin kada wani abin da ya fi wannan muni yă same ka.”
15 Sai mutumin ya tafi ya gaya wa shugabannin Yahudawa cewa, Yesu ne ya warkar da shi.
16 Saboda haka suka fara tsananta wa Yesu, don dai yana yin irin waɗannan abubuwa a Ranar Hutu ta Mako.
17 Sai Yesu kuwa ya ce musu, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina yi.”
18 Wannan magana kuwa ya sa Yahudawa suka ƙara nema su kashe Yesu. Suka ce, “Ba don ma ya karya dokar Ranar Hutu ta Mako kawai ba, amma ya ce Allah Ubansa ne, wato ya mai da kansa daidai da Allah ke nan.”
19 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, Ɗan ba ya yin kome, shi kaɗai, sai dai abin da ya ga Uban yake yi. Domin duk abin da Uban yake yi, shi ne ma Ɗan yake yi.
20 Gama Uban yana ƙaunar Ɗan, yana kuma nuna masa duk abin da shi kansa yake yi, har ma zai nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan, domin ku yi mamaki.
21 Kamar dai yadda Uba yake tā da matattu ya kuma raya su, haka ma Ɗan yana ba da rai ga dai duk wanda ya ga dama.
22 Uba kuma ba ya yi wa kowa shariˈa, amma ya ba Ɗan ikon yin dukan shariˈa,
23 domin dukan mutane su girmama Ɗan, kamar yadda suke girmama Uban. Duk wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan.
24 “Hakika, ina gaya muku, duk mutumin da yake jin maganata, yana kuma ba da gaskiya ga wanda ya aiko ni, yana da rai na har abada. Ba za a yi masa hukunci ba, ya riga ya ƙetare mutuwa zuwa rai.
25 Hakika, ina gaya muku, lokaci yana zuwa, ya riga ya zo ma, da matattu za su ji muryar Ɗan Allah, waɗanda suka ji kuwa za su rayu.
26 Gama kamar yadda Uba da kansa tushen rai ne, haka ma ya sa Ɗansa yă zama tushen rai.
27 Ya kuma ba shi ikon yin shariˈa domin shi Ɗan Mutum ne.
28 Kada ku yi mamakin wannan magana, domin lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa,
29 su fito. Waɗanda suka yi abu mai kyau za su tashi, su rayu, amma waɗanda suka yi rashin gaskiya, za su tashi a kuwa yi musu hukunci.
30 Bāna iya yin kome ni kaɗai. Ina shariˈata ne yadda Allah ya faɗa mini in yi. Saboda haka shariˈata ta gaskiya ce, domin ba nufin kaina nake bi ba, amma nufin wanda ya aiko ni ne.
31 “Idan na yi wa kaina shaida, to, shaidata ba tabbatacciya ba ce.
32 Amma akwai wani wanda yake yin shaida a kaina, na kuma san shaidar da yake yi a kaina tabbatacciya ce.
33 Kun aiki mutane wurin Yohanna, shi kuwa ya shaida muku gaskiya.
34 Duk da haka ban dogara da shaidar mutum ba. Na dai faɗa haka ne domin ku sami ceto.
35 Yohanna fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki sosai da haskensa a ɗan lokaci kaɗan.
36 Amma ina da tawa shaida a kaina wadda ta fi shaidar da Yohanna ya bayar game da ni. Ayyukan da nake yi, waɗanda Ubana ya ba ni in yi, su ne abubuwan da suka zama shaidata, cewa Uba ne ya aiko ni.
37 Uban kuma wanda ya aiko ni shi da kansa ya zama shaidata. Ba ku taɓa jin muryarsa ba, ba ku kuma taɓa ganin yadda yake ba.
38 Kalmarsa ba ta zama a zuciyarku, domin ba ku ba da gaskiya ga wanda Uba ya aiko ba.
39 Kuna ta binciken Rubutacciyar Maganar Allah, don a tsammaninku za ku sami rai na har abada a cikinsu. Waɗannan Maganar Allah kuwa su ne suke ba da shaida a kaina.
40 Amma duk da haka kun ƙi zuwa wurina ku sami rai.
41 “Bāna karɓar yabo daga wurin mutane.
42 Amma fa na san ku, na kuma san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku.
43 Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku karɓe ni ba, amma idan wani ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi.
44 To, yaya za ku ba da gaskiya saˈad da kuke ƙoƙarin samun yabo daga junanku, amma ba ku yi ƙoƙarin samun yabon da yake fitowa daga wurin Allah wanda yake ɗaya kaɗai ba?
45 Kada ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke sa zuciya zai taimake ku.
46 Da a ce kun ba da gaskiya ga Musa, da kun ba da gaskiya gare ni, gama Musa ya rubuta game da ni.
47 Amma in kuwa ba ku gaskata da abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata da maganata?”