Hausa Bible
Luka 9
1 Ana nan sai Yesu ya kira sha biyun nan wuri ɗaya, ya ba su iko da kuma izni a kan dukan aljanu, su kuma warkar da cututtuka.
2 Ya kuma aike su su je su yi waˈazin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.
3 Ya ce musu, “Kada ku ɗauki kome domin tafiyarku, kada ma ku riƙe sanda, ko jaka, ko abinci, ko kuɗi, ko kuma ku ɗauki riguna biyu.
4 Duk gidan da aka karɓe ku, ku zauna a nan sai lokacin da za ku bar garin.
5 Duk inda aka ƙi karɓarku, in za ku bar garin sai ku kakkaɓe ƙurar ƙafafunku domin yă zama shaida a kansu.”
6 Sai suka tashi suka zazzaga ƙauyuka suna waˈazin labari mai daɗi, suna warkar da marasa lafiya a koˈina.
7 Saˈad da Hirudus mai mulkin Galili ya ji labarin dukan abubuwan nan da suke faruwa, sai ya damu sosai, domin waɗansu mutane suna cewa an tā da Yohanna Mai Baftisma ne daga matattu.
8 Waɗansu kuma suna cewa annabi Iliya ne ya sāke bayyana. Waɗansu kuma har wa yau, suna cewa ɗaya daga cikin annabawa na dā ne ya tashi.
9 Sai Hirudus ya ce, “Yohanna dai, na sa aka cire masa kai. To, wane ne wannan wanda nake jin abubuwan nan a kansa?” Sai ya yi ta ƙoƙari yă ga Yesu.
10 Da manzannin suka dawo, sai suka faɗa wa Yesu dukan abin da suka yi. Sai ya ɗauke su su kaɗai suka tafi wani garin da ake ce da shi Betsaida.
11 Da mutane suka ji yana can, sai suka bi shi. Ya kuwa yi musu maraba, ya yi musu magana a kan mulkin Allah, ya kuma warkar da dukan masu bukata a warkar da su.
12 Da rana ta kusan fāɗuwa, sai sha biyun suka zo wurinsa suka ce, “Ka sallami mutane su shiga ƙauyuka da karkara domin su nemi abinci da wurin kwana, don inda muke ba mutane.”
13 Amma Yesu ya ce musu, “Ku, ku ba su wani abu su ci mana.” Sai suka ce masa, “Duk abin da muke da shi a nan bai wuce burodi biyar da kifi biyu ba. Sai dai in za mu je mu saya wa dukan jamaˈar nan abinci.”
14 Gama maza kaɗai sun kai wajen dubu biyar. Yesu ya ce wa almajiransa, “Ku gaya wa mutanen su zazzauna a ƙungiyoyi hamsin-hamsin.”
15 Sai almajiran suka bi umarnin, suka sa dukan mutane suka zazzauna.
16 Sai Yesu ya ɗauki burodi biyar da kifi biyu ɗin nan, ya ɗaga kansa sama ya yi wa Allah godiya, saˈan nan ya kakkarya su, ya ba almajiransa su rarraba wa mutanen.
17 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi. Almajiran suka kwashe sauran da ya ragu har suka cika kwanduna goma sha biyu.
18 Wata rana Yesu yana adduˈa shi kaɗai, almajiransa kuma suka zo wurinsa. Sai ya tambaye su ya ce, “Wa mutane suke ce da ni?”
19 Almajiransa suka ce masa, “Waɗansu suna cewa kai ne Yohanna Mai Baftisma, waɗansu kuma suna cewa kai ne annabi Iliya. Har wa yau waɗansu suna cewa, ɗaya daga cikin annabawan dā ne ya tashi.”
20 Sai Yesu ya ce musu, “Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu na Allah.”
21 Sai Yesu ya ja musu kunne sosai kada su gaya wa kowa wannan magana.
22 Ya sāke gaya musu cewa, “Lallai ne Ɗan Mutum yă sha wuya iri-iri, shugabannin jamaˈa da manyan firistoci da malaman Koyarwar Musa su ƙi shi, har a kashe shi, amma rana ta uku a tashe shi kuma.”
23 Sai ya ce wa dukansu, “Duk mai so yă bi ni, sai yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa kowace rana, yă bi ni.
24 Gama duk wanda yake so yă ceci ransa, zai rasa shi. Amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai cece shi.
25 Wane amfani ne mutum zai samu, in ya sami duniya duka a kan hasarar ransa ko a bakin ransa?
26 Gama duk wanda yake jin kunyata da kuma kunyar maganata, Ɗan mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da zai zo a cikin ɗaukakarsa, da kuma ɗaukakar Ubansa, da ta malaˈiku masu tsarki.
27 Hakika ina gaya muku, akwai waɗansu a nan tsaye da ba za su mutu ba sai sun ga mulkin Allah.”
28 Bayan kamar kwana takwas da yin wannan magana, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yohanna da kuma Yakub, suka hau kan tudu tare domin su yi adduˈa.
29 Da yana cikin adduˈa, sai fuskarsa ta canja kamanni, rigunansa kuma suka yi fari fat, har suna kashen ido.
30 Ba labari sai ga waɗansu mutum biyu suna magana da shi, wato, annabi Musa ne da annabi Iliya.
31 Sun bayyana da ɗaukaka, suna magana da Yesu a kan yadda zai cika nufin Allah ta mutuwar da zai yi a Urushalima.
32 Bitrus tare da abokan tafiyarsa kuwa suna barci. Da suka farka sai suka ga ɗaukakar Yesu da kuma mutum biyun nan da suke tsaye tare da shi.
33 Da mutanen nan za su bar Yesu ke nan, sai Bitrus ya ce masa, “Maigirma, ya yi kyau da muke a nan! Bari mu yi bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin annabi Musa, ɗaya kuma domin annabi Iliya.” Bai ma san abin da yake faɗa ba.
34 Bai rufe baki ba sai ga girgije ya rufe su. Da girgijen ya rufe su, sai almajiran suka ji tsoro.
35 Sai murya ta fito daga cikin girgijen tana cewa, “Wannan Ɗana ne, wanda na zaɓa. Ku saurare shi!”
36 Da muryar ta yi shiru, sai aka ga Yesu shi kaɗai. Almajiran kuwa suka yi shiru da bakinsu. A kwanakin nan kuwa ba su faɗa wa kowa abin da suka gani ba.
37 Washegari, saˈad da Yesu da almajiran nan guda uku suka sauka daga kan tudun, sai ga wani babban taro ya zo ya same shi.
38 Sai wani daga taron ya yi kira da ƙarfi, ya ce, “Malam! Ina roƙonka ka ji tausayin ɗan nan nawa, shi ne kaɗai nake da shi!
39 Ga shi, wani ruhu yakan hau shi, yakan sa shi yă yi ihu kawai ba dalili. Ruhun kuma yakan buge shi, jikinsa yana rawa, har bakinsa yă yi kumfa. Ba ya barinsa sai ya yi masa ciwo sosai.
40 To, na roƙi almajiranka su fitar da shi, amma ba su iya ba.”
41 Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ku mutanen tsarar nan marasa bangaskiya, masu mugunta! Har zuwa yaushe zan zauna da ku, ina jimre muku? Kawo yaronka a nan.”
42 Yaron yana zuwa ke nan sai aljanin ya ɗaga shi ya buga a ƙasa, jikinsa ya fara rawa. Amma Yesu ya tsawata wa ƙazamin ruhun, ya warkar da yaron, ya mai da shi ga babansa.
43 Dukan mutanen da suke wurin suka kama baki suna mamakin ikon Allah. Mutane suna cikin mamakin abubuwan da Yesu yake yi, sai ya ce wa almajiransa,
44 “Ku kasa kunne ga abin da zan faɗa muku! Za a ba da Ɗan Mutum ga hannun mutane.”
45 Amma almajiran ba su gane abin da yake nufi da wannan magana ba, an ɓoye musu ita ne domin kada su gane. Su kuma suka ji tsoro su tambaye shi game da wannan magana.
46 Sai musū ya tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma.
47 Yesu ya gane tunaninsu, sai ya ɗauki wani ɗan ƙaramin yaro, ya sa shi yă tsaya kusa da shi,
48 ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ɗan yaro saboda ni, ya karɓe ni ne, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Domin wanda ya fi ƙanƙanta a cikinku duka, shi ne ya fi girma.”
49 Sai Yohanna ya ce, “Maigirma, mun ga wani yana fitar da aljanu a cikin sunanka, muka hana shi, don ba ya binmu.”
50 Yesu ya amsa, ya ce, “Kada ku hana shi, ai, duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”
51 Da lokaci ya yi kusa da Yesu zai koma zuwa sama, sai ya sa kai zuwa Urushalima.
52 Sai ya aiki ˈyan aika su yi gaba, su kuwa suka je cikin wani ƙauye na Samariya, domin su shishirya masa abubuwa.
53 Amma mutanen ƙauyen suka ƙi su karɓe shi, domin ya sa kai zuwa Urushalima.
54 Da almajiransa Yakub da Yohanna suka ga haka, sai suka ce, “Ubangiji, kana so mu umarci wuta yă sauka daga sama yă cinye su?”
5 Amma Yesu ya juya, ya tsawata musu.
56 Sai suka je wani ƙauye.
57 Da suna kan hanya, sai wani mutum ya ce wa Yesu, “Zan bi ka duk inda za ka.”
58 Yesu ya amsa masa ya ce, “Karnukan daji suna da ramukansu, tsuntsaye kuma suna da wurin kwanansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin kwana.”
59 Ya kuma ce wa wani, “Bi ni.” Amma mutumin nan ya ce, “Maigirma, bari in je in binne babana tukuna.”
60 Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari waɗanda suka mutu su binne ˈyanˈuwansu matattu. Amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.”
61 Wani mutum kuma ya ce, “Ni zan bi ka, maigirma, amma ka bar ni in je in yi ban kwana da mutanen gidana tukuna.”
62 Yesu ya ce masa, “Duk wanda ya fara noma da keken noma, yana kuma duban baya, bai dace da mulkin Allah ba.”