Hausa Bible
Romawa 9
1 Ina faɗin gaskiya cikin Almasihu, ba ƙarya nake yi ba. A ciki tunanin zuciyata ina da tabbaci bisa ga shaidar Ruhu Mai Tsarki game da wannan cewa
2 ina da baƙin ciki ƙwarai, da kuma damuwa a kullum cikin zuciyata.
3 Da ma a ce ni kaina an laˈanta ni, an kuma kawar da ni daga Almasihu saboda ceton ˈyanˈuwana, wato mutanen kabilata!
4 Waɗannan kuwa su ne Israˈilawa. Su ne Allah ya mai da su ˈyaˈyansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya yi yarjejeniya da su, ya ba su Koyarwar Musa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawaran.
5 Asalinsu kuwa daga kakannin kakannin nan ne waɗanda aka san su sosai. Almasihu kuwa, bisa ga mutuntakarsa, shi daga kabilarsu ne. Bari Allah mai mulki a kan kome, yă karɓi yabo har abada. Amin.
6 Ba wai kalmar Allah ta kāsa ba. Gama ba duk waɗanda asalinsu Israˈila ne suke na Israˈila ba.
7 Kuma ba duk waɗanda suke daga zuriyar Ibrahim ne ainihin ˈyaˈyan Ibrahim ba. A maimakon haka Allah ya ce wa Ibrahim, “Ishaku shi ne mutumin da ta wurinsa ne za a ci gaba da kira zuriyarka.”
8 Wato, ˈyaˈyan da aka samu ta haifuwar jiki ba su ne ˈyaˈyan Allah ba, sai dai ˈyaˈyan da aka samu ta cikawar alkawari, su ne akan ce da su ˈyaˈya na gaske.
9 Gama ga abin da Allah ya ce a lokacin da ya yi wa Ibrahim alkawari, “A saˈad da lokaci ya cika zan komo, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.”
10 Akwai wani misali kuma. ˈYaˈyan Rebeka suna da baba ɗaya ne, wato ubanmu Ishaku.
11 -
12 Amma kafin a haifi yaran nan biyu, Allah ya faɗa wa Rebeka cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.” Wannan ya faru kafin ma su aikata wani abu mai kyau, ko marar kyau. Allah ya faɗa haka domin yă zama cewa, wanda za a zaɓa za a zaɓe shi ne bisa ga nufin Allah, ba wai saboda ayyuka ba, sai dai bisa ga kiran Allah.
13 Kamar yadda yake a rubuce cikin Maganar Allah cewa, “Na ƙaunaci Yakub, na kuwa ƙi Isuwa.”
14 To, me za mu ce? Allah bai yi daidai ba ke nan? Ina! Ko kaɗan!
15 Gama Allah ya ce wa Musa, “Ga wanda zan nuna wa jinƙai, zan nuna masa jinƙai. Ga wanda zan nuna wa tausayi, zan nuna masa tausayi.”
16 Wato, wannan bai dogara ga son mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah kawai.
17 Gama Rubutacciyar Maganar Allah ta ce wa Firˈauna, “Na tashe ka ka zama sarki da nufi cewa in nuna ikona ta wurinka, a kuma sanar da sunana cikin duniya duka.”
18 Ta haka Allah yakan nuna jinƙai ga wanda yake so yă nuna masa jinƙai, yakan kuma taurara zuciyar wanda yake so yă taurara masa zuciya.
19 Waninku zai iya ce mini, “To, idan haka ne, me ya sa Allah yana ganinmu da laifi har yanzu? Wane ne zai iya ƙin yarda da nufin Allah?”
20 Amma wane ne kai, ya mutum, da har za ka yi musū da Allah? Abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, “Me ya sa ka gina ni haka?”
21 Ai, mai ginin tukwanen laka yana da iko yă yi amfani da laka yadda yake so. Yana iya yin amfani da dunƙule guda na laka yă yi waɗansu tukwane saboda aiki mai daraja, waɗansu kuma saboda aiki marar daraja.
22 Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa, yă kuma bayyana ikonsa a fili. Amma fa cikin haƙuri sosai ya jimre da waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda Allah ya keɓe ga halakarwa.
23 Haka kuma ya so yă bayyana yalwar ɗaukakarsa ga waɗanda ya nuna musu jinƙansa, waɗanda ya shirya tun da farko domin ɗaukakarsa.
24 Wato, mu ke nan, mu waɗanda Allah ya kira, ba daga cikin Yahudawa kawai ba, amma har daga cikin waɗanda ba Yahudawa ba ma.
25 Kamar yadda aka faɗa a littafin Hosiya cewa, “Su waɗanda ba mutanena ba ne zan ce da su ‘Mutanena’. Kuma alˈummar da ban ƙaunace ta ba zan ce da ita ‘Wadda nake ƙauna.’ ”
26 Kuma, “A daidai inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba’, a wurin ne za a ce da su ‘ˈyaˈyan Allah Mai Rai.’ ”
27 Game da Israˈila kuwa annabi Ishaya ya ɗaga murya ya ce, “Ko da yake mutanen Israˈila sun yi yawa, yawansu kamar yashi a bakin teku, duk da haka ragowa kaɗan ne daga cikinsu kawai za a cece su.
28 Gama Ubangiji zai aikata hukuncinsa a duniya gaba ɗaya, ba da ɓata lokaci ba.”
29 Kamar yadda Ishaya ya yi annabci a dā cewa, “Da ba don Ubangiji Mai Runduna ya bar mana zuriya ba, da mun zama kamar Sodom, da an mai da mu kamar Gomora.”
30 To, yaya ke nan? Ai, waɗanda ba Yahudawa ba waɗanda ba su yi ƙoƙari su sami adalcin Allah ba, sun samu. Adalcin nan da suka samu kuwa irin wanda ake samuwa ta bangaskiya ne.
31 Amma Israˈilawa waɗanda suka yi ƙoƙarin neman hanyar adalcin Allah ta wurin bin Koyarwar Musa, ba su samu ba.
32 Me ya sa haka? Domin ba ta hanyar bangaskiya ne suka neme shi ba, sai dai ta hanyar aikata aikin lada. Sai suka yi tuntuɓe da “dutsen nan mai sa tuntuɓe.”
33 Kamar yadda yake a rubuce a cikin Maganar Allah cewa, “Ga shi, ina kafa dutse a Sihiyona, dutse mai sa tuntuɓe, dutse mai sa mutane su fāɗi. Amma duk mai ba da gaskiya gare shi ba zai sha kunya ba.”