Skip to content

Hausa Bible

Markus 13

1 Yesu yana fitowa ke nan daga Haikali, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam, dubi manyan duwatsun nan, da gine-ginen nan masu ban mamaki!”

2 Sai Yesu ya ce masa, “Ka ga dukan waɗannan manyan gine-gine? Za a rushe su duka. Ba za a bar ko dutse ɗaya a kan ɗanˈuwansa ba.”

3 Yesu yana zaune a kan Tudun Itatuwan Zaitun wanda yake fuskantar Haikalin, sai Bitrus, da Yakub, da Yohanna, da Andarawus suka tambaye shi a ɓoye, suka ce,

4 “Ka gaya mana, yaushe ne za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama ce za a gani a lokacin da suke shirin faruwa?”

5 Sai Yesu ya ce musu, “Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku.

6 Mutane da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa su ne ni, har su ruɗi mutane da yawa.

7 Idan kuma kuka ji labarin yaƙe-yaƙe da jita-jitarsu, kada hankalinku yă tashi. Dole ne wannan yă faru, amma ƙarshen bai zo ba tukuna.

8 Alˈumma za ta tasar wa alˈumma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi ta rawar ƙasa a wurare dabam-dabam, za a kuma yi yunwa. Amma duk waɗannan ba ainihin azabar ba ne. Masomin azaba ne kawai.

9 “Sai ku kula da kanku, don za su kai ku kotu a kuma yi muku dūka a majamiˈu. Za a kai ku gaban shugabanni da sarakuna saboda sunana, domin ku shaida labari mai daɗi a gabansu.

10 Amma kafin ƙarshen yă zo, dole ne a yi wa dukan alˈummai shelar labarin nan mai daɗi.

11 Duk lokacin da suka kama ku suka kai ku kotu, kada ku damu a kan abin da za ku faɗa. Ku dai faɗa duk abin da ya zo muku a wannan lokaci, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.

12 Ɗanˈuwa zai ba da ɗanˈuwansa a kashe shi, baba kuma yă ba da ɗansa. ˈYaˈya kuma za su tayar wa iyayensu har su sa a kashe su.

13 Kowa zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jimre har zuwa ƙarshe, zai tsira.”

14 “Za ku ga abin ƙazanta mai kawo halakarwa da yake kawo rushewa yana tsaye a wurin da bai kamata ba. Bari mai karatu yă gane. To, sai waɗanda suke cikin yankin Yahudiya su gudu zuwa cikin duwatsu.

15 Wanda yake kan rufin ɗaki kuma kada yă sauko yă shiga cikin gida wai zai ɗauki wani abu.”

16 “Wanda yake a gona kuma kada yă koma wai zai ɗauki mayafinsa.

17 Kaiton mata masu ciki da masu goyo a wannan lokaci!

18 Ku yi adduˈa kada abubuwan nan su faru a lokacin sanyi.

19 A kwanakin nan za a yi wata azaba mai zafi sosai wadda ba a taɓa yi ba tun farkon lokacin da Allah ya halicci duniya, har zuwa yanzu. Ba kuwa za a ƙara yin irinta ba har abada.

20 Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba ɗan Adam da zai tsira. Amma saboda tausayin waɗanda ya zaɓa, sai ya rage tsawon kwanakin.

21 “A lokacin nan duk wanda ya ce muku, ‘Duba, ga Almasihu nan!’ ko, ‘Duba, ga shi can!’ kada ku yarda.

22 Almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su fiffito, za su nuna alamu da ayyukan ban mamaki, domin su ruɗi mutane har ma da waɗanda aka zaɓa, idan zai yiwu.

23 Saboda haka, ku lura! Na gaya muku dukan kome tun da wuri.”

24 “Amma a kwanakin nan, wato bayan azabar nan mai zuwa, “ ‘Rana za ta yi duhu. Wata kuma ba zai yi haske ba.

25 Taurari za su dinga fāɗuwa daga sama. Za a kuma girgiza ikokin sararin sama.’

26 “Saˈan nan za a ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin girgije da iko mai girma da ɗaukaka.

27 Saˈan nan zai aiko malaˈikunsa su tattaro waɗanda ya zaɓa daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, wato daga wannan iyakar duniya zuwa wancan.”

28 “Ku koyi wani abu daga itacen ɓaure. Idan rassansa sun fara sākewa, suna fitar da sabon ganye, kun san damina ta yi kusa ke nan.

29 Haka kuma idan kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san lokaci ya yi kusa, yana dab da bakin ƙofa.

30 Hakika ina gaya muku, mutanen zamanin nan ba za su mutu ba, sai duk abubuwan nan sun faru.

31 Sama da duniya za su ƙāre, amma kalmata ba za ta ƙāre ba ko kaɗan.

32 “Amma ba wanda ya san ranar, ko a ƙarfe nawa ne wannan zai faru, ko malaˈikun da suke sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.

33 Ku lura, ku zauna da shiri, domin ba ku san lokaci, ko a ƙarfe nawa ne wannan zai faru ba.

34 Kamar mutum ne mai tafiya, in ya tashi, yakan ba da gidan a hannun bayinsa, kowannensu da aikin da zai yi. Saˈan nan yă faɗa wa maigadin ƙofa yă zauna a shirye.

35 Saboda haka, ku zauna da shiri, don ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba. Gama zai iya dawowa ko da yamma, ko da tsakar dare, ko da carar zakara, ko kuwa da safe.

36 Kada yă zo ba labari, yă same ku kuna barci.

37 Abin da nake gaya muku, ina gaya wa kowa ne, ku zauna da shiri!”

Open Bible reader