Skip to content

Hausa Bible

Markus 2

1 Bayan ˈyan kwanaki, Yesu ya sāke komawa Kafarnahum, sai mutane suka ji labari yana gida.

2 Mutane da yawa suka taru, har ba sauran wuri, ko a bakin ƙofa ma. Yesu yana faɗa musu kalmomin Allah.

3 Sai ga mutum huɗu suka zo, suna kuwa ɗauke da wani shanyayye.

4 Da suka kāsa shigar da shi zuwa wurin Yesu saboda yawan mutane, sai suka buɗe rufin gidan daidai inda Yesu yake. Da suka huda rufin, sai suka saukar da mutumin, duk da tabarmarsa.

5 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, an gafarta maka zunubanka.”

6 To, waɗansu malaman Koyarwar Musa suna zaune a wurin, suna ta tunani a cikin zuciyarsu,

7 suna cewa, “Don me mutumin nan yake magana haka? Ai, yana wa Allah saɓo ne! Wa yake da ikon gafarta zunubi in ba Allah kaɗai ba?”

8 Nan da nan Yesu ya gane abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, “Me ya sa kuke yin irin waɗannan tunani?

9 Wanne ya fi sauƙi, a ce wa mai ciwon nan, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka ɗauki tabarmarka ka yi tafiya?’

10 Amma ina so ku sani cewa Ɗan Mutum yana da iko yă gafarta zunubai a duniya.” Sai ya ce wa shanyayyen,

11 “Na ce maka, tashi, ka ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”

12 Nan da nan ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya fita. Dukan mutane kuma suna kallonsa, suna mamaki, suna ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin wani abu kamar haka ba.”

13 Yesu ya sāke fita ya je bakin Tekun Galili. Mutane da yawa suka taru kewaye da shi, ya kuwa koya musu.

14 Yana wucewa, sai ya ga Lawi ɗan Halfa yana zaune a wurin karɓar haraji. Sai Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.

15 Wata rana, Yesu yana cin abinci a gidan Lawi. Waɗansu masu karɓar haraji da waɗansu masu zunubi da yawa suna ci tare da shi da almajiransa, gama mutane da yawa daga cikinsu ne suka bi shi.

16 Waɗansu malaman Koyarwar Musa waɗanda su Farisiyawa ne, suka ga yana cin abinci tare da masu zunubin nan da masu karɓar haraji. Sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Me ya sa yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

17 Da jin haka, Yesu ya ce musu, “Masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”

18 To, almajiran Yohanna Mai Baftisma da na Farisiyawa suna yin azumi, sai waɗansu mutane suka zo suka tambayi Yesu suka ce, “Me ya sa almajiran Yohanna da na Farisiyawa sukan yi azumi, amma naka ba sa yi?”

19 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Abokan ango sukan yi azumi a lokacin da ango yake tare da su ne? Ai, saˈad da ango yake tare da su ba za su yi azumi ba.

20 Lokaci yana zuwa da za a ɗauki angon a bar su. To, a lokacin ne za su yi azumi.

21 “Ba mai facin tsohuwar riga da sabon yadi. Idan kuwa ya yi, sai sabon yadin ya naɗe tsohuwar rigar, har yagewar ta fi ta dā muni.

22 Kuma ba wanda zai zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. Idan ya yi haka, sai ruwan inabin yă farfashe salkunan, a kuma yi hasarar salkunan duk da ruwan inabin. Ai, sabon ruwan inabi, sai sababbin salkuna.”

23 Ana nan a Ranar Hutu ta Mako Yesu da almajiransa suna wucewa ta gonakin hatsin alkama. Suna cikin tafiya sai almajiransa suka fara karya waɗansu kan alkama.

24 Sai Farisiyawa suka ce masa, “Duba abin da almajiranka suke yi. Don me suke yin abin da Koyarwar Musa ta hana yi a Ranar Hutu ta Mako?”

25 Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, a lokacin da yunwa ta dame shi kuma yana cikin rashi, shi da abokan tafiyarsa?

26 A zamanin da Abiyatar yake babban firist ne, Dawuda ya shiga wurin sujada, ya ci Burodin da Aka Keɓe, wanda bai kamata kowa yă ci ba, sai dai firistoci kaɗai. Har ma ya ba abokan tafiyarsa!”

27 Sai Yesu ya ce musu, “Ai, an yi Ranar Hutu ta Mako domin mutum ne, ba a yi mutum domin Ranar Hutu ba.

28 Ai, Ɗan Mutum Ubangiji ne har ma da na Ranar Hutu ta Mako.”

Open Bible reader