Skip to content

Hausa Bible

Matiyu 13

1 A ranar nan Yesu ya fita daga gidan, ya je ya zauna a bakin teku.

2 Taron mutane da yawa sosai suka taru kewaye da shi, har sai da ya shiga jirgin ruwa ya zauna, taron mutanen kuma suka tsaya a bakin tekun.

3 Sai ya gaya musu abubuwa da yawa ta wurin misalai, ya ce, “Wani manomi ya je gona domin yă yi shuka.

4 Yana cikin yafa iri ke nan, sai waɗansu iri suka fāɗi a kan hanya, sai tsuntsaye suka zo suka cinye su.

5 Waɗansu kuma suka fāɗi a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa sosai. Suka tsiro da sauri saboda ƙasar wurin ba zurfi.

6 Da rana ta yi zafi sai ta ƙone su, har suka bushe, gama ba su da saiwa sosai.

7 Waɗansu kuma suka fāɗi a wurin da akwai ƙaya, sai ƙayar ta tashi ta sha ƙarfinsu.

8 Waɗansu kuma suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi tsaba ɗari-ɗari, waɗansu sittin-sittin, waɗansu kuma talatin-talatin.

9 Bari mai kunnen ji, yă ji.”

10 Sai almajiran Yesu suka zo suka ce masa, “Don me kake yi musu magana da misalai?”

11 Ya amsa musu ya ce, “Ku dai an yarda muku ku gane asirin mulkin sama, amma su ba a ba su ba.

12 Gama wanda yake da abu za a ƙara masa har yă yalwata sosai, amma wanda ba shi da kome, za a karɓi ɗan kaɗan ɗin da yake da shi.

13 Abin da ya sa nake yi musu magana da misalai shi ne, “ ‘Gama ko sun duba ba sa gani, ko sun saurara ba sa ji. Ba sa kuma ganewa.’

14 “Lallai annabcin Ishaya ya cika a kansu cewa, “ ‘Za ku yi ta ji kam, amma ba za ku gane ba sam, Za ku yi ta dubawa kuma, amma ba za ku fahimta ba sam.

15 Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri, kunnuwansu kuma ba sa ji. Sun kuma rufe idanunsu, domin kada su gani da idanunsu, kada kuma su ji da kunnuwansu, domin kada su gane a zuciyarsu, har su juyo wurina in warkar da su.’

16 “Idanunku masu albarka ne gama suna gani. Kunnuwanku ma haka gama suna ji.

17 Hakika ina gaya muku, annabawa da masu adalci da yawa sun so su ga abin da kuke gani, amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”

18 “To, ga abin da misalin mai shuka yake nufi.

19 Idan mutum ya ji kalmar mulkin saˈan nan bai gane ba, Shaiɗan yakan zo yă ƙwace abin da aka shuka a cikin zuciyar mutumin. Wannan shi ne irin da ya fāɗi a kan hanya.

20 Irin da ya fāɗi a wurin da yake da duwatsu kuwa, shi ne kwatancin mutum wanda da zarar ya ji kalmar Allah, sai yă karɓa da farin ciki.

21 Amma da yake ba shi da tushe, bai daɗe sosai ba. Saˈad da azaba ko tsanani ya tashi saboda wannan kalmar Allah, sai mutumin yă ja da baya.

22 Irin da ya fāɗi a wurin da akwai ƙaya kuma, shi ne kwatancin mutumin da idan ya ji kalmar Allah, sai damuwar duniya da son arziki su hana kalmar girma, har ta zama ba ta da amfani.

23 Irin da ya fāɗi a ƙasa mai kyau kuma, shi ne kwatancin mutumin da idan ya ji kalmar Allah ya kuma gane ta, sai yă yi amfani da ita, har ya yi riba, wani ɗari-ɗari, wani sittin-sittin, wani kuma talatin-talatin.”

24 Yesu ya sāke ba su wani misali ya ce, “Za a iya kwatanta mulkin sama da mutumin da ya shuka iri mai kyau a gonarsa,

25 amma lokacin da kowa yake barci, sai abokin gābansa ya je ya shuka wata irin ciyawa a gonar alkamar, ya tafi abinsa.

26 Da shukar ta tashi ta yi tsaba, sai ciyawar ma ta tashi.

27 Sai bayin maigidan suka zo suka ce masa, ‘Maigida, ashe, ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? To, yaya duk ciyawa ta fito a wurin?’

28 “Ya ce musu, ‘Abokin gābana ne ya yi wannan.’ “Bayin suka ce, ‘Kana so mu je mu cire ciyawar?’

29 “Amma ya ce, ‘Aˈa, kada garin cire ciyawar ku cire tare da alkamar.

30 Bari dukansu su yi girma tare har lokacin girbi, a lokacin girbin zan gaya wa masu girbin su fara cire ciyawar su tara, su ɗaɗɗaure, a ƙone, amma a tara alkamar a zuba a rumbuna.’ ”

31 Yesu ya sāke ba su wani misali, ya ce, “Mulkin sama kamar ƙwayar mastad ne wanda wani mutum ya ɗauka ya shuka a gonarsa.

32 Ita ce ta fi ƙanƙanta cikin sauran iri, amma idan ta yi girma, sai ta fi duk sauran ganyaye, ta zama babban itace, har ma tsuntsaye su yi gidansu a kan rassansa.”

33 Yesu ya sāke ba su wani misali, ya ce, “Mulkin sama kamar yisti yake, wanda wata mace ta ɗauka ta kwaɓa da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”

34 Yesu ya gaya wa taron mutanen duk waɗannan abubuwa da misalai. Ba ya gaya musu wani abu sai tare da misali.

35 Wannan kuwa domin a cika abin da annabi Ishaya ya faɗa ne cewa, “Zan yi magana da misalai, abin da yake a ɓoye tun farkon duniya, zan sanar da shi.”

36 Sai Yesu ya bar taron mutanen ya shiga gida, almajiransa kuma suka zo wurinsa suka ce masa, “Ka gaya mana abin da misalin nan na ciyawa a gona yake nufi.”

37 Sai ya amsa ya ce, “Wanda ya shuka iri mai kyau shi ne Ɗan Mutum.

38 Gonar kuma ita ce duniya, iri mai kyau kuma shi ne ˈyaˈyan mulkin, ciyawar kuma ˈyaˈyan Mugun nan ne.

39 Kuma abokin gāban da ya shuka ciyawar, shi ne Shaiɗan. Lokacin girbin kuwa, ƙarshen duniya ne. Masu girbin kuma su ne malaˈiku.

40 Kamar yadda ake tara ciyawa a ƙone ta, haka zai zama a ƙarshen duniya.

41 Ɗan Mutum zai aiko da malaˈikunsa, za su tara dukan abubuwan da suka sa mutane su yi zunubi, da kuma duk masu yin mugayen ayyuka, su fitar da su daga mulkinsa,

42 su kuma jefa su a cikin gidan wuta mai zafi. A nan za su yi ta kuka suna cizon haƙoransu.

43 A lokacin ne masu adalci za su haskaka kamar rana a cikin mulkin Ubansu. Bari mai kunnen ji, yă ji.”

44 “Mulkin sama kamar dukiya ne wadda aka ɓoye a gona, wadda wani ya samu, ya sāke ɓoyewa. Saboda yawan murna ya je ya sayar da dukan abubuwan da yake da su, ya sayi gonar.”

45 “Har yanzu dai, mulkin sama kamar ɗan kasuwa yake, mai neman duwatsu masu daraja wato, luˈuluˈu.

46 Da ya sami luˈuluˈu ɗaya mai daraja sosai, sai ya je ya sayar da dukan abubuwan da yake da su, ya saye shi.”

47 “Har yanzu dai, mulkin sama yana kama da ragar kamun kifi wadda aka jefa a teku ta kamo kifi iri-iri.

48 Da ta cika, aka jawo ta gefen tekun, aka zauna, aka zaɓa kifi masu kyau, aka sa a kwando, aka zubar da waɗanda ba su da kyau.

49 Haka zai zama a ƙarshen duniya, malaˈiku za su zo su raba, su cire mugaye daga masu adalci.

50 Su kuma jefa mugayen cikin gidan wuta mai zafi, inda za su yi kuka da cizon haƙora.

51 “Kun gane wannan duka?” Suka amsa suka ce, “I.”

52 Sai ya ce musu, “Saboda haka duk malamin da ya zama almajirin mulkin sama, kamar maigida yake wanda ya ɗebo sabuwar dukiya da tsohuwa daga wurin ajiyarsa.”

53 Da Yesu ya gama faɗin waɗannan misalai, sai ya bar wurin.

54 Yesu ya zo garinsa ya fara koya wa mutane a majamiˈunsu. Suka yi mamaki suka ce, “Ina wannan mutum ya sami hikimar nan haka, da kuma ikon yin waɗannan ayyukan ban mamaki?

55 Wannan ba shi ne ɗan kafintan nan ba? Ba mamarsa ce sunanta Maryamu ba? Ba ˈyanˈuwansa ba ne su Yakub, da Yusuf, da Siman, da Yahuda?

56 Ba ˈyanˈuwansa mata duk tare da mu suke ba? To, daga ina ya samo duk waɗannan?”

57 Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa daraja sai dai a garinsa da kuma cikin gidansa.”

58 Kuma bai yi ayyukan ban mamaki da yawa a can ba, saboda rashin bangaskiyarsu.

Open Bible reader