Hausa Bible
Romawa 14
1 Ku karɓi mutumin da bangaskiyarsa ba ta yi ƙarfi ba, amma kada ku neme shi da laifi idan raˈayinsa dabam yake da naku.
2 Bangaskiyar wani mutum za ta yarda masa yă ci duk abin da ya ga dama, amma mutumin da ba shi da ƙarfi cikin bangaskiyarsa, sai kayan lambu kawai yake ci.
3 Mutumin da yake cin duk irin abincin da ya ga dama kada yă rena shi wanda ba ya cin kowane irin abinci. Kuma wanda ba ya cin kowane irin abinci, kada yă ɗora laifi a kan wanda yake cin kowane irin abinci, don Allah ya riga ya karɓe shi.
4 Kai wane ne da za ka ɗora laifi a kan bawan wani? Ko bawan ya yi aiki mai kyau, ko ya kāsa, ai, wannan ruwan maigidansa ne. Hakika za a ƙarfafa shi yă tsaya, gama Ubangiji ya iya sa shi yă yi nasara.
5 Wani yakan ga wata rana da muhimminci fiye da sauran ranaku. A ganin wani kuwa dukan ranaku daidai ne. Kowa dai yă sami nasa cikakken tabbaci a cikin zuciyarsa.
6 Duk mai ganin wata rana da muhimminci yana yin haka ne domin a girmama Ubangiji. Duk mai cin kowane irin abinci yana yin haka ne domin a girmama Ubangiji, gama yakan ba da godiya ga Allah saboda abincin. Duk wanda ba ya cin kowane irin abinci shi ma yana yin haka ne domin a girmama Ubangiji, gama shi ma yakan yi wa Allah godiya.
7 A cikinmu, ba domin amfanin kansa mutum yake rayuwa ba. Ba domin amfanin kansa kuma yake mutuwa ba.
8 Idan muna rayuwa, saboda Ubangiji ne muke yi, in kuma mutuwa za mu yi, saboda Ubangiji ne muke yi. Saboda haka ko rayuwa ne muke yi ko mutuwa, mu na Ubangiji ne.
9 Gama Almasihu ya mutu ya kuma tashi da rai domin yă zama Ubangiji na waɗanda suke matattu da kuma na waɗanda suke masu rai.
10 Kai fa, me ya sa kake ganin ɗanˈuwanka da laifi? Kai kuma me ya sa kake rena ɗanˈuwanka? Dukanmu dai za mu tsaya a gaban Allah wanda shi ne mai yi mana shariˈa.
11 Gama a rubuce yake cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, “Hakika, da yake ni ne Ubangiji Allah Mai Rai, na ce, ‘Kowace gwiwa za ta durƙusa a gabana, kowane harshe zai shaida cewa ni ne Allah.’ ”
12 To, kowane ɗayanmu zai ba da lissafin rayuwarsa ga Allah.
13 Saboda haka sai mu daina halin nan na ganin laifin juna. A maimakon haka sai kowa yă ɗauki niyya cewa ba zai zama dalilin tuntuɓe ko abin sa zunubi ga ɗanˈuwansa ba.
14 Na sani, ina kuma da cikakken tabbaci cikin Ubangiji Yesu cewa babu wani abu wanda yake da ƙazanta a asalinsa. Amma idan wani ya ɗauka cewa wani abu mai ƙazanta ne, to, a gare shi ne abin yake da ƙazanta.
15 Idan abin da kana ci ya kawo wa ɗanˈuwanka damuwa, ba zaman ƙauna kake yi ba ke nan. Kada abincin da kake ci yă zama hanyar lalatar da ɗanˈuwanka wanda Almasihu ya mutu dominsa.
16 Kada abin da yake mai kyau a ganinka yă zama abin zargi ga waɗansu.
17 Gama mulkin Allah ba zancen ci da sha ba ne, amma zancen adalci ne, da salama, da farin ciki a cikin Ruhu Mai Tsarki.
18 Kuma duk wanda yake yi wa Almasihu bauta ta wannan hanya, shi mai faranta wa Allah rai ne, mai samun yarda kuma a wajen mutane.
19 Saboda haka bari mu yi iyakacin ƙoƙarinmu don mu aikata abin da zai kawo salama da ƙarfafawar juna.
20 Kada ku rushe aikin Allah saboda shaˈanin cin abinci. Lallai kowane irin abinci marar ƙazanta ne, amma mugun abu ne idan abincin da ake ci ya zama abin sa wa wani tuntuɓe.
21 Ya fi kyau kada ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko ka aikata kowane irin abu idan zai sa ɗanˈuwanka yă fāɗi.
22 Bari duk raˈayin da kake da shi game da wannan shaˈani yă kasance tsakaninka da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa ba ta ba shi laifi ba, game da abin da shi da kansa ya ɗauka cewa mai kyau ne.
23 Amma mutumin da yake da shakka a kan abin da yake ci, yana jawo wa kansa hukuncin Allah ne idan ya ci, don halin nan da yake yi bai dogara ga bangaskiya ba. Kuma duk abin da bai dogara ga bangaskiya ba, zunubi ne.