Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 15
1 Sai kuma waɗansu mutane suka zo Antakiya daga yankin Yahudiya suna koya wa ˈyanˈuwa masu bi, suna cewa, “Idan ba an yi muku kaciya kamar yadda alˈadar Musa take ba, ba za ku iya samun ceto ba.”
2 Ba ƙaramar gardama Bulus da Barnaba suka yi da mutanen nan a kan wannan magana ba. Sai aka sa Bulus da Barnaba da kuma waɗansu su je Urushalima wurin manzanni da dattawan jamaˈar masu bi domin su tattauna a kan wannan magana.
3 Jamaˈar masu bi ta raka su, suka tafi, suka bi ta ƙasar Finikiya da Samariya, suna ba da labarin yadda waɗanda ba Yahudawa ba suka ba da gaskiya. Wannan ya sa duk masu bi suka yi farin ciki sosai.
4 Da suka isa Urushalima, dukan jamaˈar masu bi, da manzanni, da dattawan jamaˈar masu bi suka yi musu maraba. Sai Bulus da Barnaba kuma suka ba da rahoton duk abin da Allah ya yi ta wurinsu.
5 Amma waɗansu masu bi, ˈyan ƙungiyar Farisiyawa, suka tashi tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa masu bi waɗanda ba Yahudawa ba kaciya, a kuma sa su dole su bi Koyarwar Musa.”
6 Manzannin da dattawan jamaˈar masu bi suka taru domin su tattauna a kan wannan magana.
7 Bayan da aka yi ta gardama sosai, sai Bitrus ya tashi tsaye ya ce musu, “ˈYanˈuwa, kun sani tun tuni Allah ya zaɓe ni a cikinku, cewa ta wurina ne waɗanda ba Yahudawa ba za su ji labari mai daɗi, su kuma ba da gaskiya.
8 Allah kuwa wanda ya san zuciyar kowa, ya nuna cewa ya karɓe su da ya ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.
9 Kuma bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsabtace zukatansu ta wurin bangaskiyarsu.
10 Saboda haka don me kuke gwada Allah ta wurin sa wa almajiran nan gungumen da yake danne su, wato dokokin da mu da kakanninmu duka ba mu iya ɗaukawa ba?
11 Amma mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne mun sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”
12 Sai duk taron mutanen suka yi shiru, suka saurari Barnaba da Bulus saˈad da suka ba da labarin alamu da ayyukan ban mamakin da Allah ya yi ta wurinsu a cikin waɗanda ba Yahudawa ba.
13 Bayan da suka gama magana, sai Yakub ya amsa ya ce, “ˈYanˈuwa, ku saurare ni.
14 Siman ya ba da labari yadda Allah ya fara nuna ƙauna ga waɗanda ba Yahudawa ba, ta wurin keɓe wata jamaˈa daga cikinsu ta zama tasa.
15 Wannan kuwa ya yi daidai da maganar annabawa yadda yake a rubuce cewa,
16 “ ‘Bayan haka zan dawo in sāke gina gidan Dawuda da ya rushe. Daga zamansa kufai, zan sāke gina shi, in kuma sabunta shi.
17 Ta haka ragowar mutane za su neme ni, ni Ubangiji, waɗanda ba Yahudawa ba da na zaɓa su zama nawa.
18 Haka Ubangiji ya faɗa, shi da ya bayyana waɗannan abubuwa tun zamanin dā.’ ”
19 “Saboda haka na ga bai kamata mu matsa wa waɗanda ba Yahudawa ba waɗanda suke juyowa ga Allah.
20 Sai dai mu rubuta musu wasiƙa mu gaya musu kada su ci abincin da aka miƙa wa gumaka, kada su yi lalata ko su ci naman dabbar da aka murɗe, da kuma nama da jini.
21 Gama tun zamanin dā, a kowane gari akwai masu yin waˈazi da Koyarwar Musa, ana kuma karanta ta a majamiˈu kowace Ranar Hutu ta Mako.”
22 Sai manzannin da dattawan jamaˈar masu bi, tare da dukan ˈyan jamaˈar masu bi, suka ga ya yi kyau su zaɓi waɗansu daga cikinsu, su aike su zuwa Antakiya tare da Bulus da Barnaba. Sai suka zaɓi Yahuda, wanda ake ce da shi Barsaba, da kuma Sila, waɗanda su shugabanni ne cikin masu bi.
23 Suka ba su wasiƙar da take cewa, “Daga ˈyanˈuwanku manzanni da dattawan jamaˈar masu bi, zuwa ga masu bi waɗanda asalinku ba Yahudawa ba ne, a Antakiya da ƙasar Suriya da ta Kilikiya. Muna gaisuwa.
24 “Mun sami labari cewa waɗansu daga cikinmu sun tayar muku da hankali da maganganunsu, suna rikitar da ku, ko da yake ba mu ba su umarni su yi haka ba.
25 Domin haka, bayan da muka tattauna sai muka ga ya yi kyau mu zaɓi waɗansu mu aika muku su, tare da abokanmu, wato Barnaba da Bulus,
26 waɗanda suka ba da ransu saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu.
27 Domin haka mun aiko muku Yahuda da Sila. Su da kansu za su tabbatar muku waɗannan abubuwa da bakinsu.
28 “Gama Ruhu Mai Tsarki ya ga ya yi kyau, haka kuma muka ga ya yi kyau, kada a sa muku wani nauyi fiye da na waɗannan abubuwan da suka zama dole,
29 wato, ku kiyaye kanku daga abin da aka miƙa wa gunki, da cin nama tare da jini, da cin naman dabbar da aka murɗe, da kuma lalata. Idan kun kiyaye kanku daga waɗannan abubuwa, kun yi abin da yake da kyau ke nan. “Ku huta lafiya.”
30 Sai aka aike su, suka tafi Antakiya. Da suka tara jamaˈar masu bi, sai suka ba da wasiƙar.
31 Da jamaˈar suka karanta wasiƙar kuwa, suka yi farin ciki saboda ƙarfafawar da suka samu.
32 Yahuda da Sila kuma, domin su annabawa ne, suka yi wa ˈyanˈuwa gargaɗi da maganganu masu yawa, suka kuma ƙarfafa su.
33 Bayan da suka yi ˈyan kwanaki a wurin, sai aka sallame su lafiya, suka komo wurin waɗanda suka aiko su.
34 Amma Sila ya ga ya yi kyau yă zauna a nan tukuna.
35 Bulus da Barnaba kuwa suka yi ˈyan kwanaki a Antakiya. Su da waɗansu mutane da yawa suna koyarwa suna kuma yin shelar kalmar Ubangiji.
36 Bayan ˈyan kwanaki, Bulus ya ce wa Barnaba, “Zo mu koma duk garuruwan da muka yi shelar kalmar Ubangiji a dā, mu ziyarci ˈyanˈuwa, mu ga yadda suke.”
37 Barnaba ya so su ɗauki Yohanna wanda ake ce da shi Markus yă tafi tare da su.
38 Amma Bulus ya ga bai yi kyau su tafi da Markus ba saboda a dā ya bar su a ƙasar Famfiliya, ya kuma ƙi yă ci gaba da yin aiki tare da su.
39 Rashin yardar ya yi zafi har ya kai su ga rabuwa. Barnaba ya ɗauki Markus, suka shiga jirgin ruwa zuwa Sayifurus.
40 Amma Bulus ya zaɓi Sila, suka tashi, bayan da masu bi suka miƙa su ga alherin Ubangiji yă kiyaye su.
41 Suka bi ta ƙasashen Suriya da Kilikiya, suna ƙarfafa dukan jamaˈar masu bi.