Hausa Bible
Romawa 8
1 Saboda haka, babu wani hukuncin mutuwa yanzu a kan waɗanda suke na Almasihu Yesu.
2 Gama ta wurin Almasihu Yesu ƙaˈidar Ruhun nan mai ba da rai ta ˈyantar da ni daga ƙaˈidar zunubi da mutuwa.
3 Gama abin da Koyarwar Musa ba ta iya aikatawa ba saboda kāsawar halin mutuntaka, shi ne abin da Allah ya aikata. Allah kuwa ya aiko da Ɗansa ɗaya tak da kamannin jikin nan namu mai zunubi domin yă zama hadaya saboda zunubi, a kuma rushe ikon zunubi cikin jiki.
4 Allah ya yi wannan ne domin duk ayyukan adalcin da Koyarwar ta ce a yi su sami cikawa a gare mu, mu da ba rayuwar halin mutuntaka muke yi ba, sai dai ta Ruhu.
5 Masu rayuwar halin mutuntaka sukan mai da hankalinsu ga shaˈanin jiki ne, amma masu rayuwar Ruhu sukan mai da hankalinsu ga abin da Ruhu yake so ne.
6 Mai da hankali ga shaˈanin jiki yakan kawo mutuwa, amma mai da hankali ga Ruhu yakan kawo rai da salama.
7 Duk wanda ya mai da hankalinsa ga shaˈanin jiki ya zama abokin gāban Allah ke nan, gama ba ya miƙa kai ga bin Koyarwar Allah, ba kuwa zai iya ba.
8 Masu rayuwar halin mutuntaka ba dama su faranta wa Allah rai.
9 Ku kam ba rayuwar halin mutuntaka kuke yi ba, sai dai ta Ruhu, idan Ruhun Allah yana zaune a zukatanku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, shi ba na Almasihu ba ne.
10 Idan Almasihu yana zama cikinku, ko da yake jikinku yana hanyar mutuwa saboda zunubi, Ruhun Allah yana rayar da ku saboda Allah ya karɓe ku a matsayin masu adalci.
11 Idan kuma Ruhun Allah, wanda ya tā da Yesu daga matattu yana zama a zukatanku, to, shi wanda ya tā da Almasihu daga matattu zai ba da rai ga jikinku mai mutuwa ta wurin Ruhunsa wanda yake zama a zukatanku.
12 Saboda haka, ˈyanˈuwa, muna da hakki, amma ba na yin rayuwar da halin mutuntakarmu yake so ba.
13 Domin idan rayuwar halin mutuntaka kuke yi, za ku mutu. Amma idan ta ikon Ruhu kuka kashe halin yin zunubi, za ku rayu.
14 Gama waɗanda Ruhun Allah yake bishe su, su ˈyaˈyan Allah ne.
15 Gama Ruhun da aka ba ku ba na bauta ba ne yadda za ku sāke zama cikin tsoro. Aˈa, Ruhun nan na zaman ˈyaˈyan Allah ne, kuma ta wurin Ruhun ne muke kira ga Allah, mu ce da shi “Abba! Uba!”
16 Ruhun Allah da kansa tare da ruhunmu yana tabbatar cewa mu ˈyaˈyan Allah ne.
17 Ashe, tun da yake mu ˈyaˈya ne, mun zama masu cin gādo ke nan. Wato, mu masu cin gādon albarkun Allah da kuma abokan gādo tare da Almasihu ne, idan kuwa mun sha wahala tare da Almasihu, domin kuma a ɗaukaka mu tare da shi.
18 Ai, na tabbata cewa ba yadda za a kwatanta wahalolin da muke sha a wannan zamani da ɗaukakar da za a bayyana mana nan gaba.
19 Dukan halitta tana marmari sosai, tana jiran Allah yă bayyana ˈyaˈyansa.
20 Gama an sa halitta ta kāsa kai ga manufarta, wannan kuwa ba bisa ga nufin halitta da kanta ba ne, sai dai domin haka ne Allah ya so. An yi wannan da sa zuciya
21 cewa halitta da kanta za ta sami tsira daga bautar da take wa ruɓewa, za ta kuma sami ˈyancin nan na ɗaukakar da za a yi wa ˈyaˈyan Allah.
22 Mun dai san cewa har wa yau dukan halitta tana nishi kamar yadda mace mai jin zafin haifuwa takan yi.
23 Ba halitta kaɗai take nishi ba, har da mu ma. Mu da mun riga mun sami Ruhu Mai Tsarki wanda shi ne kyauta ta farko ta abubuwan da aka ba mu, muna nishi a ranmu, muna jira da marmari sosai don Allah yă mayar da mu cikakkun ˈyaˈyansa, yă kuma fanshi jikin nan namu.
24 Gama ta sa zuciyar nan ne aka cece mu. Amma idan mun riga mun ga abin da muke sa zuciya a kai, ai, wannan ba sa zuciya kuma ba ke nan. Wane mutum yake sa zuciya ga abin da ya riga ya samu?
25 Amma idan muna sa zuciya ga abin da ba mu riga mun samu ba, ai, mukan jira, muna haƙuri.
26 Haka kuwa Ruhu yake yi mana taimako cikin kāsawarmu. Ba mu san yadda ya kamata mu yi adduˈa ba, amma Ruhu da kansa yana roƙon Allah a madadinmu tare da nishe-nishe waɗanda kalmomi ba za su iya bayyana ba.
27 Allah kuma, wanda shi ne mai bincika zuciyar mutum, ya san duk nufin Ruhu, domin Ruhu yana yin roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah ne.
28 Mun dai san cewa a cikin dukan kome Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke yi masa ƙauna ne, wato, waɗanda aka kira su bisa ga nufinsa.
29 Gama waɗanda Allah ya riga ya sani tun tuni, ya kuma ƙaddara su su ɗauki kamannin Ɗansa, domin yă zama na fari a cikin ˈyanˈuwa masu yawa.
30 Waɗanda Allah ya ƙaddara kuwa su ne ya kira. Waɗanda ya kira, su ne ya mai da su marasa laifi a gabansa. Waɗanda aka mai da su marasa laifi a gabansa kuwa, su ne ya kuma ɗaukaka.
31 To, me za mu ce game da wannan batu? Idan Allah yana tare da mu, wa ya isa yă yi gāba da mu?
32 Allah kuwa bai hana mana Ɗansa ba, amma ya miƙa shi saboda mu duka. Ashe, shi Allahn da ya riga ya ba mu Ɗansa ba zai ba mu duk sauran abubuwa hannu sake ba?
33 Wane ne zai kawo ƙara a kan waɗanda Allah ya zaɓa? Ai, Allah da kansa ne yake mai da su su zama marasa laifi a gabansa.
34 Wane ne ya isa yă yi wa mutum hukuncin mutuwa? Almasihu Yesu wanda ya mutu, ko kuwa a ce, wanda aka tā da shi daga matattu, wanda yana kuma zama a hannun dama na Allah, shi ne kuwa yana roƙon Allah a madadinmu.
35 Wane ne zai iya raba mu da ƙaunar da Almasihu yake yi mana? Azaba ce, ko wuya, ko tsanani, ko yunwa, ko rashi, ko hatsari, ko mutuwa?
36 Kamar yadda Rubutacciyar Maganar Allah ta ce, “Saboda kai muke fuskantar mutuwa kullum, an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”
37 Ai! A cikin dukan waɗannan alˈamura mun wuce a ce da mu masu nasara kawai, wannan kuwa ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu ne.
38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko malaˈiku ko aljanu, ko halin yanzu ko na nan gaba, ko ikoki iri-iri,
39 ko tsawo ko zurfi, ko wani abu dabam a dukan halitta, duk ba su isa ba sam su raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu.