Skip to content

Hausa Bible

Markus 10

1 Daga nan Yesu ya bar wannan wuri, ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Kogin Yodan. Mutane da yawa kuma suka sāke haɗuwa a wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba.

2 Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wajensa domin su gwada shi, suka tambaye shi suka ce, “Bisa ga Koyarwar Musa, daidai ne mutum ya saki matarsa?”

3 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Wane umarni ne Musa ya ba ku?”

4 Suka amsa masa suka ce, “Musa ya ba da izni mutum yă rubuta takardar kashen aure, yă kuma sallami matarsa.”

5 Yesu ya ce musu, “Don taurin kanku ne Musa ya rubuta muku wannan umarni.

6 Amma tun farkon halitta, ‘Allah ya yi mutane namiji da ta mace.’

7 Domin haka fa, mutum zai bar babansa da mamarsa, yă manne wa matarsa,

8 su biyun kuma su zama ɗaya. Har nan gaba ba za su zama mutum biyu ba, sai dai su zama kamar mutum ɗaya.

9 Saboda haka, abin da Allah ya haɗa, kada wani yă raba.”

10 Da suka sāke komawa cikin gida, sai almajiransa suka yi wa Yesu tambaya a kan wannan magana.

11 Sai ya ce musu, “Duk mutumin da ya saki matarsa, ya auri wata, yana cin amanar mace ta farko da yin laifin zina ke nan.

12 In kuma mace ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”

13 Mutane suka yi ta kawo wa Yesu ˈyan yara domin ya sa musu albarka, amma almajiransa suka tsawata wa mutanen.

14 Da Yesu ya ga haka, sai ya ji haushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Gama mulkin Allah na irinsu ne.

15 Hakika ina gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai taɓa shiga cikinsa ba.”

16 Sai ya ɗauki yaran ya rungume su yana tattaɓa su, yana sa musu albarka.

17 Da Yesu zai tashi yă bar wurin ke nan, sai ga wani mutum ya zo da gudu, ya durƙusa a gabansa, ya tambaye shi ya ce, “Malam mai kirki, me zan yi in sami rai na har abada?”

18 Sai Yesu ya ce masa, “Don me kake ce da ni mai kirki? Ai, ba wani mai kirki sai Allah kaɗai.

19 Ka dai san dokokin wato, ‘Kada ka yi kisan kai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar ƙarya. Kada ka cuci mutum. Ka ba da girma ga babanka da mamarka.’ ”

20 Sai saurayin ya ce, “Malam, ai, duk na kiyaye waɗannan tun ina yaro.”

21 Yesu ya dube shi da duban ƙauna, ya ce masa, “Abu ɗaya ne tak ka rasa. Ka je ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba talakawa, za ka sami dukiya mai yawa a sama. Saˈan nan ka zo ka bi ni.”

22 Da jin wannan magana sai saurayin ya ɓata fuska, ya tafi yana baƙin ciki, don shi mai arziki ne sosai.

23 Sai Yesu ya dubi almajiransa, ya ce musu, “Zai zama da wuya sosai masu arziki su shiga mulkin Allah!”

24 Almajiran kuwa suka yi mamakin wannan magana. Sai Yesu ya sāke ce musu, “Ku ˈyaˈyana, zai zama da wuya sosai fa, mutum yă shiga mulkin Allah!

25 Zai fi wa raƙumi sauƙi yă bi ta ramin allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”

26 Da jin wannan, almajiran suka ƙara mamaki suna tambayar juna cewa, “To, in haka ne, wa zai iya samun ceto?”

27 Yesu ya dube su ya ce, “A wurin mutane kam, ba zai yiwu ba. Amma a wurin Allah zai yiwu. Domin kowane abu mai yiwuwa ne a wurin Allah.”

28 Saˈan nan Bitrus ya tā da magana ya ce, “Ga shi mu mun bar dukan kome mun bi ka.”

29 Yesu ya ce, gaskiya ina gaya muku, wanda ya bar gidansa, ko ˈyanˈuwansa, ko mamarsa, ko babansa, ko ˈyaˈyansa, ko gonakinsa, saboda ni da kuma saboda labari mai daɗi,

30 abin da zai samu a zamanin nan ma, zai fi sau ɗari, na gidaje, da ˈyanˈuwa, da iyaye, da ˈyaˈya, da gonaki, amma tare da tsanani. Saˈan nan a zamani mai zuwa, sai rai na har abada.

31 Mutane da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe. Na ƙarshe kuma, za su zama na farko.

32 Suna haurawa zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran kuma suna binsa suna mamaki. Waɗanda suke binsu a baya kuma suna tsoro. Sai Yesu ya ja su sha biyun nan gefe ya sāke faɗa musu abin da zai faru da shi. Ya ce,

33 “Ga shi za mu je Urushalima. Za a ba da Ɗan Mutum a hannun manyan firistoci da malaman Koyarwar Musa. Za su yanke masa hukuncin kisa, su ba da shi ga waɗanda ba Yahudawa ba.

34 Za su yi masa baˈa, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kashe shi. Bayan kwana uku zai tashi da rai.”

35 Ana nan, sai ˈyaˈyan Zabadi, Yakub da Yohanna, suka zo wurin Yesu, suka ce, “Malam, muna so mu roƙe ka wani abu.”

36 Sai ya ce, “Me kuke so in yi muku?”

37 Suka ce, “Muna roƙonka a ranar da za ka shiga ɗaukakar mulkinka, ɗayanmu yă zauna a hannun damanka, ɗayan kuma yă zauna a hannun hagunka.”

38 Amma Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha a kwaf na wahalar da zan sha? Ko kuwa za ku iya a yi muku baftisma da baftisma da za a yi mini?”

39 Suka amsa suka ce, “I, za mu iya.” Yesu ya ce musu, “I, za ku sha a kwaf da zan sha, za a yi muku baftisma kuma da baftismar da za a yi mini.

40 Amma zama a damana, ko a haguna, ba ni nake da ikon bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda aka riga aka shirya musu ne.”

41 Da sauran almajiran nan goma suka ji wannan, sai suka fara jin haushin Yakub da Yohanna.

42 Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani, a cikin waɗanda ba Yahudawa ba, waɗanda aka san su da mulki, sukan nuna wa mutanensu iko, manyansu ma suna nuna wa mutanensu iko.

43 Amma ba haka zai zama a tsakaninku ba. A maimakon haka, duk wanda yake so yă zama babba a cikinku, dole ne yă zama mai yi wa sauran hidima.

44 Kuma duk wanda yake so yă zama shugaba a cikinku, lallai ne yă zama bawan kowa.

45 Gama Ɗan Mutum ya zo ba domin a yi masa hidima ba, amma domin yă yi hidima, yă kuma ba da ransa domin ceton mutane da yawa.”

46 Sai suka kai Yeriko. Yana fita daga Yeriko ke nan, da shi, da almajiransa, da mutane da yawa, sai ga wani makaho yana zaune a gefen hanya yana bara. Sunansa kuwa Bartimawus ne, wato ɗan Timawus.

47 Da ya ji cewa Yesu Banazaret ne yake wucewa, ya fara ɗaga murya yana cewa, “Ya Yesu Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

48 Waɗansu da yawa suka tsawata masa cewa yă yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya sosai yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

49 Sai Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kira mini shi.” Sai suka kirawo makahon, suka ce masa, “Ka yi murna! Tashi, yana kiranka.”

50 Sai ya yar da mayafinsa, ya yi wuf! Ya tashi ya tafi wurin Yesu.

51 Yesu ya tambaye shi ya ce, “Me kake so in yi maka?” Sai makahon ya amsa ya ce, “Maigida, ina so in sami ganin gari.”

52 Sai Yesu ya ce masa, “Tafi, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan ya sami ganin gari, ya bi Yesu, suka tafi.

Open Bible reader